Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 27

Chapter 27

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,226 words 0 views Progress saved
Download Book

Umma tace,"suna bedroom ɗin su". "kice ina gaida su kuma nayi fishi tunda basa nemana...kuma ko ɗansu yazo ba zan basu shi ba". Umma tace,"ai kina da wayarsu ki kira su mana". sannan ta ɗaure murya tace,"ina Yusuhun?". lokaci ɗaya Nuratu ta nemi hawa bori ajikinsa akan Umma tace Yusuhu, dan ita bata son sunan ana ɓata masa suna ya koma na ƴan ƙauye. ita kuma Umman duk lokacin da Yusuf ya ɓata mata rai ko ya ya ne sunan da take faɗa masa kenan. "bana son iya shege Malama bawa mijinki". tana ɓata fuska tace,"don Allah Umma ki daina cewa Yusuhu idan wasu suka ji sai su ɗauka". Umma tace,"to sai kizo ki faɗawa ubansa ai yay masa sabon yanka". sai around uku na yamma tukunna suka fita outing, Mommi nata jin daɗin fitar tasu saboda yanda suke ta ma ta hira su biyun, kowa so yake ya nuna bajintarsa na ɗebe ma ta kewa tamkar wasu ƴaƴanta. basu suka dawo gida ba sai after isha'i. *Nigeria, Gombe, Dikko resident.* kan Fillo duƙe tana yankan farce suna magana da Kaka, wadda ke ta yabon Turaki saboda mutumcinsa. Fillo dai bata cewa komai, dan ita duk da halin kirkin daya nuna bata jin zai wani burgeta. saboda haushinsa ma ta ke ji gaba ɗaya, har ga Allah ta tsani mutum me ji da kai, wannan yasa tun a wancan ranar da ta fara zuwa aiki ɓangarensu taji ko kaɗan bata ƙaunar ma hanya ta ƙara haɗata da shi ko bisa kuskure. ita bata ma yi tsammanin yana da halin ƙwarai har haka ba da zai iya taimakawa wani, tayi mamakinsa sosai. sai daga baya taga ashe tayi masa bahaguwar fahimta ne, bata san da yaje duba Kaka da jiki ba sai daga baya, tun ranar farkon aikin nan nata daya kira waya a ɗakin baya da akace ta zauna, bata ɗaga ba saboda baccin daya fara ɗibarta. da kansa yazo ɗakin ya sameta tana bacci, yana shirin juyawa ne ta farka, ta tambaye shi akwai buqatar wani abu ne fuskarsa a tamke yace mata babu, sai kawai ya fice daga ɗakin. kuma babu jimawa ya ƙara dawowa ya tambayeta ina tsohuwar da ta samu anan, tace masa ai ko da tazo babu kowa a ɗakin. kamar bai yarda da abinda ta faɗa ba lokacin, saboda ɗan jim yayi kamin ya fice a ɗakin. sai bayan isha'i da ta koma ne ta tarar da uban cartons jere a falonsu, maltina, madarar gwangwani da ruwa da kayan marmari kala-kala, ga kaza gasashshiya, abun ya bata mamaki sosai, duk da zuciyarta ta raya mata ko Amir ne ya kawo, to amma iya ƙoƙarinsa dai tasan baida kuɗin wannan uban sayayyar. tana tambayar Kaka tace mata ai Zaytuna ce suka zo ita da Yayanta suka kawo mata, a lokacin bata kawo cewar Turakin ba ne dan haka kawai godiya tayi tana daɗa faɗawa Kaka kirki irin na Zaytuna da Hajiyarsu, Kakan itama na ƙara faɗar nata kirkin da ta san Zaytunan da shi a ɗan tsukukun zaman jinyar Turaki da tai. Sai da Fillo ta shiga ɗaki taga ledar drip da tarin magani akan katifarsu sannan tai saurin fitowa daga ɗakin, tsayawa tayi kawai tana kallon Kaka kafin ta iya buɗar baki tace,"Kaka wa akaiwa ƙarin ruwa?". Kakan tace,"ni ce, ai da suka zo dubani ɗinne sai shi Yayan Zaytunan ke cewa ina da buqatar asamin ruwa domin na samu ƙwarin jikina. yana zaune anan ya kira likita yazo ya dubani shine har ya biya kuɗin waɗannan magungunan, ina ji likitan yana lissafin kusan dubu takwas