Chapter 121
Chapter 121
kan lamarin ba kawai sai ya jefar da bindigar a wajen ya kwasa a guje ya ƙarasa gaban mutumin, ta baya ya damƙi kwalar rigarsa ya ɗago da kansa, ya zagayo ta gabansa yasa gwiwar ƙafarsa ya daki haɓarsa, ta-ke jini da ƙwaƙwalwarsa suka haɗu waje ɗaya, ƙwayar idonsa ta firfito waje yana buɗe su da ƙyar saboda azabar harbin da ya shige shi ya kalli Turaki, cikin zafin nama Turaki yasa hannu ya fizge facemask ɗin dake fuskarsa. yana faman huci kamar mayunwaci za ki yace,"ina yarinyar ta ke?". ya faɗa cikin ɗaga murya sosai. sai kuma ya sassauta muryarsa yace,"zaka tsira da ranka, kuma zan kai ka asibiti sannan zan barka da wannan jakar kuɗin ka tafi safely, but first tell me ina yarinyar ta ke?". shirunsa ya haɗe da ƙarasowar ƴan sanda wajen, suna zuwa ɗaya daga cikin ƴan sanda yasa ƙafa ya daki gabansa atake ya ƙwalla wata razananniyar ƙara saboda yacca yaji kamar za'a zare masa rai, babu shiri ya ɗaga hannu yana yi musu nuni da katangar gidan dake can gabansu. Turaki is the first one da ya bar wajen a cikin gudu, wasu cikin ƴan sanda suka mara masa baya, yayinda wasu mutum biyu suka ɗauke wannan wanda Turaki ya harba sukai mota da shi. harbin farko da Turaki yayi su Amir sunji a lokacin suna laluben Fillo acikin gidan, kuma rashin tabbatar da cewar harbin bindigar suka ji da gaske yasa basu bi ta kai ba sai a harbi na biyu, anan hankalinsu ya tattaru wuri ɗaya saboda haka duk sai suka dakata da batun nemanta suka koma ta yanda zasu tsira. Amir yace,"duk yanda akayi shegun mutanen nan da police suka zo". wani me kama da shi yace,"tabbas kuwa, but har ta ya mu kayi sakacin hakan ya faru?". sai ya juya yana kallon mutumin da ya taimakawa Fillo yace,"hau katanga ka duba mana". yana hawa katangar ya ƴan sanda daga can nesa kamar cinnaku sun baibaye faɗin wajen, hakan yasa da ƙarfi yace musu,"police ne mota har guda uku". yana faɗar hakan ya dirge ta baya dan ba ya tunanin zai iya bari a rutsa har da shi. su kuma nan suka fara neman hanyar guduwa ta ƙofar baya da Fillo ta bi, sai dai cikin rashin sa'a suna buɗewar suga police tsaitsaye a wajen riƙe da bindigu, kuma babu wata-wata suka shiga sakar musu harbi ratata, harbin ya sami kusan mutum huɗu su kuma sauran suka koma ciki da gudu don tsira da ransu, sai dai ko a lokacin tuni wasu ƴan sandan ma sun cika gidan. "raise your hands up". su shidan da suka rage ba'a harba ba suka ɗaga hannayensu sama time ɗin da Dsp yay arresting ɗinsu. Turaki kuwa tun shigowarsu babu ta kan wanda yabi sai laluben inda zai ga Fillo, haka ya koma kamar wani zautacce ya shiga can ya fito ya faɗa can ya leƙa can, kaf babu inda bai duba acikin gidan nan bai ganta ba, sai ga shi ya faɗo parlon kamar an jefo shi yana zazzare ido ko zai ganta anan duk da perlon ya fara dubawa. jiri ya ɗebe shi ya tafi ya faɗa kan wata kujera dake wurin, yasa hannu ya dafe kansa da yake jin yana barazanar tsage masa, ya rumtse idonsa sosai yana rasa me ke masa daɗi a duniyarsa, wucewar daƙiƙa ɗaya ya ɗago kai ya buɗe idonsa wacca ƙwayar ta kaɗa tayi jawurr ya sauke kallonsa akan Dsp yace,"yallaɓai banfa ganta ba, bata cikin gidan nan yallaɓai". muryarsa ta fito cikin bala'in rauni kamar zai yi kuka. Dsp na