Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 131

Chapter 131

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,221 words 0 views Progress saved
Download Book

feeling now dear?, ina ke miki ciwo?". tace,"feeling much better Mum". ta faɗa da ƙyar saboda yacca take jin babban yatsan Turaki na ƙafarsa na yawo akan ƙafarta. ga shi yana matso da fuskarsa saitin kunnenta kamar baya ganin kowa da komai a wajen, ita al'amarunsa tun before ya tafi suka fara bata tsoro, kuma kawai sai ji tayi ya ratso da hannunsa ta baya ya matsa cikinta, ta ɗanyi zillo tana jin kamar ta fashe da kuka. a hankali ta yanda ko kaɗan Mum ba zata ji ba balle ta gane yace,"tanks immeasurably". ta ɗan kallesa kaɗan ta ɗauke idonta. a sannanne suka jiyo guɗa ta karaɗe cikin asibitin, Boɗejo ce ta taho sai rawa takeyi, take kuma wuri ya ƙara kacemewa da murna. Inna Wuro dai na gefe da sakakken baki cikin ranta tana faɗin ashe haka aljanu ma suke da haɗin kai. daga bige musu ƴa har sunyi cincirindo haka da wannan uban daren, sai dai babu hankali sam dan taga kamar murna suke yi. ta ratsa ta gefen su Kaka da suke tsatstsaye da ƴan gidan su Yusuf, ta tafi da sauri zuwa reception, ta sami wasu nurses su huɗu a zaune suna hira, tayi musu sallama suka gaida ita. tace,"ku ana can anata haska film kunan zaune da farin kaya kamar sabababbin gawa, a'a to ni dai da ku ka ganni kujerar zama nazo ɗauka. wata ƴar arziƙin tazo ta kai min kujera dan Allah in samu wajen zama tunda naga abin bana tsayuwa ba ne". Nurse ɗaya ta taso tana cewa,"Hajiya kawo Babyn". ɗayar kuma da mamaki tace,"film kuma Hajiya! a asibitin?". Inna Wuro ta gyara zaman mayafi tana riƙe Farha da kyau tace,"a'a babu zancen wani in kawo Baby, sunanta Farha ba Baby ba, kuma yanzu ina ni ina baki jaririya alhalin ban sanki ba?, inje ki cuceta in shiga uku, to wallah uwarta a kotu take yin aiki tsab sai ta iya sawa a ɗaure ni ba mutunci ne da ita ba, a hannuna ta san ƴarta haka kawai in baki ki yiwa ƴar allurar tetanus ki jamin jafa'i, yo banda ma tana can tana kallon Film ina zata bar min ita, ai basa bani ita nima kuma bana karɓa saboda sunan Zainabu Yusuf ya saka mata, ummm wai ko dai sunan uwarsa yasa bacin yasan Uwar ba mutumiyar ƙwarai bace, Allah yasa ma dai kar ƴar ta yo gadon hali, dan naga goshinta iri ɗaya da na Zainabun". Nurse ɗin tai murmushi kawai. Inna Wuro tace,"yanzu dai ɗaukar min kujerar muje, ko kuma sai an biya kuɗin ɗaukar ne?". Nurse ɗin tai ƴar dariya tace,"a'a Mama, kula daku ai aikinmu ne, muje". ta faɗa tana ɗaukar kujerar. Inna Wuro tace,"a'a in ma kince sai an biyaki ai sai a biyaki, albashin da ake baku dudu nawa yake, kuɗin fa abincin rana ɗaya ne da Amadu yake kashe mana, muje wallahi sai in sa ya baki wani abin ai ɗana yana da kuɗi, shisa ma kaf nabi Malaman duniya nace suke masa adu'a kar a sawa kuɗin ido su ƙare da wuri mu shiga uku mu gantale acin ɗumamen safe, shayi kuma ba madara balle isassan sikari". Nurse ɗin tayi gaba tana ƙunshe dariyarta, Inna Wuro na lura da hakan tace,"a'a wallahi dawo ki ajiye in ɗauka da kaina, sam bana haɗa hanya da ƴan banza irinku, shisa kaf ƴaƴan Amadu da Kursum ce bama shiri saboda irin wannan munafukar dariyar, sai inyi magana a wani ƙunshe dariya saboda ga taɓaɓɓa na magana