Chapter 140
Chapter 140
shiri ta saki Fillo tayi gefe ɗaya. me gadi yayo wajen da sauri yana bawa Turaki haƙuri duk da bai san meke faruwa ba amma da dukkan alama dai ba lafiyar. Turaki yay masa wani kallo shima yaja gefe, ya fizgi Fillo da ke ta tirjewa tana faɗin,"ni ka sakeni babu inda zan bika, me nai maka da zaka tsaneni, kuma Allah sai na rama marin da kayi min ai ba abin da na maka, Allah ni ka sakeni sai na rama". ganin yana ƙoƙarin duƙawa ya ɗauketa ba shiri ta saki jiki ta bisa suka fita. suna fita bakin gate ta gartsa masa cizo a hannu babu shiri ya saketa, ta falla a guje zata juya cikin zafin nama ya damƙota ya sunkuceta bai direta ba sai bakin ƙofa, bai ma san ashe a buɗe ya bar motar ba, yana zuwa ya buɗe front seat ya tankaɗata ciki yasa key ya rufe, dan yasan tsab zata iya guduwa before ya zagaya side ɗinsa. Fillo ta saki wata razananniyar ƙara tana ƙwala kiran Umminaaaa, ƙarar da ta fito tun daga cikin motar har waje, hakan ya ƙara ƙular da shi, yaji kamar ya buɗe ya fito da ita ya rufeta da duka, yay saurin zagayawa side ɗinsa ya buɗe ya shiga gudun karta cire lock ɗin, ya doka mata tsawa sosai da cewa. "za ki rufe min baki ko saina farfasa miki shi?". ta ɗago kanta daga jikin glass ɗin da ta kifa, ta waigo tana kallonsa da ƙwayar idonta da tayi jajir, numfarfashi kawai take saukewa kamar wacce tai tseren gudu, magana take so tayi masa but ta rasa ta yanda zata furta saboda neman shiɗewa da take yi, ta kasa cewa komai sai yarfar da ɗayan hannunta da take yi. ya ɗauke idonsa daga kanta yana kallon wurin da suka tsaya kwanaki ita da Amir, sannan ya mayar inda suka tsaya yanzu ita da Dr Yusuf, tukunna muryasa ta fito da wani irin amon sauti da ke shaida bala'in kishin da ke cinsa da kuma ɗacin ƙasan zuciyarsa yace,"ke akuyar ina ce da kowanne jaki zai dinƙa zuwa wurinki?, mutuncinki kika siyar ko me da ba za ki iya kame shi ba?, abinda ya faru da ke last bai isa kiyi hankali ba shine har kike ƙara sauraron wani namijin saboda baki da hankali, ke kinfi gane kiyita tallan kanki a titi ko?, ko ce miki akayi ƙofar gidan Alƙali matattarar ƴan iska ne da za ki dinƙa tara mana banzaye?". Fillo ta kasa jurewa azabar da take ji yana shigarta, ta miƙa hannu ta damƙo kafaɗarsa, wannan yasa maganarsa ta katse ya juyo yana kallonta, sai yaga tana ta kallonsa tana hawaye kamar an kunna famfo, yaga jikinta ya saki gaba ɗaya hannunta na barin jikinsa ya faɗi, yaga ta kwantar da kanta a jikin kujerar idanuwanta sun lumshe numfashinta na fita da ƙyar. sai yaji kamar tsoro ya kamasa, yay sauri kai hannunsa saman fuskarta, jin kamar bata motsi sai ya ruɗe ya shiga kiran sunanta yana girgiza fuskarta. shiru bata amsa ba kuma kamar bata numfashi balle ta motsa, lokaci ɗaya hankalinsa ya tashi ya tattaro ƙafafunsa ya haye kan kujerar gaba ɗaya yana ƙoƙarin janyota jikinsa, can ƙasa yaji muryarta ta fita a wahalce da cewa,"hannuna". ta faɗa tana kama gaban rigarsa ta riƙe. yace,"what?". ta ƙara cewa,"hannuna". ta faɗa tana fizgar numfashi. a burkice yace,"hannunki?, me ya sami hannun naki?". bata iya ce masa komai ba sai rufe ido da tayi ta ɓingilar da kai a jikinsa. sai ya kamo hannunta da ke jikinsa ya duba yaga babu komai, ya kai hannu zai kamo ɗaya kawai sai ƙwayar idonsa ta sauka akan