Chapter 29
Chapter 29
ta juyo da murmushi fuskarta, abunda ke burge shi da ita fara'arta da tsabtarta, bata da wannan cunkus ɗin irin na sauran ƴan aikin da suka yi a baya. har ta ƙaraso ta tsuguna a gefen kujerar da yake zaune bai bar kallonta ba, kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta tace,"Hamma Khalil gani". ta faɗi sunan nasa kamar yanda taji ƙannensa na faɗa masa. yace,"ai nai zaton ko kina ciwon baki ne". ya faɗa da salon zolaya. ta murmusa da cewan,"ciwon baki kuma?". yace,"ehh mana, da na kiraki ai ba ki amsa ba tahowa kawai kika yi". ta saki murmushi me faɗi da cewar,"Hamma Khalil to ai kaine kake faɗin sunan da ba nawa ba, shisa sai nayi zaton ko bada ni kake ba". shima murmusawar yay kafin yace,"yanzu ke tsakani da Allah duk wanda ya ganki ranar nan da kika yi ƙeƙam a tsakiyar rana me zai yi zato?, kinga kam dan na kiraki da sojan rana ai ba laifi ba ne". murmushi kawai tayi bata ce komai ba. "anyway, wanne class kike before ki taho aikatau?". furucin da yay yasa ta ɗagowa ta kalle shi kaɗan sannan ta mayar da kanta ƙasa. "bana zuwa makaranta ai". da mamaki ya kalleta,"gaba ɗaya ba ki taɓa zuwa makarantar boko ba?". ta ɗaga masa kai tabbacin hakan. ya girgiza kansa,"to islamiya fa?". ruwan hawaye ya cika idonta kafin tace,"nayi islamiya kamin Ummi ta rasu, kuma itama tana yi min a gida". yace,"wace Ummi?". sai da tasa hannu ta goge hawaye tukunna tace,"mahaifiyata". lokaci ɗaya tausayinta ya kama shi. "Allah ya jiƙanta". ta amsa da,"amin na gode, Allah yaja da ransu Baffa". shima ya amsa da,"amin na gode. amma kuma idan baki je makarantar boko ba taya akai ranar nan kika karanta saƙon da Maama ta bar miki?". taja yatsanta na tsakiya bata ce komai ba. ya katse shirun,"tambayarki nake". murya a hankali tace,"wanda zan aura ne ya fara koya min yanda zanyi karatu, kuma daga baya sai muka daina saboda ayyuka da suka yi masa yawa". kalmar wanda zan aura ta ba shi mamaki. to amma sai dai aure wa ƙaramar yarinya kamar wannan a wajen ƴan ƙauye ba wani abu bane, wataƙila da ace ba anan suke zaune ba yanzu haka tana da ƴaƴa. ya sauke numfashi yace,"yayi ƙoƙari shi wanda za ki aura ɗin...yanzu yaushe ne bikin?". tace,"ba'a tsayar ba tukunna amma dai da an kusa wani dalili yasa aka ɗaga". ta faɗi hakan idonta na kawo ruwa sosai, kuka ta ke sonyi a lokacin amma saboda Khalil ɗin ta hana kukan samun ƴancin fita daga bakinta, domin bata so ya gano wani ciwo da rayuwarta ke ɗauke da shi. ya ɗaga kafaɗarsa ya ajiye wayarsa sannan ya fuskantota gaba ɗaya. "to kin san menene?, mu a gidan nan idan mutum zai yi aiki dole sai yana karatu, kije ki tambayi duk wanda ya taɓa aiki anan, haka tsarin Baffa yake...and dalilin daya sa ma inaga Maama bata yi miki zancen ba kwana biyu aiki ya sha kanta ne, amma yanzu idan kinje ki tuna mata, akwai Malamin da yake zuwa yana yi muku karatu". ta ɗago ido tana kallonsa, kamar bata fahimci me yake son cewa ba. ya ɗaga mata gira,"ehh idan kinje ki cewa Maama ke ba ki yi karatu ba". ta gyaɗa kai kawai sannan ta miƙe zata wuce. Turaki ya shigo parlon a lokacin yana waya. ta gabansa ta wuce tana ji yana cewa,"me zan yi da yarinyar da bata waye ba, ka bar wannan batun she is not my type...infact ni babu aure ma a lissafin rayuwata". hannuwan Fillo suka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin