Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 66

Chapter 66

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
Download Book

ce masa,"to me zanyi maka? me kake so?". sai taji ya ƙara damƙe hannunta sosai, ya sauke kallonsa daga kanta ya tsayar ajikin bangon dake facing nasu. ta tsaya kawai tana kallon gefen fuskarsa, tana jin yanda ruwan hawayensa ke ɗiga a saman skirt ɗin jikinta, tana jin yana ɗauke kansa daga ƙasa yana ɗorawa a saman cinyarta, tana ji yana ƙara damƙe hannunta, tana jin yanda wani abu ke fita daga tafin hannunsa yana shiga cikin nata, tana jin wannan zafin da ta tabbatar yana ji a zuciyarsa yana taɓa tata zuciyar. ta rumtse ido for few seconds sannan ta buɗe, ta buɗe tana bin inda yake kallo har sanda ta sauke kallonta gaba ɗaya akan ƙaton enlargement ɗin dake manne a bango. tayi mugun zabura da hoton da ta gani, ta tsayar da ƙwayar idanuwanta cak akan hoton tana ƙarewa dattijuwar matar dake jikin hoton kallo, ba sai an faɗa ba matar balarabiya ce, kallon matar take tana hango tsananin kamanni na Turaki dana Zaytuna a tare da ita, tun daga murmushinta har dimple ɗinta daya lotsa ciki sosai babu abinda ya banbanta daga na Turaki dana Zaytuna. _but who is she?_, tambayar da taiwa kanta kenan, kuma kafin zuciyarta ta raya mata wata amsa sai ganin Turaki tai ya miƙe tsaye yana toshe duka kunnuwansa biyu yana doka goshinsa a jikin glass da ƙarfi. tayi azamar miƙewa tana ruƙo shi tana faɗin,"ka daina, zaka ji ma kanka ciwo". ta faɗa cikin tashin hankalin da ta rasa na menene, kuma rufe bakinta kenan jinin dake fita a goshinsa ya zuba akan ƙirjinta. ta kalla jinin dake ƙirjinta, ta kalla jinin dake fitowa a goshinsa, idonta a waje tace,"ka bari". ta faɗa da wani mugun ƙarfi tana sa hannu da iya ɗan ƙarfin da take da shi ta fizgo shi daga bakin glass ɗin da yake tsaye, sai gasa a gabanta, taja hannunsa ta zauna da shi a ƙasa tana kunce ɗankwalinta ta ɗaure masa goshin. "menene? ka daina kukan to dan Allah, ka faɗa min me kake so?, me zanyi maka?, ka jira anan karka ƙara tashi zanje na kira Maama". ta faɗa kukan dake bakinta na fitowa. kuma sanda ta yunƙura zata miƙe lokacin ya janyota jikinsa ya rungume tsam yana kama hannunta ya toshe kunnensa da su. muryarsa na fitowa cikin muryar namiji mai rauni da faɗin,"don Allahhhhh, ki taimaka min". *Comment naku shi ne ƙwarin gwiwata.* [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *23* ya ƙara maimaitawa,"help me pleaseeee". ya faɗa yana ƙara ƙanƙameta. Fillo ta haɗiye yawun bakinta da ƙyar, ita bata taɓa jinta a jikin ɗa namiji ba ko da Yayanta Hamid. amma yau itace gaɓa ɗaya cikin jikin wani ƙaton ya ƙanƙameta, ƙanƙamar da tasa ta jin kasala, kuma tana ta ƙoƙarin ta fita a jikin nasa ta kasa. sai tayi shiru kawai tana sauraren yanda zuciyarsa ke bugawa, beat ɗin na fita da ƙarfin gaske, sai taji tana jin tsoro. muryarta a hankali tace,"taimakon me zanyi maka?". ta faɗa tana so ta raba jikin nata da nasa, lokaci ɗaya sai tsoronta ya ƙaru jin yacca jikinsa ya saki gaba ɗaya. ta fita daga jikin nasa a sanda ya tafi luu ya faɗi ƙasa, bata san lokacin da ta kurma uban ihu tana tallafo kansa da sauri. ta shiga girgiza shi tana cewa,"ka faɗa min taimakon me zan maka?, me kake so na maka?, Turaki ka tashi dan Allah". kuka take sosai tana cewa ya tashi, da dai ta