Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 143

Chapter 143

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,231 words 0 views Progress saved
Download Book

yi, a haka sai da ta shanye guda ɗaya tass tukunna ya kafeta da ido yana kallonta da wani sihirtaccen murmushi. bata hanasa kamo hannunta me ciwon ba, ya tmbayeta,"yana zafin ko ya daina?". Tace,"yana zafi sosai dauriya kawai nake yi, kaine ina ta maka alama ka datse min hannu kaci gaba da masifarka, dan Allah ka mayar dani wajen likitan ya yanke min su na huta, kuma dan Allah ka rage masifa in ba haka ba wataran zaka iya ɓallani gaba ɗaya". ya shafo wuyansa yana wani irin murmushi da yake jin yana motsa ilahirin jikinsa da wani feelings na daban. sai taga ya sauke daga kan stool da yake zaune ya zauna gaban ƙafafunta, sannan ya ɗora kansa da hannunsa ɗaya kan ƙafafunta yace,"idan aka yanke kuma da wanne za kike wa mijinki ƙunshi yana kallo yana jin daɗi?, a barsu dai insha'Allahu zuwa safiya zasu daina zafin". ta ture kansa da ɗayan hannun tace,"ka ɗagani ba kyau". ya riƙe hannun ya mayar da kansa yana cewa,"naji, Allah kuma kika ƙara ce min ba kyau sai kin kwana a dakin nan yau". tai shiru tana sakin kukanta mara sauti, ya ɗago kansa haɓarsa kan gwiwarta yana kallonta sosai yace,"ai dama ranar nan kince min ni ke saki kuka, dan haka yi me isarki tunda yau Allah ya haɗa mu". da mamakinsa sai yaga ta saki kukan sosai, sai turesa daga jikinta take yi tana so ta tashi, shi kuma har ga Allah yau karo na farko kenan da yaji kukan nata na masa daɗi saɓanin da sai ya dinga jin kukan na haifar masa da jin zafi a zuciyarsa. har tsawon minti uku bai daina kallon yanda take da bakin kukan ba kamar yarinyar ƴar 3years, yasa wayarsa yana ta mata vedio, dan kansa dai yaji kukan ya fara taɓasa tukunna ya tashi ya kamota ya miƙar da ita. jikinsa ya janyota ya rungumeta yana lallashinta yana bata haƙuri, ita dai bata daina kukan ba kuma ba tai ƙoƙarin fita daga jikinsa ba. a ranta kuwa rayawa take yau babu abinda zai hanata faɗawa Maama irin wannan abinda yake mata. ya kai bakinsa saitin kunnenta ya kira sunanta, tana shagwaɓe murya tace,"ni Fullo sunana ba Fulani ba". Yace,"ba haka naga damar faɗa ba". Ya faɗa yana kai hannunsa saman sumar kanta. tasa ƙarfi tana ture shi tana faɗin,"dan darajan Allah ka ƙyaleni in fita, wallahi hakan da kake yi babu kyau, ni fa ba muharramarka bace, kuma idan wani ya shigo ɗakin fa?". yace,"zan bar ki ki wuce yanzu i promise, but you answer me first me yasa kika dinƙa taimakona?". ya faɗa yana janyeta daga jikinsa yana kallon cikin ƙwayar idonta, ta ƙanƙance ido tace,"taimako kuma?, wane irin taimako na maka ni kam?, ni ban taɓa maka taimakon komai ba, kaine ma ka taimaka min aka kulle Amir". ya matse tsintsiyar hannunta yana cewa,"kar na ƙara jin kin ambaci sunansa ko ba'a gabana ba". ya faɗa da sautin ɓacin rai da kuma kashedi me kyau. tace,"to ka sakeni in tafi". yace,"fara ban amsata tukunna, asirikan da kika dinga ɗaukewa akaina me yasa kika ɗauke su?, me yasa baki bari sun same ni ba?, kuma me yasa baki taɓa faɗawa kowa ba?". tai ƙasa da idonta tana so ta ƙaryata zancen nasa sai taji hannunsa a haɓarta ya ɗago fuskarta yana ɗagamata kai,"ehen am all ears, ba kuma na son ƙarya dan nasan komai". tayi narai-narai da idanu tace,"ni fa duk ban san me kake cewa ba, ni