ta buɗe, tayi sallama amma ba'a amsa ba. hakan yasa tasa kai zuwa ciki ƙafafuwanta na luntsumewa cikin tattausan carpet ɗin dake malale a duka ɗakin tun daga bakin ƙofa, kai kace cikin auduga kake sanya ƙafa saboda tsabagen taushi. tayi tsaye daga nan bakin ƙofar bayan ta maida ƙofar ta rufe, jikinta take takurewa saboda yanda sanyin ac ke ratsata. ta kusan minti uku tsaye sannan Hajiya Madina ta fito daga wata ƙofa da idan ba sani kai ba ba zaka ce ƙofa bace. da sauri ta durƙusa a ƙasa tana kama gefen zanenta ta riƙe. dalilin wani abu da yayi duka acikin kanta sanadin furucin da taji Hajiya Madina tayi acikin wayar da ta ɗauka yanzu da aka kira. "asiri fa kika ce Lubna, wa ya faɗa miki?". abinda Hajiya Madinan ta fara kenan cikin muryar razani, amma ita a wannan lokacin kalmar asirin ce ke ta maimaituwa acikin kwanyar kanta, lokaci guda kuma hankalinta ya gushe daga cikin ɗakin ta lula wani wurin can daban da tunanin abinda ya danganci asirin. "to shikenan Allah dai ya kyauta...ni ma kinga zamu je gidan Alhaji Babba ne akan lamarin Hammansu, sam yaƙi aure kuma ko zancen auren baya so ayi masa, mun rasa kuma dalilinsa dan ko jiya sun fi awa shi da Baffansa kan ya sanar masa da dalilinsa yace shi babu komai haka ɗaya, sannan babbar matsalar duk wannan nacin ibadar tasa yanzu ba yayi, sai kiga ko sallah ake yana zaune...to shine Boɗejo ke ganin abun kamar ba lafiya ba". Hajiya Madina ta faɗawa ƙawarta Lubna da suke wayar. daga ɓangaren Lubna ɗin tace,"subhanallah, gaskiya kam dai wannan labari ba lafiya ba a tashi a nemi magani, namiji har namiji kamar Turaki ace baya son aure, ai lamarin akwai duba...Allah dai ya kawo komai da sauƙi". Hajiya Madina tace,"amin ya Allah...shikenan sai mun ƙara yin waya, dan Allah karki manta da saƙon nan ki bayar akai musu". daga ɓangaren Lubna ta sake cewa wani abu sannan Hajiya Madina tace,"ina ta ƙoƙarin yin hakan. sai dai ina tsoro Lubna, ban san mutanen dake bibiyar rayuwarsa ba, haka ban san wanne irin shiri suke yi akansa ba, dalilin da yasa na dage akan cewar ya haƙura da kowanne irin aiki zamansa a gida shine kwanciyar hankalinmu, haka kuma shima a nasa ɓangaren wannan ne kaɗai tsaron da zai samu...wallahi ba ki ga munin last accident ɗin da yay ba, Lubna sai dana gama cire rai da shi tukunna ya farfaɗo...amma akan maganar wannan company ɗin da Baffa ke cewa zai buɗe musu wataƙila na yarda ya zama jagoran ciki amma in har bai ɗara daga state ɗin nan ba, amma muddin wani gari ko wata ƙasa ce can daban hakan ba zai yiwu ba". haka suka ci gama da tattaunawa tsawon mintuna kafin suyi sallama. ta ajiye wayar tana mai cewa da Fillo,"buɗe wancan closet ɗin ki ɗauko min wasu takardu daga sama". Fillo ta miƙe dan cika umarninta, tana ɗauko takardun tana mamakin irin jama'ar da Allah ya bawa Hajiya Madina, ko da yaushe acikin yin waya ta ke, inda take gani da itace gaskiya ba zata iya ba, domin idan kunnenta bai ciwo ba to bakinta zai yi. yanzu fa ta gama waya ko minti biyu ba'a ƙara ba amma har an kuma kiranta. "zan bar su a gida, akwai yarinya idan kazo zata baka". abinda ta ke cewa dana wayar kenan, kuma lokacin da Fillon ta ƙaraso ta durƙusa ta bata takardun. "alright sai ka zo". daga haka wayar tasu ta yanke, ta dubi Fillo tace da ita,"gobe za ki fara ɗaukar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243