Chapter 109
Chapter 109
ƙarshe ya haɗe da rufewar idanun Turaki yana dukan ƙirjinsa, for few seconds yana jin kukan Kaka acikin kansa da kuma hasashen halin da take ciki. ya buɗe idon ya sauke a ƙasa murya a sarƙe yace,"ki daina faɗar gawa Kaka, ganin gawarta ba yanzu ba insha'Allah, za'a ganta very soon aci gaba da adu'a Allah ya bayyanata". yanda yake yin maganar sai yaji kamar me koyon magana dan bai ma san ta yanda ya haɗa kalmomin ba ya faɗa. Yami tace,"Allah ya amince". Turaki yasa hannu ya shafa fuskarsa tukunna ya yunƙura zai miƙe sai yaji Yami da Kaka na maimaita kusan magana mai shigen wacca yaji ɗazu da yana shigowa. "ashe kuma lokaci yazo to ubangiji Allah ya sanya alkhairi". ana cikin wannan halin suke faɗar kalmar Allah ya sanya alkhairi!, to ko dai duk tsananin tashin hankali ne yasa kowa ya fita a hayyacinsa har yake faɗar abinda bai kamata ba. sai da ya isa bakin ƙofa sannan ya juyo yana kallon Kaka yace,"kuma babu gidan wasu ƴan'uwa da zata iya zuwa can?". Kaka tace,"babu, duk inda ya kamaci ace an bincika duk an duba. dan shi wanda ma zai aureta da kansa yaje can dangin mahaifinta ya duba, kwanansa ma biyu acan ɗin, amma ko da ya dawo yace wallahi bata can". Kaka ta faɗa tana sake fashewa da kuka. Turaki ya dinga kallonta kafin ya fice daga ɗakin ba tare da yayi musu sallama ba. ya wuce yana maimaiata kalmar wanda zata aura cikin ransa. daga nan kai tsaye ɗakin Maama ya wuce, lokacin da ya shiga zaune ya sameta a gefen gado ta zuba uban tagumi. har ya cire takalmansa ya shigo ya zauna kusa da ita bata sani ba, sai da ya janye hannun da tayi tagumi tukunna tai firgigit ta ɗago tana kallonsa. tana ɗago ido ta gansa sai ta fashe da kuka tare da kifa kanta a kafaɗarsa. ya rumtse idonsa sosai yana jin kukan nata na taɓa zuciyarsa tana ƙara matsewa da damuwar da take ciki, yasa hannu a kanta yana cewa,"innalillahi wa'inna ialihi raji'un, Maama whats wrong?, kukan me kike Maama?". ya faɗa dan yana so ya ƙara tabbatar da komai daga bakinta, amma da mamakinsa sai gani yay ta ɗago tana yi masa zancen da ya ɗaure masa kai matuƙa ya kuma rasa ina ta nufa. "Me Babban suna ka taɓa ce musu kana sonta ne?, ko kuma ita tace maka tana sonka ne da har ka amince musu?, yanzu shikenan ni ban isa ba, ban isa ai magana da ni akan abinda ya shafi rayuwar ɗana ba?, kuma a rasa a lokacin da zaa shirya bikinka sai lokacin da akaga ina cikin tashin hankali, me Fulani Azima ta shirya?". sai kukanta ya ƙaru sosai hakan yasa tayi shiru tana ƙara kwantar da kanta a kafaɗarsa. "Maama ban fahimci abinda kike son cewa ba, me ya faru?". sai ta ɗago da kanta ta kalle shi sosai, a ƙwayar idonsa ta gasgata cewa bai san duk abinda ke faruwa ba. saboda haka sai ta miƙe tsaye ta kamo hannunsa tace,"ka muje ka faɗawa Baffa da gatanka, kai ba maraya ba ne, dan haka ba irin wannan shirin kayi ba, ba irin wannan tanadin ka yiwa aurenka ba". bai iya cewa komai ba har suka fita daga ɗakinta suka bar part dinta suka nufa na Baffa still tana riƙe da hannunsa. suna shiga suka tarar da Baffa zaune a parlo yana kallon news ya ɗora hannunsa akan tumtum ɗin dake kusa da shi. Hajiya Madina ta nemi kujera ta zauna tana rufe fuskarta da duka hannunta biyu, Allah