waye yace maka na ɗauke asiri akanka?". yace,"bakinki". ta waro ido waje tace,"da yaushe?". Yace,"ranar da kike bawa ƙawarki labari a asibiti, accident ɗinki na farko da na kaɗeki". tace,"da ma kaine ka kaɗe ni akace wani ne?". Kan yay magana ta tari numfashinsa da faɗin,"shima kana sane ka kaɗeni?". ya galla mata harara da cewar,"ehhh sai ki haɗa duka har marinki ki rama, yanzu amsa min tambayata". ta tankaɗe shi daga gabanta ta bar wajen da sauri, tana zuwa bakin ƙofa ya isa ya fizgota ya haɗeta da bango yana faɗin,"Allah you are going no where sai kin amsa min tun yaushe kika sanni?, kuma me yasa kika min asiri?". hakan yasa ta sakin kuka sosai, tana rantsuwar,"Allah ni ban taɓa saninka ba sai da na fara aiki a gidanku, sunanka kawai na sani ajikin takardar da akai maka asiri, amma wallahi bani nayi maka ba, banma san su waye ba jinsu nai kawai suna faɗa, kuma ma ai saboda idan na faɗa ba za'a yarda da ni ba shisa ban faɗawa kowa ba, ina tsoron kar ace ƙarya ne ni nayi maka, amma na rantse da zatin Allah bani ce nayi maka asiri ba". tai maganar idanuwanta a rufe, dalilin ba zai iya jin kukan ba ya kwantar da ita a ƙirjinsa yana shafa bayanta yace,"na yarda daina kukan cry cry Baby, kanki zai ciwo za ki zazzaɓi". tana fizgar numfashi da ƙarfi tace,"wallahi Allah bani bace kuma ban san su waye ba". ya ƙara yin ƙasa da murya very calmly yace,"ohh nace na yarda, na yarda ba ke kika min ba shikenan daina kukan haka, ko ba kya so na barki ki tafi?". da sauri ta girgiza kanta,"ina so". yace,"to inji kinyi shiru sai in barki ki tafi". ɗiff ta ɗauke wuta kamar ba ita ta cika ɗakin da kuka ba yanzu, ta lafe a chest ɗinsa tana jin yanda heart ɗinsa ke bugawa ba irin yanda ta san ainihin bugun zuciya ba, shima fuskarsa kwance akan gashinta ya lumshe ido, wayarsa na ta uban ringing bai ma san anai ba. har aka turo ƙofar ɗakin aka shigo daga shi har ita ba wanda yaji motsin buɗe ƙofar balle kuma motsin mutum. Hajiya Ramla tayi mutuwar tsaye daga inda take tana neman bango ta dafe, kafin dai tayi ƙarfin halin ɗaga ƙafarta da take jin kamar ta mutu ta dawo saitin inda zata ga fuskar wacce yake rungume da ita haka, bata san ba ko matar tasa ta dawo basu sani ba, sai dai tana zuwa ganin fuskar Fullo wacce idanuwanta ke lumshe yasa tayi saurin ja da baya tana dafe bango da furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. wannan dogon salatin da taja cikin razani shi ya dawo da Turaki cikin duniyarsa, ya buɗe ido a tsoroce jin muryar Mum akansa, ya kalleta ya juya ya kalla ƙofa sannan ya juyo ya kuma kallonta, sai kawai ya saki Fillo yana ja da baya, lokaci ɗaya sai ya dawo kamar wanda ya kashe ɗan sarki aka gurfanar da shi a gaban sarki. Mum ta bi ɗakin nasa da kallo sannan ta tsayar da kallonta akansa, ta tattaro yawun bakinta da ƙyar tace,"Babana, me nake gani haka?, kai ne da kanka tare da wadda ba matarka ba?". sai kawai ta ɗaga hannu ta wanke shi da marin da ya kai fuskarsa ƙasa, da kanta ta ɗago da shi ta ƙara wanke shi da wani sabon marin da ya kaisa ƙasa gaba ɗaya gwiyoyinsa suka zube a gabanta. Zaytuna tasa hannu ta rufe bakinta tana fashewa da kuka, tun ɗazu take kiransa a waya bai ɗaga ba, abinda take ta so ta faɗa masa kenan ga Mum nan. Fullo dai tuni ta durƙushe a wajen tana kuka sosai kamar ranta

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243