tabbatar cewa ya suma sai ta miƙe a ruɗe ta fice daga ɗakin, har ta kai step na ƙarshe zata sauka daga stairs sai kuma ta fara tunanin idan ta tafi ta barsa shi ɗaya cikin wannan halin me zai iya faruwa da shi?. dan haka da sauri ta ƙara komawa har tana kusa zamewa, Allah ya taƙaita tsautsayi bata faɗo daga benen ba. yana nan a sumen har yanzu, tai kansa cikin kiɗima tana ƙara jijjigasa tana cewa,"ka tashi don Allah, ka tashi ka faɗa min duk abinda kake so zanyi, zan taimaka da ko menene ko da ace zan rasa raina ta sanadin hakan". duk wata dabara nata da tunaninta ya gushe a brain ɗinta, tayi dirshen a wajen tana ta kuka abinta, tsoronta Allah tsoronta ace mutuwa yayi, wa ya kashe shi?. sai kawai ta ƙara fashewa da kuka tana tallafo kansa zuwa kan cinyarta, tasa hannu ta share hawayenta tana ta maganganu ita ɗaya. "kar ka yi min haka dan Allah, kar ka mutu a sanda yake daga ni sai kai a wajen, za'a ce ni na kashe ka, wallahi haka zasu ce. kuma ni ban san komai ba, ban san me ya sameka ba, dan Allah dan Annabi ka farka karka mutu yanzu, ka farka ka faɗa min duk abinda kake so, ka faɗan duk kalan taimakon da zanyi maka, ni kuma nayi alƙawarin zan maka shi". ta ƙarasa maganar tana kifa goshinta akan nasa, sam sam bata san me ya kamata tayi a yanzu ba, abu ɗaya ta sani, shine ba zata taɓa fita ta barsa shi ɗaya a cikin wannan halin ba. can kawai sai taji zuciyarta na faɗa mata cewar ta kira waya, ta kira Maama ta sanar mata komai, to amma da wacce wayar?. ɗago da kanta tayi ta fara laluben aljihunsa dan ɗauko wayarsa, ta gama lalubenta bata ji komai ba sai wallet ɗinsa. tunaninta wayar ko tana cikin wallet ɗin ne, hakan yasa ta buɗe wallet ɗin da niyyar ɗaukowa, amma da mamakinta tana buɗewa taci karo da hoton mutum biyu, na Zaytuna da kuma Dattijuwar matar da ta gani a jikin wancan hoton. kanta ya ƙara ƙullewa ta rasa wanne irin tunani za tai akan lamarin dake yawo cikin ranta, yanzu ba lokacin buƙatar lallai sai ta san komai ba ne, yanzu lokaci ne na kuɓutar da Turaki da take ganin kamar rayuwarsa tana jingine da ita ne, warwarewar abunda bata sani ba shi yafi komai sauƙi a wajenta, idan ya farka zata zauna ta zana komai dake ƙulle cikin kanta a tsakiyar tafin hannunta, tukunna ta karance shi da zurfin tunaninta, idan lissafin nata yayi dai-dai, to ta tabbata daga nan zata warware komai a cikin sauƙi. cikin azama ta miƙe ta nufi hanyar fita sai Allah ya nufeta da ganin wayarsa akan locker, ta isa wajen ta ɗau wayar hannunta sai karkarwa yake. ba security a wayar, dan haka tana buɗewa kai tsaye lambar Maama ta laluba, bata ma san ta yanda akai ta iya wayar ba tunda ba taɓa riƙe waya tayi ba a rayuwarta, ko wayar Yami ma tsakaninta da ita in Amir ya kira Maijidda ta kawo mata tasa mata a kunne, amma ko ɗaga waya bata taɓa yi da kanta ba. scrolling kawai take a ɓangaren miscalls amma ta rasa lambar da ta dace ta kira, bata san wani Bello Ƙaraye ba, haka bata san lambobin biyun da babu suna a jiki na waye ba, fita tai daga ɓangaren call ta shiga contact, take taci karo da sunan My world, cikin sauri ta danna kiran ya tafi. daga can ɓangaren Hajiya Madina da ke zaune akan kujerar dake cikin ɗakinta. ƙafafunta a harɗe tana jin yanda zuciyarta ke matsewa, tana jin yacca zuciyarta ke faɗa

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243