Chapter 12
Chapter 12
ina sonki da yawa wallahi...kai Allah dai ya ƙara miki kyau". Ya faɗa yana kamo dogon hancinta. sai kuma ya kai bakinsa saitin kunnenta yana cewa,"wai yaushe zamu ƙara tafiya honey moon ne?". Hajiya Madina tace,"da gaske fa nayi zaton ko ka ƙyalla ka gano wata ƴar baturiyar ne". Yace,"waa nii rufani ki saya, at this age ace idona bai daina gane gane ba, ke ɗaya kin ishe ni. Soyayyarmu bata tsufa ba balle ta mutu". Yana nuna idanuwansa yace,"ai wannan idanuwan babu abunda suke gani sai ke, ke ɗaya tallin tal Aina'u ta Habibullahi". "to yanzu tashi mu koma ɗaki ka samu ka rama baccin asuba da baka koma ba...nima na samu na tafi guest parlo kasan yau ranar amsar kukan mata ne". Suka miƙe tsaye tare yana faɗin,"ai nayi zaton idan munje ɗakin soyayya zamu sha". tayi murmushi ta kama hannunsa. "to kai dai muje mana Your Excellency". Da haka suka haura stairs. **** "ni kuwa na godewa Allah, wai ko Allah Fillo ba za ki daina wannan kukan alluran haka ba". Kaka ce ke maganar tana daga cikin ɗaki tana gyara, dan yau tun before 7 ta tafi kai Fillo asibiti, dalilin ma da ya sa suka dawo da wuri saboda Amir ne ya kaisu, a can asibiti suka tarar da shi da wuri yaje ya kama musu layi, tun daren jiya ya kasa zaune ya kasa kwance saboda yanayin yanda ya tafi ya barta da jikinta. tun wancan ranar da Fillo ta ƙona asirin nan shikenan ta kwanta ciwo, har sati guda tana kwance jiki sai dai yay ta tsamari ba sauƙi. Sai ma yau ɗin da ta ɗanji daɗi. A yau ɗin ne Kaka ta ƙara ƙudurtar cewar Fillo bata da wani miji a wannan duniyar sai Amir, saboda samun namiji a wannan zamanin kamarsa babu shi, yau ta daɗa yabawa da hankalinsa, yana da duk wasu good qualities da ake buƙata a wurin ɗa namiji, ga uwa uba ilimin addini. ko sisinta bata kashe ba shi ya biya komai da akai bill, duk da ba kuɗi ne da shi ba, amma akwai zuciyar nema da kuma kyauta, babu yanda ba tayi ba akan ya karɓa ya ƙara amma yaƙi. dai-dai da ruwan sha wannan sai da ya siya mata na Faro da suka dawo, da kayan marmarinsa iya koƙarinsa. tana lure da shi banda tayi masa da gaske a ɗazun bai so tafiya ba. Fillo dai kukanta ta ke rerawa da ƙarfin sauti ba kaɗan ba, da Kaka ta gaji da halinta tayi mata banza. Har ta gama duk abinda take Fillo dai bata daina kuka ba, kukan da bana komai ba ne sai na allurar da akayi mata. allurar da taja akaita fushi da masoyin da ake ji da shi, dan har Amir ya ƙaraci zamansa a parlon nan ya tafi bata ko saurari duk kalar lallashin da yake yi mata ba. "kinga yau burabusko akayi...Allah sarki su Yami sun sha aiki". Maganar Kaka keyi tana ɗiban burabuskon a cikin kwano ta saka a baki. ta kalli Fillo tace,"tunda kina sonsa daure ki tashi kici". Fillo taja majinar hancinta tana ƙoƙarin tsaida kukan da takeyi tace,"miyar mene?". Kaka tace,"miyar ganye ce, kuma yayi daɗi sosai". Fillo ta koma ta kwanta,"ki aje min zanci anjima". ta faɗa sannan taci gaba da kukan kamar ƙanƙanuwar yarinya. "Allah ya shirya min ke...ni banga wani hankali a tare da ke ba da Amir ya gani ya nace miki". "ni daga yau ai babu ni babu shi, can yaje ya nemi wata ba dai ni Haliman Ammi ba, dan ba zanje gidan da za'a kassara rayuwata ba". Kaka ta taɓe baki,"to dama Fillo wa ya ɗauko shi ya kawo miki. Ke kika yayibo