Chapter 24
Chapter 24
me yasa bata taɓa jin zancensa ba a inda ya dace a dinga ambatonsa?, me ya yiwa masu son kassara rayuwarsa?. Bata da dukkan amsar waɗannan tambayoyin, sai kawai ta lumshe ido tare da hura iska a bakinta kamin ta furzar sannan ta sauke ajiyar zuciya. Bata manta da abunda ya faru ba a wajen, tsawon watanni biyar da suka wuce. Komai yana nan daki-daki a cikin kanta, fuskokin mutanen da su kai aikin ne kawai ba zata iya shaidawa ba, dan a lokacin bayansu da kayan jikinsu kawai ta gani kamar yanda taga Muhammad Turaki a yau, amma ko muryarsu taji a yanzu zata nuna su ta rantse da Allah cewar su ne. MUHAMMAD TURAKI, harufan sunan da manyan baƙi suka ƙara haskawa cikin idonta, sunan da yake a jikin wannan farar takardar da babu zanen komai acikinta sai na sunansa da jan fenti. Sunan da ta kasa karantawa a randa tayi arangama da layar, kuma haka tayi ta ajiyar takardar har sanda Amir ya shigo cikin rayuwarta, ya fara koya mata karatu har tazo ta iya haɗa harufan a wata takarda ta daban ta maimaita rubutun sunan, sannan ta iya karantawa. Ita dai bata san asiri ba, bata san ya ake yinsa ba, kuma bata san ya yake ba. amma zata iya rantsewa cewar aikin da waɗannan mutanen su kai asiri ne duk da bata ji sun ambaci wani abu da zai haska mata hakan ba, kuma babu tantanma asirin yana da alaƙa da sunan da ke rubuce ajikin wannan farar takardar da aka maida ita laya. Abu guda kawai ta san da shi, shine idan har ta manta wurin da akai haƙan aka binne, to ba zata manta maganganun mutanen ba a lokacin da suke aikinsu. Aikin da suka gudanar a sanda ƙafafu suka ɗauke a cikin wannan babban gidan da ba ya rabo da shiga da fice ako da yaushe, ranar da akai naɗin Yarima Abbas zuwa wani matsayi da bata san wane matsayi bane, taji dai labarin irin rikicin da aka sha akan naɗin a wajen Kaka da Yami. kuma zata iya cewa Allah ya nufeta da zuwa wajen ne saboda ta zama wata hanya ta tarwatsa mugun ƙudurin da ake shirinyi akan wani bawan Allah, tunda tsawon shekarun da ta ɗauka tana rayuwa cikin gidan bata taɓa zuwa wurin ba sai a ranar, lokacin kowa ya watse ana can masarauta ita kuma ta dawo dan ɗaukar ƙwaryar furar da ta dama zata bawa Amir. A lokacin bata san ta ya ma akai ta kai kanta wajen ba. Ita dai kawai ta ganta ne ta ɓullo ta cikin lambu, ta durƙusa ta ƙasan bishiyan ayaban ta fito, kuma tana fitowa ne taci karo da wasu mutane su uku su na kalle kalle dan tabbatar da babu kowa a wurin da alama basu da gaskiya. Bata kawo komai a ranta ba ta ɗau hanyar zata fito ta bar wajen sai kawai taji namijin cikinsu na cewa. _"nan wajen ne, tace daidai inda tafukan ƙafarsa za su taka kamin ya kai ga shiga cikin lambun"._ _maganar ta fito ne daga bakin bafaden da ke tare da wasu mata su biyu._ _"andai ƙi aji shawarata, amma ni gani nake yafi ace an binne acikin lambun gaban kujerar hutawan da yake zama...amma anan wurin zai iya ma tsallakewa ya wuce"._ _Ɗaya daga cikin matan ta faɗa._ _Ɗayar muryar ta amshe da faɗin,"ni sai da muka zo gudanar da aikinma sannan nake jin zuciyata ta cika da fargabar abin da zai biyo baya, sai nake ganin kamar ba zamu yi nasara ba asirinmu zai tonu"._ _Ɗayar