Chapter 108
Chapter 108
ko kuma ke ɗaya ke cikin irin wannan ƙuncin?". kanta na ƙasa tana kallon ƙafarta dake cikin black socks tace,"bani ɗaya bace, ko Hammah Khalil da Nihal na san basa jin daɗin haka, deep down there heart na san suna jin zafi, domin babu ɗan da zai so yaga iyayensa na nuna banbanci tsakaninsa da ƴan'uwansa...so amma abinda nake so ka fahimta Sameer inda ace hankalin mahaifiyamu na kan mutum guda acikinmu da ta haifa, to da atleast zamu sami sassaucin raɗaɗin zuci, ba wai take nunawa kamar ba ita tayi naƙudarmu ba". cikin zafin nama tai wurgi da hollandia ɗin dake hannunta tasa ƙafa ta murje, tana huci take cewa,"wani sa'in zuciyata na faɗa min Turaki da Zaytuna asiri suka yiwa Maama, ba haka suka barta ba, don babu uwar dake cikin hayyacinta zata ke nuna irin son kai tsakanin ƴaƴanta da na kishiyarta, but what ever lokaci yayi, wallahi a wannan karan babu fashi da tsiya tsiya sai na aika da su lahira, zanbi ta irin waccan hanyar da suka bi, ko duk bokayen duniya zan bi saina sa an kawo min ƙarshen su Turaki". Sameer ya hura iska a bakinsa sannan yace,"bin boka is not the best solution dear tunda aikin asiri na karyewa, and ba zan bari ma mu aikata shirka ba. abu ɗaya kawai da yake nan waɗan nan mutanen su zamu ƙara bawa kwangilar...". ai tun bai ƙarasa ba ta duki table ta katse shi da cewar,"kuɗina ba zai ƙara zuwa hannun gantalallun can ba". sai kuma ta nemi kujera ta zauna ta dafe kai,"Sameer ni abinda ma yake ban mamaki, me yasa duk sanda mukai wani shiri sai kaga Turaki ya kuɓuta daga wannan shirin namu?, ka duba fa kaga last da muka sa aka datse burkin motarsa, tsakiyar dare fa muka bi, wa ya ganmu?, wa yaji plan ɗin mu?, amma sai ga shi da safe yana batun bai key na motarsa ba, kuma tun daga ranar har yau bai ƙara hawa wannan motar ba, anya Sameer?, ga shi ba wani muka sa akan aikin ba balle muce ya munafurce mu, da kanmu muka yi aikinmu, kai na kasa ganewa gaba ɗaya". Sameer shima ya kwantar da kansa kan kujera yace,"ni kaina nayi mamaki sosai a wannan time ɗin, musamman da naga up to now baya hawan motar. amma mutumin da yake kwana yana sallah har sai gari ya waye sannan ya rumtsa, mutumin da yake driving yana sauraron karatun alƙur'ani yana bi, mutumin da baya rabo da ambaton Allah a bakinsa, mutumin da common magana ɗaya yayi sai ya ambaci Allah, to ki faɗa min ta ya ba zai kuɓuta daga haɗarinmu ba?, taya ba zai kuɓuta daga sharrinmu ba?, ai muma wasa muke, iyakar kuɗin da muka ɓarnatar ya kamata zuwa yanzu ace mun haƙura kawai, mu fahimci cewar Turaki yafi ƙarfinmu dan yana tare da kulawar ubangijinsa". Samha tace,"idan kai ka haƙura ni dai ba zan haƙura ba, dole ne ma sai na ƙwaci soyayyar mahaifiyata, dole ne ma sai na ƙwatarma kaina hakki. ka duba kaga banda mota guda ɗaya da kuma fili guda ɗaya me Baffa ya taɓa mallaka mana?. amma Zaytuna motarta biyu, bayan fili har gida tana da shi, Turaki kuwa an handame duk wata kadara an basa, komai Baffa yay yunƙurin yi mana sai Maama tace shi ya kamata a bawa saboda shine Babba, ko kuma tace ai su basu da uwa sai kace mune muka sa uwar tasu ta gudu". Shiru ya ratsa kafin Sameer yace,"to yanzu what next kike ganin zamu yi?". tace,"akwai wani dodo anan ƙasar, na faɗa masa zan basa kwangilar kisan mutum biyu, yace min zan ba shi 20ML, nace masa 10ML zan ba shi, da ƙyar dai muka ƙarƙare a 15ML, dan haka zan sayar da motata ɗaya da kuma sabon filin da Maama ta bani, sai muga abin yi". Sameer yace,"hakan yayi". daga haka ta wuce ciki ta barshi anan parlo. *Gombe.