abinki". Kaka na sauraron radio akai sallama daga bakin ƙofa, ta amsa tana cewa a shigo. Zaytuna ta ɗaga labulen ɗakin da ya sha jiki ta shiga ta ƙara yin sallama. "jaɓɓama lale". Kaka ta faɗa a sanda ta ke bin Zaytuna da ido da rashin gane wacece. Ita kuma ta nemi wuri zata zauna a ƙasa Kakan tace,"ah haba dai ga darduma yi haƙuri ki shimfiɗa hannuna da maiƙo". Zaytuna ta karɓi darduman ta shimfiɗa ta zauna akai. Kaka tace,"sai dai ban gane wacece ba wallahi". Tai maganar fuskarta ɗauke da fara'a, tana so kuma ta gano a inda ta san kamannin da ke fuskar. "ehh ba lallai ki shaidani ba gaskiya. Daga cikin gida dai nake". Kaka ta washe baki tace,"ƙwarai kuwa ga kamannin Alhaji nan...sannu da zuwa, baƙuwar tamu ashe babbace...bari na kawo miki ruwa". Ta miƙe Zaytuna tace,"a'a wallah Inna ki barshi ai yanzu zan wuce". Kaka tace,"ai ko ba za ki sha ba saina kawo". Ta faɗa tana nufar inda kwandon wanke-wankensu yake ta ɗauko farantin roba, Allah ya taimaka akwai purewater wanda Amir ya siyo musu ɗazu mai sanyi kuwa, ta sako guda biyu ta ajiye agaban Zaytuna su na daɗa gaisawa. Zaytuna bata da niyyar shan ruwan saboda a ƙoshe ta ke, amma gudun kar Kaka taji babu daɗi dole ta ɗauka tasha, tasan tsohuwar zata iya ganin kamar ko ƙyanƙyami ne ya hanata sha. balle ita bata ma ga rashin tsabta a wajen ba, komai fes-fes wajen ɗal-ɗal an share, shi kansa ɗakin sai ƙamshin turaren wuta ɗan tsinke yake, duk idon da ya ga wajen dai ba zai ce wurin ƙazamai bane. Ɓangaren masu aikin a haɗe yake, amma kuma kowa da gefen da yake. kan Kaka a ƙasa tace,"ranki ya daɗe Allah sa dai ba wata matsala bace". Zaytun tace,"a'a Inna lafiya lau, kawai dai na shigo ɓangaren naku ne ina gaidaku". "Allah sarki aikuwa mun gode". Zaytun ta miƙawa Kaka farar leda mai kauri irin ta store tace,"ga wannan, atamfofin marasa ɗinkin naki ne...akwai doguwar riga guda biyu sai a bawa yarinyar, banma san da ita ba ne sai da Maijidda ke gaya min...da yake Maijiddan kawai na sa ni sauran duk sai yanzu nake ganin fuskokinsu". Kaka tace,"Allah sarki, ai Maijidda ita ta jima a gidan nan, su kam ai duk sai daga baya suka zo...itama ta wurin nawa bayan rasuwar mahaifiyarta na ɗaukota". Lokaci ɗaya idon Zaytuna ya kawo ruwa, kewar tata mahaifiyar ya kamata, tayi saurin danne hawayen da ke ƙoƙarin zubo mata, wannan ciwon da ke manne a zuciyarta ya taɓu. Muryarta so cool tace,"Allah ya jiƙan waɗanda suka rasu". Kaka ta amsa da amin, ita kuma ta yunƙura ta miƙe, dubu biyu ta ciro a purse ɗin ta ajiyewa Kaka. "gashi ai adu'a wa iyayenmu". Kaka ta zabga godiya ta koma jero adu'oi kala-kala, ita kuma tana ta amsawa da amin cike da jin daɗi. Yayin da taji ƙaunar Kaka ta shiga ranta, dan ita a rayuwa babban abinda zaka yi mata a duk duniya ka burgeta shine kaiwa iyayenta adu'a, tabbas kai mata hakan zata girmamaka kuma zata mutuntaka. Kuma har gaban abadan ba zata taɓa mantawa da kai ba, kuma haka ta dinƙa maka alkhairi kenan. Har ta fita bata lura da Fillo da ke gefe ɗaya a rakuɓe ba, ta nannaɗe jiki da wani mayafin Kaka me kauri saboda sanyin da ta ke ji, fuskar nan tayi jajur tsabar ansha kuka an ƙoshi. ta haɗe rai babu annuri ko kaɗan. ƙememe tana ganin Zaytuna amma taƙi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243