matar da ke tsaye kusa da ita ta wurga mata harara tana faɗin,"to kuwa mugun tunaninki ya ƙare akanki ke ɗaya...wannan ma ai baƙin ciki kike mana, kina jin irin uban kuɗin da Shugaba tayi mana alƙawari amma shi ne kike wannan mugun fatan...mtswww gaskiya ba ki haɗu ba, to ni kam dai akan wannan ɗaruruwan kuɗin da naji babu kasadar da ba zanyi ba"._ _"zafa ki iya samun kuɗin kuma ki kasa jin daɗinsu. Tunda idan aka kama mu bamu da wani mataimaki sai Allah dan ko ita shugaba sanin kanku ba zata waiwayemu ba gudun kar nata asirin ya tonu...ni kam ina tsoro sosai wallahi jikina na bani wani abun zai faru, dan ba lallai muyi nasara ba sai da mu faɗi"._ _A ƙufele ɗayar ta kuma cewa,"to zabiya uwar zancen ai sai kije ki faɗawa Jakadiya ke ba za ki iya wannan aikin ba saboda ga abunda kike gudu...kinga sai ta musanya ki da wadda take ganin za tayi mata aikinta ba tare da ta ji wani ɗar ba...mutum da shegen son kuɗi amma sai uban tsoro"._ _Rufe bakinta kenan Bafaden ya washe haƙoransa da faɗin,"yo ta jewa Jakadiya da wannan zancen ai sai dai wata ba ita ba. Dan tun a wajen zata zama tarihi kamin ma maganar ta kai ga kunnen Shugaba. Da farko da aka kirawo ki aka tambayeki za ki iya ba ki ce ba za ki iya ba sai bayan da kika gama jin sirrinsu saboda rashin hankali. To wa kike tunanin zai barki da rai?"._ _"ni fa ba wani abu nace ba, hankalina ne kawai yau ɗin naji bai kwanta ba. Dan duk randa asirinmu ya tonu, ko ita Shugabar da muke taƙama da ita ba zata iya ƙwatarmu ba, ƙila ma ta juya mana baya"._ -Da Bafaden da ɗayar matar su kai tsaki a tare. "to idan kin shirya rasa ranki da kuma dubu ɗari biyar ɗin da za'a ba ki kina iya juyawa ki tafi, mu ki barmu muyi aikinmu...akan kuɗi da kika ganmu babu kasadar da ba zamu iya ɗauka ba"._ _su na rufe baki Bafaden ya durƙusa ya shiga haƙe ƙasar da ke wurin, wanda bai tsaya ba har sai da yayi rami mai ɗan zurfi tukunna. Sannan macen da bata da tsoron ta ɗauko gorar ruwa a cikin jakar da ke hannunta ta juye ruwan a cikin ramin. Sannan ta miƙa hannu ta karɓi wata baƙar leda a hannun ɗaya matar ta zira a cikin ramin. Duk abunda suke yi su na yinsa ne cikin saurari-sauri gudun kar azo a gansu._ _Kuma bayan sun maida ƙasar ne sun rufe suka tsaya su na tattaunawa, wanda yanzu da su ke maganar Fillo bata jiyo komai da suke cewa saɓanin maganganun da su kai a ɗazu duk ta ji su._ _Alokacin zuciyarta na faɗa mata ne ta tunkari inda suke dan su san wani fa ya gansu, amma ɗayan ɓari na zuciyarta na hanata aikata hakan gudun karta fito suyi mata illa, duk da bata ga fuskar ko guda acikinsu ba amma tasan ba mutane bane masu imani a zuciyarsu._ _Cikin gudu mai kama da sauri suka bar wajen, sai da ta tabbatar sun bar wajen sannan ta fito, sai dai ko da taje wurin juyin duniya ta kasa gane inda akai haƙan aka binne, dan babu wata alama ta ɓurɓushin ƙasa da zai nuna maka anyi haƙan ƙasa a wajen, wannan ya nuna mata sun ƙware a iya aikinsu, kuma ba yaune farau ba._ _Ta ɗau kusan minti guda tsaye a wurin tana tunanin abinyi sai kawai taji gabanta ya yanke ya faɗi, ƙirjinta kuma na bugawa sosai, zuciyarta na faɗa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243