Chapter 41
Chapter 41
da kuzarin da Turaki yake jin ya rasa na ƙwatar kansa shine yazo masa acikin giftawar sakan ɗaya, wasu manyan jijiyo suka bayyana a hannayensa da goshinsa, tamkar idonsa akan siririn mutumin yake, kuma kamar yasan abinda yake shirin aikatawa, dan haka kawai zura hannunsa yayi ta baya ya damƙi hannun mutumin wanda yake shirin ɗaukar yarinyar, sannan yasa ɗaya hannun nasa yana ƙoƙarin ya cire hannun ƙaton daga bakinsa. damƙar da Turaki ya yiwa siririn mutumin ta shiga ratsa jikinsa, mutumin ya ɗaga murya wajen cewa wanda ke riƙe da Turaki"gayen nan fa bai suma ba, ya riƙe min hannu kuma kamar ba zan iya ƙwacewa ba, bugawa shege bindiga akai". da maganar da yay, da ɗauko bindigar da ƙaton yayi, da samun nasarar da Turaki yay na cire hannun mutumin daga bakinsa, suka haɗe lokaci ɗaya da ƙarar jiniyar motar ƴan sanda dake tashi daga can nesa. babu shiri ƙaton mutumin ya saki Turaki ya falla da gudu zuwa motarsu, shima siririn ya fizge daga hannun Turaki ya falla zuwa motar, ashe basu biyu bane kawai, suna da yawa, kamin Turaki ya zuro ƙafarsa daga cikin motar ya fito tuni sun bar wajen sai tashin ƙurar motarsu. tsayawa yayi yana bin bayan motar da kallo, so yake yaga lambar motar ko zai samu wata shaida amma duhun dake cikin idonsa ya hana. can kuma tunaninsa ya dawo kan yarinyar, dan haka da sauri ya buɗe bayan motar, ganinta yasa shi sauke ajiyar zuciya. ya shiga tattaɓata yana jin kamar ko sunyi mata wani abu ne. ji yake ba zai iya cigaba da jira ba, barin wajen zai yi, idan shi ya cutu ba komai ba ne, amma baya so wani abu makamancin wanda sheɗanin can ke faɗa ya faru da yarinyar, dan haka cikin azama ya koma seat ɗin driver zai tashi motar, dai-dai nan kuma motar Khalil ta ƙaraso wajen, motar police na biye da su a baya, yayin da abulance ke bin bayan ta police ɗin. Khalil na yin parking Hajiya Madina ta fito daga cikin motar, ƙafarta ma ko takalman babu ta barsu a mota, a guje ta tsallaka side ɗin da motar Turaki take har tana bigewa da dutse, ko gabanta bata gani da kyau, burinta ɗaya ne a lokacin taga lafiyarsa, hawayen nata ma nema suke su tsaya da zuba saboda kamar sun ƙare. tunda ta fito daga motar ƙwayar idon Turaki ta tsaya cak akanta, kamar wanda aka sassaƙa haka ya kasa ko da motsawa, kallonta kawai yake, kallonta yake tana tahowa gare shi da irin tashin hankalin da bai taɓa ganinta aciki ba, da wannan tausayin na uwa shimfiɗe a fuskarta, da wannan tsoron na mahaifiyar da bata son rasa ɗanta acikin ƙwayar idonta, yana gani tayi tuntuɓen amma ya kasa motsin da zai fita ya tareta daga faɗuwar, alhalin kuma so yake ya fita ya rungumeta, amma ya kasa, ƙafafunsa sunyi nauyin da ba zai iya ɗagasu ba, sai kawai ya rufe ido wani hoto na can lokacin baya yana haska masa. Hajiya Madina na ƙarasowa ta buɗe motar hannunta sai karkarwa yake. "me babban suna". sunan da ta kirasa kenan a sanda ta buɗe motar ta gansa kamar gunki. kuma ganinsa a hakan sai idanuwanta suka haska mata hoton wani abu da ba zata iya jurar gani ba, haka ma zuciyarta ta ɗarsa mata faruwar wani lamari da ba zata iya ɗaukarsa ba. a hankali ta shiga sauke ƙafafuwanta har gwiwarta ta kai ƙasa, sai kawai ta kifa kanta akan ƙafafunsa ta fashe da wani gunjin kuka me taɓa zuciyar duk wani me sauraro, irin kukan da duk wani me rauni yaji shima sai yayi. sai a wannan lokacin ne Turaki ya iya