tsaye daga gefe yana kallonsa bai ce masa komai ba, har sai lokacin da wasu ƴan sanda guda uku zo, waɗanda sune aka saka su nemo Fillo a sanda suka shigo gidan. "yallaɓai babu wurin da bamu duba ba acikin gidan nan kaf babu yarinyar". Dsp ya kalli tawagar su Amir da suke tsaye hannaye a sama idanu duk sun raina fata, ya sakar musu wata uwar tsawa yace,"ku faɗa min ina ku ka ɓoye yarinyar?". da farko duk shiru suka yi sai da ya ƙara doka musu tsawar da tafi ta farko tukunna ɗaya acikinsu yana karkarwa yace,"mu ma bamu san inda ta ke ba". yana rufe baki yana jin saukar harbi a gwiwarsa, ba shiri ya saki ƙara ta azaba yana duƙe a wajen, tuni zufa ta shiga haɗo masa yana faɗin,"wallahi bamu san inda tayi ba ta gudu tun ɗazu, muna cikin nemanta ne ma ku ka zo". furucin nasa yasa Turaki miƙewa daga kan kujerar da yake a kiɗime yana faɗin,"what!, ta gudu?, baku san ina tayi ba?". ya furta yana jin kamar zuciyarsa zata buga. Dsp ya ƙara harbin ƙafar wanda yay maganar, azaba ta ƙara ratsa shi ya kuma ihu wajen faɗin,"dan Allah kayi haƙuri". Dsp ya ƙara sakar masa wani a hannu, a wannan karon ko motsawa bai yi ba don tsabar azaba, maganarsa ta fito a hankali yana cewa,"na rantse da Allah ta gudu tun ɗazu". Turaki yana shirin sauke ƙwayar idonsa kan mutumin kawai sai Allah ya kai idonsa kan Amir, yay saurin maida kallonsa kan Amir gaba ɗaya yana ƙare masa kallo da son tabbatar da abinda ƙwayar idonsa ke gani. cikin kansa ya haska da hoton lokacin da yake tsaye gaban Fillo har yana riƙe ma ta hannu har zuwa lokacin da ya juya ya bar wajen. "You!". Turaki ya faɗa in shock. sai kuma ya nufi wurin Amir gadan gadan kamar zakin dake cikin yunwa ya ga abinci. yana zuwa yasa hannu ya shaƙi wuyan Amir, ya dinga tura shi da baya har sai da ya kaisa bango ya gwara kansa a jiki. "waye kai?". Turaki ya tambaya . tun Amir bai basa amsa ba ya dunƙule hannunsa ya bawa fuskarsa wani mahaukacin naushi wanda yay sanadiyar ɗaukewar ji da ganin Amir na wucin gadin, hakama haƙorinsa ɗaya ya tsinke ya fara lilo. Amir ya ɗago kansa a galabaice sai dai tun bai gama buɗe idonsa ba Turaki ya ƙara sakar ma fuskarsa mugun naushin da yafi na farko, kan Amir yayi ƙasa jini na zuba ta hancinsa. Turaki ya ƙara yin kukan kura ya ɗago da fuskar tasa ya kuma naushin fuskarsa a gefen ido, take jini ya taru cikin idon Amir, haka ma jini ya shiga fita ta hanci ta baki. Amir yay yunƙurin ƙwatar kansa amma inaa lokaci ɗaya Turaki ya damƙi hannu da wani irin ƙarfin da bai san yana da shi ba barƙala hannun har sai da hannun Amir ya ɓalle. a taƙaice dai Turaki sai ya koma kamar mahaukaci wajen dukan Amir, ya koma tamkar zakin da ya shekara ba abinci ya kuma samu abinci a daidai lokacin da yake so, naushi yake ta kaiwa fuskar Amir hagu da dama cikin ƙaraji yana tambayarsa,"who are you?". sai da fuskar Amir ta kumbura tayi suntum babu kyan gani, ko'ina ya farfashe banda uban jini dake zuba ta gefen idonsa, tukunna Turaki ya bar fuskar tasa ya kai shi ƙasa yana tattaka ruwan cikinsa, yasa ƙafa ya dako shi ta can ya doko shi ta can, yay fatali da shi ta can, ya jefa shi ta can ya gwaru da bango, haka Turaki yayta ball da shi kamar wanda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243