Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 220

Chapter 220

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
Download Book

ajiye sannan ta fito ta nufi ɗakin Turaki, yana zaune kan kujera yana operating laptop, hannunsa riƙe da ƙaramin glass cup yana kurɓan coffee. yaji shigowartata amma bai ko ɗago ya kalli wurin da take ba, sai dai yayi mamakin ganinta ɗin, dan rabonta da ɗakinsa tun ranar da ya faɗa mata cewar zai dawo da Ilham, yau kusan kwana tara kenan. ko abinci idan ta gama a parlo take barinsa, ta ci nata ta bar masa nasa, ruwansa ne yaci ruwansa ne kar ya ci, yacca ya lura ma kamar girkin ma ba yi take ba sai dai ƴan aiki su yi, shiyasa shi ma baya shigowa sai yaci abinci a gidan su ko gidan su Bello. a ciki ya amsa sallamar da yaji tayi, ta ƙasan idonsa yake kallonta, tana tsaye daga jikin madubi ta maƙale, fuska sam babu annuri. yacca take fushi da shi haka shi ma yake fushi da ita, ranar da ya faɗa mata zai mayar da aure ta ƙona masa rai, yanda ta nuna ko kishinsa ba ta yi, irin ma ba sonsa take ba, kawai da ya faɗa mata ta kalle shi da fara'arta tace Allah ya sanya alkhairi, daga nan taci gaba da harkokin gabanta tamkar ba wadda kishiyarta zata dawo ba, shi kuma wannan nuna rashin kishin nasa ya ba shi haushi har ya ɗauki fushi da ita, kuma ganin bata bi ta kan fushin nasa ba ya ƙara hawa sama. ita kam tun da tayi masa kallo ɗaya ta ɗauke kanta, ba komai take tunawa ba sai ranar da ya sameta a ɗaki tana kuka. ba kamar yacca ya tsammaci kukan nata ba, kuka take yi akan ciwon mara da ya matsa mata kwana biyu, amma buɗar bakinsa a lokacin ce mata yay,"ya fi miki ki koyawa zuciyarki haƙuri da son zama da kishiya akan wannan kukan da kike yi mara amfani, domin kuwa dawo da matata babu fashi, Allah ya halasta min na zauna da irinki har guda huɗu, balle kuma matar da na fara zama da ita kafin ke, ki san da wannan". idonsa kawai ta kalla a lokacin ta san ya faɗa mata hakanne saboda kawai ya ƙuntata mata. ita sai a yanzu ta yarda da batun sauyawar da maza suke yi idan zasu ƙara aure, duk da bata ga yana wani rawar ƙafa ba amma ya sauya fiye da tunaninta, magana wannan bata haɗa su acikin gidan, kuma ba nata laifin bane, nasa ne, don ita ko kaɗan bata ma bari kishinta ya fito ƙarara ba yacca zai gane, tun tana ɗora hakan akan tilasta masa ɗin da akayi har ta daina, ta fahimci zallar bura'uba ce kawai irin ta ɗa namiji, don sosai ya tsiri wa su halaye da bata sansa da su ba, ko zata narke tana masa magana baya tanka mata, ban da jiya da yaci zarafinta. "Jannaty..." ta kira sunansa a hankali, taji ta gaza ƙarashe abin da zata faɗa saboda kukan baƙin ciki da ya taso mata. Turaki yay banza da ita kamar bai ji kiran da tayi masa ba, sai dai still bai bar kallonta ta ƙasan ido ba, yana duban kumbararrun idanuwanta, ga wanda bai sani ba zai ce ciwon ido take yi, but to him da yasan kayarsa ya san uban kuka taci ta ƙoshi har ta godewa Allah. sai ya ɗauke kansa ya sauke ajiyar zuciya, kamar ba zai bi ta kanta ba, sai kuma ya ɗan ji tausayinta a ransa, ya maido da dubansa gareta sannan yace,"ke ba kya gajiya da kuka ne, kin shigo min ɗaki kin min tsaye sai wani faman