Chapter 18
Chapter 18
minti goma Kaka ta farka daga baccin da ya fara ɗaukanta, ta kalli Fillo da ta rafka uban tagumi alamu na nuna hankalinta ma gaba ɗaya baya jikinta. Sau uku ta kira sunanta ba taji ba, sai da ta bubbugi kafaɗarta. "tunanin ne kike?". "kin farka?". Tamyaryoyin suka fito daga baku nan su a tare, Kaka ce ta fara amsa mata da cewar,"ehh na tashi amma yanzu zan koma". Ita kuma tace,"to ki koma dan Allah, ƙila isassan baccin da ba kya samu ne kwana biyu". Kaka dai kallonta ta ke yi, tunanin da inda zata fara yi mata bayani take, kamar da wuya ta yarda taje tayi aikin nan, ba don komai ba ganin a halin da take ciki, sannan babbar damuwarta ma ta ya za'a sami jituwa tsakanin Fillo da su Nihal?. Da ace Zaytuna ce kaɗai to ba zata ji wani fargaban aikata ba. "yau ba'a gama abinci da wuri ba, ko na tambayo miki Yami?". Kaka tace,"a'a naci zuwa anjima...yanzu tashi za kiyi kije kici gaba da aikin dana baro". Fillo ta buɗe baki tana duban Kaka da irin kallon mamaki. murya a kumbure tace,"ba ki da lafiyar ma ba za su yi miki uzuri ba Kaka, ni babu inda zanje na barki ke ɗaya a haka babu lafiya, suyi aikin da kansu ko kuma su nemi wata". Kaka ta kwantar da murya tace,"a'a Halima ba haka za'ai ba, kinga aikin nan ma fa ba wata wuya ne da shi ba, daɗewar ma da kika ga ina yi saboda mara lafiyar gidan ne, hatsari yayi me muni yana buƙatar kulawa, zama kawai za kiyi idan yana da buƙatar wani abu kiyi masa, idan dare yayi Hajiyar ta sami zama shikenan sai ki taso kiyi tahowarki...kina gani fa kula da shi kawai aka ƙara yawan albashina ya koma har dubu ɗari". Fillo ta daɗa ɓata fuska babu alamar zata amince da zuwan tace,"yau ya kula da kansa, gobe naje in Allah ya kaimu". Ta faɗa tana miƙewa ta fita ta wuce ɗakin Yami, babu kowa a falon su, tana ta sallama ba'a amsa ba. ba tayi mamakin jin shirun Yami ba, wataƙila tana can wurin aiki tana lura da masu yi, tun da ita da Kaka ne manya. Maijidda kuwa ta san ba zai wuce ta kaɗa yawonta ba, ta ɗaga labulen zata fito sai ga Yami ta dawo. kular abincin dake hannun Yami ta karɓo ta shigo ma ta da ita, gaisawa suka yi ta ke faɗa mata Kaka bata da lafiya. jin hakan Yami ko zama ba tai ba ta suka fito suka wuce, idanun Kaka na bisa ƙofa suka sameta. Yami tai mata sannu Fillo kuwa ta shige ɗaki dan ma kar Kaka ta ƙara tada maganar zuwanta cikin gida, tayi shiru a ɗakin tana tunanin dake sakata zubar da hawaye, kiran Yami yasa ta fito. Yami ce ta lallamata ta yarda da zuwan, kafin ta wuce sai da ta ƙara komawa ɓangaren Yami tace da Maijidda dan Allah ta kula da Kaka bata lafiya, yanzu zata dawo ba jimawa zata yi ba. A compound ta tsaya ta rasa entrance ɗin da zata nufa, ƙofofi ne suke kallonta na part har guda guɗu, ita bata san ina Kakan ke zuwa ba, ita bama ta taɓa shigowa nan ba, kuma bata ga kowa da zata tambaya ba, kuma ba zata iya zuwa wurin me gadi ta tambaye shi ba. Ta nan tsaye Khalil yazo ya wuceta, fitarsa kenan ya dawo saboda mantuwar da yayi. yafi minti biyar kafin ya kuma fitowa, ya ƙara wuceta. sai da zai shiga mota sannan hankalinsa ya ba shi kamar fa mutum ya gani tsaye har 2 times. [8/9, 