ɗaya yasan abinda take ji a zuciyarta, kuma ta lura in bata yi da gaske ba zuciyartata na gab da bugawa. Turaki ya kalleta ya kalli Baffa wanda ko juyowa bai yi ba ya kalli inda Maama take, dan haka abin sai ya ɗaure masa kai ya dinƙa kallon su 1 by 1, abinda zai iya rantsewa bai taɓa gani ba a tsakaninsu ba kenan tsawon rayuwarsa, fushi da junansu dai, shi ko irin wannan saɓanin da ake cewa ana samu tsakanin Mata da Miji ma bai taɓa gani ba ko da a fuskokinsu. to me yake faruwa ayau ɗin?, duk akan ɓatan yarinyar ne ko ya?, me Maama take son faɗa masa ne ɗazu da bai fahimta ba?. sai ya sauke ƙafafunsa ƙasa ya zauna daga gefen kujerar da Maama take, ya kai hannunsa ya ɗora akan yatsun ƙafarta yana jin wani abu na tsarga masa. tunaninsa ɗaya ne me ya saka masa Maama zubar da hawaye irin haka?. bai san lokacin da ya haɗe yatsunsa ba ya dunƙule, banda akan ƙafar Maama yake babu abinda zai hana shi nausar koma menene. sai da ya rufe idonsa ya buɗe tukunna ya buɗe baki yace,"Barka da Rana Baffa". a sannan ne Baffa ya gyara zamansa yana kallonsa yace,"yaushe ka sauka?". yana kallon mahaifin nasa da son gano abinda ke faruwa yace,"ban jima ba. na baro Bellon acan zai ƙarasa projects na jiya da kayi magana". tun ajiya da suka yi waya da Khalil yaso ya taho amma sai Baffa ya kirasa yace zai yi representing nasa a wani program da yake da shi da safe, dalilin da yasa ya zauna ɗin kenan, kuma ayau ɗin ko Bello bai san ya taho ba saboda daga can airpot yayi. Baffa yace,"an dawo lafiya?". yace,"lafiya lau". shi dai jikinsa duk a sanyaye yake, musamman da har yanzu yaji Maama na kuka kuma Baffa ko kallon inda take zaunen bai yi ba. baya so yayi saurin interfering shi yasa yay shiru, amma sai yaji ba zai iya jurar jin kukan Maama ba, hakan yasa idonsa a ƙasa yace. "Baffa da akwai wata matsala ne?". Baffan yace,"ita Babar taka bata faɗa maka ba ne?". Turaki ya ɗago ido ya kalli Hajiya Madina sannan ya kwantar da kansa gefen gwiwarta yace,"a'a, bamu zauna da ita ba tukunna". Baffa yace,"to gobe bayan an idar da sallar juma'a insha'Allahu za'a ɗaura maka aure, kai da ƴar uwarka Ilham, dan haka sai ka zama alert". da wani bala'in shock Turaki ke kallon Baffa, maganar na maimaituwa acikin kansa. bai san sanda ya furta,"aure kuma Baffa?, dama ana irin wannan auren?, Baffa aure ban shirya ba kuma bada yarinyar da nake so ba?". kamin Baffa yay magana Maama ta buɗe fuskarta da tayi shaɓe-shaɓe da hawaye tace,"kaji ai zancen da nake maka ba. yanzu tsakani da Allah idan har aka yi masa hakan an masa adalci kenan?, ina aka taɓa yiwa mutum aure ma bai san da zancen ba sai kace wani gantalalle, and beside ita kanta matar da aka lalaƙa masa bai ce yana sonta ba, haba Baffa ka dawo cikin hayyacinka mana, ɗanmu fa da gatansa taya za'a ce za'a masa irin wannan auren da ko mara gatan ma ba'a yiwa irinsa, abar ta batun ma ni a sanar da ni tunda dama ni ba kowa bace, amma dai at first ai ya kamata shi a sanar da shi in ya amince sannan, idan ma kuma dolen ake so ayi masa sai a sanar da shi tunda wuri ba wai sai a ƙurewar lokaci irin haka ba, kawai tsakani da Allah dan anga yaro yana da biyayya sai ake zaluntarsa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243