* a cikin parlon na Kaka, tana zaune ta zabga tagumi tana jan carbi, sai Yami ma a gefe ta zabga nata uban tagumin, sai Maijidda dake kwance akan ledar ɗakin, ba bacci take yi ba idonta ne kawai a rufe. dukkansu kallo ɗaya zaka yiwa fuskokinsu ka shaida bala'in tashin hankalin da suke ciki, duk sun rame sosai. tun a daren jiya Amir ya ƙara kai kuɗin da kidnappers suka nema amma shiru har safiyar yau babu wani labari na dawowar Fillo, tun kiran da suka yi na cewar sun ɗauki kuɗin zasu yi abinda ya dace to basu ƙara kira ba, haka su Kaka suka yi kwanan zaune kamar yanda Amir yay daga can gidansu, amma shiru-shiru babu wani bayani. to haka yau ɗinma tun 11 na rana Hajiya Madina tayo musu aiken abinci amma sun kasa ci. dan a inda Ɗausiyya ta ajiye flask ɗin tun ɗazu yana nan a inda yake babu wanda ya taɓa shi. Yami ce tace,"Ƙawata ki ɗanci abincin nan ko loma biyu ce dan Allah". Kaka ma tace,"ke ya kamata kici tunda kina da matsalar ulcer". Kaka ta dubi Maijidda tace,"tashi ki zuba abincin nan kici". bata buɗe idonta ba hawayen daya taru aciki ya sauko tace,"ba zan iya ci ba Kaka". dai-dai nan suka ga an ɗaga laben ɗakin, da sauri suka waiga kusan a tare suna kallon ƙofar, da fatansu ace Fillo zasu gani, but sai saɓanin hakan, sai suka tsaya suna kallonsa sun kasa ɗauke idonsu akansa. kamar yadda shima ɗin bin su yake da kallo ɗaya bayan ɗaya. kallon su yake yana so ya hango maganar da Khalil ya faɗa masa a fuskokinsu, babu wanda yasan da dawowarsa hatta kuwa Maama, dan ko driver bai kira yaje ɗaukansa ba, daga airpot napep kawai ya nema ya hau ya taho. ta gate ɗin ma'aikatan gidan aka sauke shi, kuma yana shigowa straight ɗakin Kaka yayo bai ko bi ta kan ma'aikatan dake gaishe shi ba, dan wata magana ma da yaji suna yi ta Allah ya sanya alkhairi duk bai fahimta ba. Kaka ta ɗauke idonta akansa tana cewa,"bismillah me Babban suna". baya jin zai iya ɗaga ƙafafunsa daga wurin da yake ya shigar da ita cikin ɗakin, dan ya riga ya gama samun amsar tambayarsa a fuskarsu, ta tabbata matarsa ta ɓata, har tsayin lokaci ba'a ganta ba. kuma sai ka lura sosai zaka hango uban hakin da yake yi tamkar wanda ya taho a guje tun daga El-Salvador. Yami ta yunƙura ta miƙe ta ɗauko darduman sallah ta shimfiɗa tana cewa,"bismillah ga wuri". Turaki ya ziro daguwar ƙafarsa ciki yana takawa tamkar wanda bai da jini a jikinsa. ya zauna hoton Fillo na haska masa acikin idonsa, tunaninsa ya katse sanda Kaka tace,"ina yini, an sauka lafiya?". Yami ma ta gaishe shi sannan ya buɗe baki yana jin kamar ba zai iya maganar ba yace,"lafiya lau". sai kuma duk sauran maganar tasa ta katse ya kasa faɗin komai. sai da Yami tace,"muna godiya da kulawarku, Allah ya bada lada". shirunta ya haɗe da fashewar kukan Kaka. Turaki ya juyar da idonsa kanta yana ta kallonta kamar yaune ya fara ganinta. kuka sosai Kaka take kamin tace,"ni da gawarta ne ma na gani hankalina zai fi kwanciya, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". furucin nata na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243