Chapter 46
Chapter 46
fashe da kuka ba, wutar dake ƙara ruruwa ta kusa kamo rigarta tai saurin matsawa daga wurin, kuka takeyi sosai, "Kaka". sunan da take ta ambata kenan, ita bata san ta inda zata bi ta koma gida ba, saboda haka ta zube a wajen tana daɗa fashewa da matsanancin kuka, tsoro na ƙara cikata. tana cikin hakan taji zuciyarta na biyo mata wasu ayoyi acikin alqur'ani da kuma wasu adu'oi dake cikin hisnul muslim, bakinta na karkarwa ta fara biyosu a fili. sai taji komai dake cikin kanta na washewa, haske na zuwar mata, mafita na zuwa cikin kanta. sai tayi zumbur ta miƙe, zuciyarta na faɗa mata ta bar wajen da sauri. tasa hannu ta toshe hancinta saboda warin hayaƙin, wani irin ɗoyi ne yake tashi aciki, tai azamar barin wajen da gudu amma sai taji ƙafarta guda ɗaya ta riƙe, sai sannan ta tuna da ciwon dake ƙafar. amma a hakan ta dinga jan ƙafar tana ɗaga waccan har ta bar wurin, kuma tana zuwa bakin wata ƙatuwar bishiya taji tushh abu ya fashe, bata tsaya ba taci gaba da tafiya, tsoro kuma na ƙara kamata, haka har ta shigo cikin wasu gonaki, ananne tsoro ya tsananta gareta saboda kukan karnuka dake tashi, bata san lokacin da ta kwasa a guje ba ta manta da ciwon dake ƙafarta duk da tana jin zafin ciwon na ratsata. ta fito kan hanya kawai taga fitilar mota na haskawa, da fari kamar ba zata tsaya ba sai ta tsaya tana miƙa hannu don tsayar da motar, dole zata tsaya ta nemi taimako in ba haka bata san ina zatai ba, haka kuma bata san meke cikin wannan dajin ba, komai zai iya faruwa da ita. tana ta ɗagawa motar hannu, so take tai magana amma ta kasa, ga motar ita take tunkarowa, a wannan lokacin kuwa kan Turaki na ƙasa yana ƙaro volume na karatun qur'anin daya kunna, lokacin har ya ƙaraso inda take ba tare daya san da mutum a gabansa ba, a time ɗinne ta fahimci ko waye na cikin motar baya ganin gabansa, saboda haka cikin hanzari ta ɗaga ƙafarta da tayi mugun nauyi zata janye daga wurin, sai dai inaaa, kafin tai wani yunƙuri Motar Turaki ta daki gwiwoyinta ta kifo kan motar tasa. ta san sanda kanta ya ƙwalu a jikin motar, ta san lokacin da ta silalo ta faɗo ƙasa, taga kuma lokacin da tayoyin motar ke ƙoƙarin bi ta kanta. take ta sallama da rayuwar, yau dai tasan babu abinda zai hanata bin Umminta, zata je su rayu tare harda Addarta, zata bisu shikenan sun bar Kaka ita ɗaya. tana kallon tayoyin motar na ƙara motsi suna tahowa zasu talitse kanta, sai dai daga nan, ji da gani da numfashinta duka suka ɗauke. bata san me ya faru ba bayan nan, sai yanzu data farka, ta farka ta ganta acikin ɗakin asibiti, kan gadon asibiti, that means wanda ya bugeta mutumin kirki ne kenan?, shi ya kawota asibitin ko ya?, idan ba shi bane to wa ya tsintota daga cikin wannan dajin ya kawota nan?, ina Kaka?, ina Maijidda?, ina Yami?, ina Amir?, shin wanne hali suke ciki?. shin sun samu labarin inda take?, ko kuma suna can suna nemanta?, wacce amsa zata basu a lokacin da kowannensu yay mata tambaya?. duk ba wannan bama, idan ta miƙe yanzu zata koma gida, ta san kuma amsar tarin tambayoyinsu, ba zata ɓoyewa Maijidda komai ba domin ita zata kawo solution. abun ɗaya ne kawai ke cikin kanta a yanzu itace sallah, sallolin da bata yi ba a wancan ranar na la'asar da magriba da isha. to kwana nawa