cin magani kike kina faman ɗaga hanci". Ya ida maganar yana yi mata kallon sama da ƙasa. Cikin sanyin murya ta ce masa,"don Allah kayi haƙuri ka bar ni in yi lallen". ya tamke murya ya ce,"na ce ba za'ai ba". "to ya zan yi da Maama fa?, ita fa ta ban umarni akan in je ayi min". yay ɗan jim kafin ya ce,"fita ne daga gidan nan zuwa gidan mu ba za kiyi shi ba, idan me lallan zata zo nan tayi miki ta zo, idan ba zata zo ba ki haƙura". ta haɗiye ƙullun abu a maƙogoronta na takaici, ta sunkuyar da kanta ta ƙara cewa,"don Allah ka bar ni in koma gidan ku in zauna har a gama biki, don Allah don Annabi". ɗago kansa yay ya bita da kallo, duk tayi sanyi sosai kamar mara lafiya. nazartar yanayinta ya shiga yi, so yake ya gano dalilinta na dagewa akan sai ta koma gidan su har an gama biki sannan ta dawo. yaga ta ƙara kawar da kai gefe tana goge hawaye. Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce,"matsayina na mijinki wanda aljannar ki ke ƙarƙashin ƙafata, ina me ba ki umarnin ko nan da parlo kar ki bari ayau, har sai an kawo abokiyar zamanki tukunna". yay maganar cikin muryar ba da umarni. ta dube shi a sanyaye,"yan zu ba zan iya cin alfarmar Maama ba?". tayi maganar cikin wani irin rauni. yan da bai tanka mata ba haka itama bata ƙata cewa komai ba ta fita. tana fita ya ɗauki waya ya kira Maama yace mata wai sun fita ita da shi sai zuwa yamma za su dawo, a faɗawa me ƙunshin sai gobe ayi. ƙarfe bakwai na dare aka kawo Ilham, sai da aka fara kaita gidan su Turaki sannan aka yo da ita gidanta. lokacin da Fillo ta jiyo guɗa sai da zuciyarta tayi wani mugun matsewa, yunwa take ji a lokacin ta ɗauko abinci zata ci, amma lokaci ɗaya taji ta ƙoshi, bata buƙatar komai a wannan lokacin sama da tayi kuka. ɓangaren Ilham kuwa tana can tana shan mugwayen shawarwari, an cika mata kai fal da abubuwan da muddin ta ɗauke su ba zata jima ba Turaki zai ƙara saita mata hanya. wajen ƙarfe takwas da rabi na dare, Fillo ce a ɗakinta tana shirin kwanciya bacci, wayarta tayi ƙara, waƙar da ke tashi wajen ringing ɗin ya shaida mata Turaki ne, hakan yasa bata ko matsa daga inda take ba balle taje ta ɗauka. har sau biyu kiran na shigowa ya katse bata ɗauka ba, tana gama shiryawa ta haye kan gado ta kwanta, ta dunƙule a waje ɗaya, idanuwanta na ta hasko mata yacca Turaki zai kwana tare da wata yau ba ita ba. tayi nisa cikin wata duniya ta daban Turaki ya turo ƙofar ɗakin ya shigo, ya kunna fitila ya bita da kallo, ƙarasawa yayi gaban dressing mirror da ya hangi wayarta akai, ya ɗauka ya kunna, sai yaga a silent take, hakan ya tabbatar masa da cewa ba da gangan taƙi ɗaga kiran nasa ba. ajiye wayar yayi ya shiga taɓa ƙafarta, tana jinsa amma tayi masa banza, ta rufe idonta kamar me baccin gaske. zama yay a gefen gadon kafin yasa hannu ya yaye blanket ɗin da ta rufa da shi, ya rumtsa idonsa a lokacin da idanuwansa suka sauka akan cikakkun breast ɗin ta da ya kwan biyu bai haɗu da su ba. Fillo ta buɗe ido a lokacin ta zabga masa harara tare da faɗin,"lafiya?". ta faɗa murya a sama kamar ba ita ba. ba tare da ya kalleta ba ya miƙe tsaye, ya zuba hannayensa

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243