yatsunta a jikin ƙofa ya ɓame da su, bai san lokacin da ya furta,"innalillahi wa'inna ilaihi waji'un". a matuƙar gigice ba ya saketa daga jikinsa. da sauri ya buɗe murfin motar, daidai lokacin ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya ta wahala, gumi ya keto masa kamar yanda itama ta haɗa uwar zufa duk da ac ɗin cikin motar, ya kamo hannun yana duban yatsun, sunyi jazur jini ya tare a waje ɗaya, fatar da farcen sun haɗe sun laguɓe, siririn ƙashin wajen kamar ya karye, sai kawai ya rufe idanunsa yana kai yatsun ya saka su cikin bakinsa, ya cika bakin da iska ya hura musu iska, ɗumin iskar ya ratsa yatsun har ɓargon jikin Fillo. tayi wani zullo a jikinsa saboda tsananin azaba, ta saki sabon kuka tana cewa,"da zafiii". ta faɗa da ƙyar cikin mawuyacin hali. ya rugumeta sosai yana ɗora haɓarsa kan fuskarta yace,"am sorry Fulaniii, i didn't do it to you on purpose, please am very sorry". yaji yacca tai wata iriyar shaƙuwa, irin shaƙuwar da ke fitowa ba saboda ƙishirwa ba sai dan tsananin azabar da mutum ke ji, ya rumtse idonsa sosai yana cije leɓensa na ƙasa, yana jin kamar duk duniya ya rasa jin daɗinsa har mutuwa. wucewar sakanni 30 ya miƙa hannu ya ɗauko wayarsa ya kira Zaytuna, tana ɗagawa bai ko amsa sallamarta ba yace,"fito da sauri". Tsantsar damuwar da ta tsinta a muryarsa ita ta shaida mata babu lafiya, kuma ita tasa ta fitowa da gudu bada sauri ba, tana zuwa bakin motar ta leƙo tana cewa,"Hammah lafiya?". Ta tambaya da fargaba ganin tashin hankali shimfiɗe a fuskarsa. bai amsa mata ba ya fito daga motar ya zaga ya ɗauki Fillo ya shiga baya da ita, sannan ya iya cewa da Zaytuna,"mu wuce asibiti". ya faɗa muryarsa a sama kamar ita ke da laifin. akan hanya tana tambayarsa me ya faru amma bai iya ko amsa mata ba, sai jijjiga Fillo yake a hankali kamar yanda ake lallashin jaririn da ake son yay bacci, kuma har suka isa asibitin yatsun Fillo na cikin bakinsa kamar yanda take rungume tsam ajikinsa tamkar zai sakata cikin ƙirjinsa. ba asibitin su Dr Yusuf suka je ba, dan gani yake idonsa idon Dr Yusuf ba za'a kwashe ta daɗi ba, wani abokinsa ya kira Allah ya taimaka yana asibitin, allurar lidocane aka yi mata don kashe zafin wajen, aka haɗa mata da drugs na pain relive, duk tsoronta da allura amma ko kusa bata yi kuka ba saboda wahala ba zata barta yinsa ba, tana lafe jikin Turaki sai kallo da ido kawai, haka ma maganin da Zaytuna ta bata tasha sam bata iya musawa ba, ta zama kamar hoto sai kallon Turaki da duk ya hargitse take yi. ya sauketa daga jikinsa ya zauna da ita kan kujera ya fita cikin sauri, in few minutes sai gashi ya dawo da malt da madara peak kamar wanda likita yace masa tana da buƙatar jini. Zaytuna dai sai kallonsa take yi tana murmushi tana kuma tausayinsa, ganin yacca duk yake ta abu kamar ba Hammansu da ta sani ba, ko su suka ji ciwo ko rashin lafiya ba ya wannan rawar jikin akansu, akwai dai kulawa kamar me amma ba irin wacca take gani a yanzu ba. ta bisa da kallo har ya isa dispenser ya ciro cup ya haɗa malt ɗin da madara, ya durƙusa gaban Fillo ya kama hannunta ɗaya yana murzawa tare da kai cup ɗin bakinta, idonta ƙyam akansa da rashin makamar ma wanne irin tunani zata yi, ya kwantar da murya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243