kenan yanzu?, sallar kwanaki nawa ne akanta?, wa zai bata amsa?, don tasan ba lallai akan lokaci aka sameta ba balle ta iya ƙiyasta wasu kwanakin, kuma dole zata rama sallolin dake kanta. ta kulle ido ta motsa ƙafafuwanta zata yunƙura ta tashi zaune sai taji tamkar zasu karye saboda sandarewa da kuma azabar ciwon da suke yi mata. kawai sai ta fashe da kuka, kuka sosai, likitan daya gama aikinsa ya tsaya akanta, tana jin yanda kallonsa ke shiga jikinta. baice komai ba har sai da ta tsaya da kukan dan kanta ta buɗe idon tana kallonsa, murmushi taga ya sakar mata tare da ce mata. "sorry". muryarta na fitowa da sautin kuka tace,"dan Allah zanyi sallah". murmushi taga ya ƙarayi sannan yace,"za kiyi sallah amma ba yanzu ba, ki bari ko zuwa safiya ne". sai ta koma tana bin ko'ina na ɗakin da kallo, agogo take nema taga lokaci. tace da shi,"me yasa to ba zanyi ba yanzu?". yana kallonta yace,"saboda ba za ki iya ba...". tun bai ƙarasa maganar ba ta kalle shi da idanunta da suka kawo ruwa ta katsesa da faɗin,"zan iya, Allah zan iya". tai maganar tana son fashewa da kuka. Dr Yusuf yace mata,"to shikenan tashi ga banɗaki nan ki shiga, can kuma jakar kayanku ce sai ki ɗau hijab aciki ga abin sallah can". ta kalli inda yayi mata nuni, ta maimaita kalmar jakar kayanku acikin ranta, ta juyo ta kalle shi yana niyyar fita tace,"dan Allah wa ya kawoni nan?". yace,"police da kuma wanda ya buge ki". ta maimaita kalmar a ranta kan tace,"dama ya tsaya?". yace mata,"ehh yana da imani shisa". hawaye na ƙara sauko mata a sanyaye tace,"Kakata fa?". ya juyo ya kalleta sannan yace,"kin fasa yin sallar ne?". ta girgiza masa kai tare da cewa,"a'a zanyi". ta faɗa tana so ta tashi amma tana jin ba zata iya ba, komai yayi mata nauyi kamar an danneta, kawai sai ta saka kuka. Dr Yusuf ya dawo yana bata haƙuri da faɗin,"na faɗa miki ba za ki iya tashi ba, akan aikina fa nake, zuwa wayewar gari insha'Allah da kanki za ki tashi bama sai an taimaka miki ba". bata bar kukan ba tace,"to idan ban kai goben ba fa naje nace da Allah me?, ni dai dan Allah ka taimaka min na tashi na sauke nauyin da yake kaina". Yusuf dai da yaga zasu yi daru da ita kuma ba jin duk wani bayani da zaiyi zata yi ba kawai sai ya sakar mata allurar bacci. baccin da bata farka a shi ba kenan ba har sai washegari da wajen ƙarfe goma, lokacin su Kaka sunzo, tana buɗe ido akan Kaka ta sauke wacca ke zaune kan kujera ta rafka uban tagumi. Maijidda kuma na tsaye jikin bango kana kallon fuskarta zaka san tasha kuka ta gode Allah, itama duk ta faɗa saboda tashin hankalin da suka shiga. Yami ce kawai me ɗan ƙarfin hali da take ta tausar Kaka akan ta daure ta saka abu acikinta tunda likitan yace zata farka. kuma kwana biyu Kakan banda ruwa babu abinda take sha, shima idan tasha ɗacinsa take ji. "Yami ba zan iya sa komai acikina ba sai yarinyar nan ta farka, yau fa kwana huɗu kenan, faɗa mana suke tana raye, ni dai ina tantamar hakan, gwara kawai a faɗa min gaskiya a bar ɓoye-ɓoye aini musulma ce na yarda da mutuwa". Yami dai tayi shiru bata ce komai ba, sai kallonta da ta maida kan Fillon, itama dai ta fara tantama akan maganar likitocin nan, ace kwana huɗu mutum bai farka ba kuma sannan ace
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243