Halimatu...ai yaran nan sunyo halin iyayensu". a lokacin hannu Fillo tasa ta goge hawayenta bata ce wani abuba. kuma tun daga ranar kullum sai Turaki yazo ya duba jikin Kaka sati guda kenan. ita bata ma san shine Turakin da tai kasada akansa ba sai ranar da Hajiya Madina ta aikata ɓangarensa tace tai gyara. anan ne tana shiga taga lafcecen enlergment ɗinsa a jikin bangon bedroom ɗin wanda daka shiga shi zai fara maka maraba. kuma a sannan babu hoton abinda ya shiga haskawa a idonta sai na sunansa dake jikin wannan farar takardar da ta ƙona, kamar yanda akai rubutun manya ajikin hotonsa haka ma yake a jikin takarda. tarin tambayoyi da mamaki suka maƙale a kwanyar tunaninta. tambayoyin da ta ƙudurcewa ranta son sanin su nan kusa bada jimawa ba in har taci gaba da zuwa aiki, tunda Hajiya Madina tace ko da Kaka taji sauƙi ba zata dawo ba ita zata ci gaba da aikin. dan sosai Hajiya Madina ke sonta, tunda ko da akace za'a ƙaro wasu ƴan aikin tace a'a a barsu ita Halimatunta kawai ta isheta yanzu, inma zaa ƙaro to a ƙaro ɗaya saboda kar aikin yay mata yawa, kullum cikin yabonta take tace bata taɓa ganin yarinya me hankali da natsuwa ba irinta, hakan yasa ta ke jin daɗin aikin sosai. ko a ƴaƴanta ma da Samha ne kawai basa wani ɗasawa amma ko Khalil idan ya ganta ya dinga tsokanarta da Sojan Rana. kuma sau tari indai Hajiya Madina na parlo sai tace itama ta zauna ayi kallon tare da ita, Turaki ne ma ta fuskanci kamar baya so talaka ya raɓe shi, shi yasa fuskarsa kullum ɗaure ta ke akanta, ko da yake ba ita ɗaya ya kewa hakan ba har ƙannensa idan aka cire Zaytuna da Khalil. saurin da ta ke yanzu ta gama yankan farcen ta wuce don taji Hajiya Madina na faɗin yau zasu unguwa duka gida. Kaka ta katse shirunta da cewar,"kin kuwa ɗauki namanki?". ta ɗago tace,"aina?". Kaka tace,"a'a na aje miki nama cikin farar robar nan, da za ki wanke-wanke ba ki gani ba?". "ni banga komai aciki ba, ƙila Maijidda ta shigo ta wawashe shi...wa ya kawo miki nama dama?". Kaka ta dire wani hijabi da ta ke linkewa tace,"Yayan Zaytuna ne ya shigo jiya da daddare, ba ki jima da kwanciya ba lokacin...nace masa ai ma na gama warwarewa lafiya ta samu dan jibi ma zan dawo aiki shine yace a'a nai zamana na ƙara hutawa tunda akwai me taimaka min, koma da babu a nemo wata". Fillo ta miƙe ta ɗauko tsintsiya tana share wurin da ta ɓata tace,"an gode masa...yana ta abu na masu kirki alhalin ba haka yake ba". Kaka dai shiru tayi, ita kuma ta ɗauki hijabi tana ce mata. "zan tafi Kaka. yau babu kula da buƙatun ɗan gwal da wuri zan dawo dan naji Hajiya tace zasu je unguwa". Kaka tace,"sai kin dawo ki gaida Hajiyar". tana fitowa haraba sukai kiciɓis da Maijidda, Fillo ta tsaya tana kallon yanda ta ke jera hamma daga gani kaga wadda ta taso a bacci. Maijidda tace,"yauwa dama wajenki za ni". ta faɗa tana miƙa mata wayar hannunta tace,"Amir ne ke kira tun asuba". Fillo ta kallesu ita da wayar kafin tace,"kuma ai sai kice masa bama tare". Maijidda tayi hamma sannan tace,"ai yaƙi gane wannan bayanin, ni dai ungo idan kin gama kya kawo wallahi mugun bacci ke idona". ba tare da Fillo ta karɓa ba tayi gaba abinta da cewar,"sai ki faɗa masa kinzo ba ki sameni ba". Maijidda tabi bayanta da kallo tana faɗin,"ni ban iya ƙarya ba, Allah haka zan faɗa masa kince

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243