19:25] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *9* Khalil ya kalli me gadi daya buɗe masa gate,"waccan fa?". ya tambaye shi yana Indicavit masa Fillo. Me gadin yace,"ehh tou Yallaɓai nima dai bayan fitowata daga banɗaki nan na ganta tsaye, ina ce ma cikin masu aiki". Khalil ya maida kallonsa ga Fillo, ba fuskarta yake kallo ba, side view ɗinta kawai yake iya gani, tsinin hancin nan ya fita ta gefe kamar allura. to ai kaf cikin masu aikin babu fara kamar wannan, infact bama sa gari dukansu, banda tsohuwar da ya gani jiya su Samha suka ce masa ita ke aiki yanzu kamin a sami wasu. to ko dai ba mutum bace?, banda haka ya za'ai bawa yazo cikin rana ya tsaya sama da minti biyar, kuma bai ganta da jakar kaya ba balle yace baƙuwa ce ta shigo, to wannan ƴar ƙauyen ma baƙuwar wa zai ce?, yana da tabbacin ba tasu bace, and cikin yaran gidan babu me yin ƙawance da wannan villager ɗin. ba tare da ya dubi me gadin ba yace,"baka ga lokacin da ta shigo ba ne?". "a'a ranka ya daɗe, bata nan ta shigo ba gaskiya, dan ko second ɗaya banyi da shiga ɗaki na ɗakko radio ba na fito, can kuma ina ɗaga kai na hangeta tsaye a wurin". mamaki ya kama Khalil, ya bar motar a buɗe ya nufi inda ta ke, me gadin ya mara masa baya. taji zuwan mutum wurin, taga kuma inuwarsu a ƙasa inda idonta yake kallo, amma sai tayi kamar bata san da zuwan kowa ba. ai yana kallonta ɗazu yazo ya wuceta yay shigewarsa ciki, ya ƙara fitowa ya wuceta ko sannu kamar bai san darajar ɗan adam ba. To yanzu da ya dawo ya tsaya gabanta me ya dawo da shi ko kuma me zai mata?, tukunna ma shirun da yay bai yi magana ba yana jiran cewarta ne?, ashe kuwa wannan ranar zata ƙare akansu. Shi kam Khalil tsayawa yayi yana ƙare mata kallo da yanda ta ke wasa da yatsun hannunta, yatsunta sirara dogwaye gwanin sha'awa, farcenta fari ƙal da shi. abunda zuciyarsa ta raya masa shine yarinyar kurma ce ko kuma makauniya, tunda ga shi dai ko yanzu da ya tabbatar tasan da tsayuwarsu a gabanta ko motsi bata yi ba, tana nan kamar wadda aka sassaƙa. yanayinta ne kaɗai zai nuna maka ba'a waye ta ke ba, amma kyawun surarta ba zaka taɓa cewa hakan ba. "lafiya dai?". Ya tambaya idonsa tarr akanta. Ta ɗago kyawawan idanuwanta farare ƙal da babu ko kwalli ta ɗan kalle shi, tukunna ta mayar da idonta ƙasa tace,"aiki nazo yi?". Da mamaki yace,"Wanne irin aiki?". Har yanzu idonta na ƙasa ta ba shi amsa da cewa,"ni dai haka aka ce nazo nayi aiki, Kakata ce ke yi, ita kuma yau bata lafiya". Khalil ya gyara tsayuwa tare da cewa,"kuma sai tace miki idan tazo aikin cikin rana ta ke nema ta tsaya?". ta girgiza kai tace,"a'a, ban san inda zan shiga nayi aikin ba ne". yana daɗa ma ta duban tsanaki, a cikin ƴan ƙauyen ma wannan lamba ɗaya ce. yay wani guntun tsaki yace,"shi kuma bakinki wari yake yi da ba za ki iya buɗe shi kiyi tambaya ba?". muryarta tayi sanyi yayin faɗin,"ai banga mutane ba ne". Yay mata wani kallon up and down na ban haushi sannan yace,"shi me gadin da kika gani dodo ne ko?". Fillo na ƙifta idanuwa ta ɗago zata dube shi taga har ya bar wajen, tabi bayan nasa da kallo, saurin tafiya yake amma ba zaka gane hakan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243