ko?, to Allah ya isar min dan ba yafe miki zan ba, yanzu tsakani da Allah wani yazo wucewa ya gani ai sai yace min sannu, to sannu ina lafiya ƙalau ai zagi ne da cin mutumci, gaskiya ajiye kujerarki bana so na ɗauka da kaina, dama ku yaran asibitin nan duk ƴan banza ne sam baku da mutumci wallahi, kullum sai mutane sun kai ƙararku radiyo tsabar ba kwa so ku gama da duniya lafiya, to wallahi ni babu ruwana a lahira kuna kallo zan yi gaba in shige aljannah salin alin ku kam kuna baya ana ramawa talakawa abinda ku kayi musu". Nurse ɗin tace,"yi haƙuri Mama bada ke nake ba". Inna Wuro ta haɗe rai tayi mata wani kallo tace,"wato ke harda halin ƙarya irin na Aliyu kina da shi kenan, ina ganinki da idona kina ce min bada ni kike ba, to kawai na barwa Allah abar zancen bana son sabuwar fitina bacin wadda nake ciki". tasa ƙafa tayi fatali da kujerar, ta nemi wata ta ɗauka tayi gaba sai masifa take yi. sai da zata bar wajen kuma sai ta dawo murya ƙasa-ƙasa tace,"ba zaku zo kallon ba ne?, ai ko dai zaku yiwa kanku dan zaku rasa na ɗorarwa, kunga yanda jama'a suka cika wajen akayi maƙil da ƙyar ake numfashi, to dai za'ai babu ku wallahi indai baku zo ba dan faɗan aljanu da mutane ne, ɗana Aliyu ne ya kashe musu ƴarsu suka zo cin Uwassa Zainabu, ni dai du Allah kuzo ina gayyatarku kallo, ku taho da kujeru kuma ku sami na takawa dan anyiwa wajen rumfa nima sai na taka zan hango abinda ke faruwa, dan baku ga yacce suka zo da makamai suka yiwa wajen ƙawanya ba, ni yanzu so nake ma suce ba akan Aliyu zasu ɗau fansar ba akan Zainabu zasu ɗauka, ni dai da nayi sati ban bacci ba saboda tsabagen murna". jiyo tashin hayaniya ta tafi da sauri,"kai kai kai na tafi kar ayi babu ni, kar a shanye ƙafar Aliyu banga ta yanda akayi ba in kasa bada labari". Nurses ɗin na dariya suka biyo bayanta da sauri suma, ita dai sai jan kujera take tana ɗaga ƙafarta me ciwo da ƙyar, ɗayar nurse ɗin ta dage sai da Inna Wuro ta tsaya ta bata Farha, ta bata ita tana cewa,"ni da ace da jakar goyo ma sai ku ara min in sakata aciki kar inje tashin hankali yay tashin hankali nayi ta kaina in yasar musu da ƴa a wajen ban sani ba". suka gimtse dariyarsu Nurse Raliya tace,"zan riƙe miki ita Mama". tace,"aiko dai Allah rabaki da sharrin zaurawa ya haɗaki da saurayi me irin zuciyar ɗana Amadu, ya rabaki da sharrin samarin zamani masu munin hali irin na Aliyu". ta amsa da amin. tana tafe sai faman sauri take tana cewa nurses ɗin,"amma fa kuyi shiri ku riƙe takalmanku a hannu dan da zarar an fara sare-sare ta kaina zanyi in barku, dan ba zan tuna ma ni na gayyatoku ba, ku taho da sauri dai kar ayi a gama babu mu". kuma duk bakin room ɗin da Inna Wuro tazo wucewa sai ta leƙa tace,"jama'a ku fito ana faɗan aljanu da mutane ana can ana faman shanye ƙafafu, dan Allah ku fito jama'a ku taimaka mana kar a kashe jikana Aliyu, wayyo na Annabi ku taimaka jikana yana cikin masifa ya kashe ƴar aljanu, ku kawo mana ɗauki dan Allah, jama'a da yawa sun taru an rasa yanda za'ai da su kowa yabi su da kallo ana zazzare ido". jin wannan yasa mutane aka dinƙa fitowa ana ta faɗin subhanallah da innalillahi, dama tun ɗazu suna ɗan jiyo hayaniyar, kan kace me wannan wuri ya ƙara ɗinkewa da mutane

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243