motsa hannunsa ya kamata ya ɗagata, sannan ya fito daga cikin motar, ya kasa magana haka itama ta kasa, kuka takeyi shima hawayen yake, ya jata zuwa jikinsa yayi mata wata runguma, itama wata runguma tayi masa wadda take daban da tasa, har tsakiyar babban yatsansa yaji rungumartata, irin rungumar da rabon da tai masa ita tun yana yaro. likitocin dake cikin ambulance ɗin suka fito cikin hanzari, da gadonsu suka iso wajen motar Turaki, Khalil ne ya buɗe bayan motar, yayin da nurses suka janyo yarinyar suka ɗorata akan gadon suka yi ambulance da ita. cikin sanin makamar aikinsu wasu nurses ɗin suka shiga goge jinin da yake kan fuskarta, yayinda wasu daga cikinsu kuma suka shiga ƙoƙarin ganin sun saita numfashinta ganin cewar da ranta. duk aikin da suke gudanarwa akan idon Khalil dake tsaye hannayensa acikin aljihunsa, kuma tsananin mamaki ya wanzu a fuskarsa lokacin da suka gama goge fuskarta tayi tas, wa zai gani?, yana gani dai-dai kuwa?, ba yarinyar daya kai asibiti bace ɗazu, Fillo ce fa me aikinsu. sai kawai ya fuskanci wurin da Hajiya Madina da Turaki ke tsaye har yanzu, tana ta aikin tattaɓa shi da kallon ko'ina a jikinsa kamar wadda ta ɗauki tsawon lokaci bata gansa ba. Turaki yake kallo ba Maama ba, kallonsa yake yana recalling back wani moment da Fillo tace masa,"tsoronsa nake ji". haka ta faɗa masa jikinta na kyarma, sanda ya shigo kitchen zai ɗauki abu. tambayarta yayi kawai menene ya faru yaga kamar a tsorace ta ke, shine ta faɗa masa hakan, kuma ko da ya tambayeta me ta ke tsoro sai ta kalli ƙofar kitchen ɗin sannan tasa hannu ta goge hawayenta tukunna tace masa,"Hammah". "me yasa to?, yayi miki wani abunne?". tambayar da yayi mata kenan. amma amsar da ta ba shi ita ta ɗaure masa kai,"babu abinda yayi min amma yace zan cutu idan har ban bar inda yake da rayuwa ba, wai haka yaji zuciyarsa tana faɗa masa...kuma ni bana so mu daina wannan aikin saboda da kuɗin muke rufawa kanmu asiri, kuma ni wallahi Hammah Khalil banda mugun nufi, bana cutar da kowa sai ƙoƙarin ganin na kare wanda za'a cutar". abunda ta faɗa masa kenan tana hawaye, bai ce mata komai ba a lokacin, kawai ya ɗauki abinda zai ɗauka ya fice daga kitchen ɗin. kuma yana zuwa ɗakin Turaki ya maimaita masa abunda ta faɗa, Turaki bai mu sa masa ba, hasalima ce yayi masa. "Khalil haka jikina yake bani, haka zuciyata take faɗa min...kamar yanda nake jin Granny zata iya cutuwa idan muna rayuwa a wuri ɗaya, haka nake ji akan wannan yarinyar itama". Khalil ya sauke ajiyar zuciya sanda tunanin nasa ya katse, sukai magana da wani police sannan yayi tattaki ya ƙarasa wurin su Hajiya Madina. yana zuwa ya sanar mata cewar,"Maama DPO yace zamu wuce". ta haɗiye wani yawu sannan tace,"pack anything that is very important daga cikin motar nan ka kaisu cikin taka...sai a bar wannan anan, ko ta zama rabon wani ko kuma in Allah yayi azo a ɗauketa daga baya, tunda babu me drving ɗinta yanzu". Khalil na kallonta da tsananin tausayi yace,"wani police ɗin yay driving ɗinta, ko kuma ni na tuƙa, ku sai ku tafi tare da wani acikinsu". tana kama hannun Turaki ta riƙe tace,"a'a mu tafi dai taren, wani cikin nasu yaja wannan ɗin, sai ka faɗa musu key ɗin na jiki". da faɗin hakan taja hannun Turaki suka yi gaba, shi kuma Khalil ya shiga motar ya ɗauko wayarsa sannan yabi bayansu.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243