Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 153

Chapter 153

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,231 words 0 views Progress saved
Download Book

wannan waɗanda ke zaune anan Gombe har sun zazzo. saboda manyan yayyansa da ke can taraba dole aka fasa kaisa a ranar akace a bari sai gobe, a washegari da safe kuwa ƙarfe takwas na safe gida ya cika maƙil da ƴan'uwan Hayyo maza da mata, lokacin har anyi masa wanka jira ake babban wansu yazo ai masa sallah. lokacin da aka ɗauko gawar Hayyo za'a fita da ita a lokacinne mutane da dama da basu sami damar kuka ba suka saki nasu, saboda bala'in tausayin Fullo wacce ke ta kuka tana kiran a bar mata Abbanta dan Allah, sai da ƙyar Ammi ta iya ruƙota Hajiya Madina ta ƙwace hannunta daga kan makarar da ta yiwa mugun riƙo, sannan ne aka samu aka fita da gawar Hayyo daga parlon, kuma lokacinne Fullo ta yanke jiki ta faɗi bayan ta ƙwalla wata razananniyar ƙara da ta amsakuwa a gidan gaba ɗaya. aljanun da ba'a santa da su ba suka tashi.... *Vote, Comment and Share.* [9/3, 19:37] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *43* *Taraba Satate, Wurkum district, Late Alhaji Aminu Barkinɗo Residence.* tafkeken gida ne me irin ginin gidan sarauta, sai dai ginin irin na zamanin da ne bana yanzu ba, but an ɗan sabunta shi ba kamar yanda yake ainihinsa ba. ƙofar gidan na marigayi tsohon Hakimin Wurkum danƙare yake da jama'a kace ɗaurin auren wani babban mutum ake ko kuma za'a ƙara yin naɗin sarauta ne. daga cikin rumfar tempol ɗin da akayi, Maudo ne zaune akan kujera yasha rawani yana amsar ta'aziyya daga bakunan mutane da dama, shi ne Babban ɗa a wurin marigayi Alhaji Aminu Barkinɗo, kuma shine wanda ya zauna a hannun mahaifiyar Hayyo a lokacin da ta na raye, domin shi tasa mahaifiyar ta rasu, kuma tun bayan rasuwar mahaifin nasu ya maye gurbin kujerar tasa har zuwa wannan ƙarni da muke ciki. daga cikin gidan, ɗumbin mutane ne ƴan gaisuwa ke ta hada-hadar shige da fice a ƙaton tsarkargidan da yay kusan filoti biyu, kana kallon yanda aka kakkasa ɓangare ɓangare zaka san family house ne. wata farar tsohuwa tukuf ta fito daga wani ɗaki tana dogara sanda, sai da suka ƙaraso tsakiyan tsakar gidan sannan ta tsaya tana kallon mai yi mata hidima wadda ke biye da ita a baya tun fitowarta, hannunta riƙe da ƙwaryar fura babba, ita ɗaya ta rage acikin matan Alhaji Aminu Barkinɗo, cikin su uku da ya aura ita ɗaya tayi tsawo rai haka. cikin yaren fulatanci tace da Hadimar,"ki nemo Gaji ki basa furan ya kaiwa Dottijo, tun ɗazu ya aiko Manga kuma ba'a samu an kai masa ba, kuma ƙila zai sha tare da baƙi ne, yi maza du Allah". Hadimar ta wuce da sauri tabi dogon soron da zai kai ka wani babban fili kafin ka fita zuwa waje. Dada ta waiga tana kallon masu fitowa daga ɓangaren Hakimi, ta ƙwala kiran,"Munyoɗo". sai da ta kira sau biyu tukunna wata farar dattijuwa ta fito da sauri tana amsawa, tazo gabanta ta rissina tana faɗin,"Dada gani, lafiya kika fito ke ɗaya?, kuma kin tsaya ai a rana, me kike da buƙata?, ina Petel din?". tayi maganar tana kamata ta matsar da ita daga cikin ranar. ta kalleta ta cikin glass ɗinta tace,"ina wannan shike, amnn mata na wurin Hayyo?". Munyoɗo tace,"wacce daga ciki Dada?". Dada ta ɗan ɓata fuska da muryar ƙorafi tace,"wannan yaro dai Allah ya jiƙan shi kawai, du yaje ya haɗo mata da yawa in ka tashi neman ɗaya sai kayi ta faman kwatance". tayi tsaki sai kuma tace,"wasu sun ƙara zuwa ne?". Munyoɗo tace,"ai Dada jiya duk sun gama zuwa, su bakwai ne yanzu sauran huɗun ance sun rasu, suna babban parlo yanzu haka". Dada ta girgiza kai alamar Allah ya kyauta sannan tace,"to wannan Balarabiyar za ki kirawo min". Munyoɗo tace,"tom Dada bari na duba". ta faɗa tana juyawa ta nufi ɓangaren da yake nanne na mahaifiyar Hayyo, ta shiga babban parlon da ya tara ƴan zaman makoki, ta dinƙa wuce su har ta ƙetara inda Ammi da Ummi suke zaune tace da Ummi,"Dada tana kiranki". Ummi ta amsa da to tana yunƙurawa ta miƙe, Ammi ma ta miƙe tana faɗin,"kin san Allah na sha'afa gaba ɗaya Dada tana nemana". tare suka fito gaba ɗaya, suka tadda har an ajiyewa Dada kujera ta zauna akai, suna zuwa ta ɗaga sandar hannunta ta bugawa Ammi, Ammi ta kauce tana faɗin,"kiyi haƙuri baƙi ne suka tsayar da ni". Dada ta harareta ta cikin glass bata ce mata komai ba, ta mayar da dubanta ga Ummi da ke tsugune a gabanta tace mata,"kije ki sako mayafinki mu wuce asibiti, ance tun shekaranjiya baki koma wurin yarinyar nan ba, ban sani ba ko isashshen hankali ne baki da shi". Ummi ta miƙe cikin sanyi jiki ta wuce, Dada ta kalla Ammi tace,"kije ɓangaren Giɗaɗo kice da matarsa ta bayar da ferfesun kaji da nace ayi, na santa da ɗan banzan cin yajin jaraba, idan ta san yayi yaji da yawa to ta zubar da shi ba mayu ne zasu sha ba, ta ɗora sabo na mara lafiya ne". har Ammi ta wuce sai kuma ta ƙara tsayar da ita,"kice da Belɗo ya fito da mota zai kai ni asibiti, yace da Safara'u taje ta haɗa min kayana a kawo min yau can ina kwana". tana tafiya sai ga wata hadima daga bangaren Modibbo ta fito, tayo wurin Dada da sauri tana zubewa tare da cewa,"Allah juttin balɗe ma, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana Dada, da akwai abunda kike buƙata ne ayi miki cikin gaggawa?". Dada ta dubeta tace,"a'a bana buƙatar komai". Hadimar bata tashi ba ta cire takalmanta ta zauna akai ta shiga matsa ƙafafun Dada. lokacin maƙwabtansu suka shigo, da girmamawa matar ta tsuguna tana gaida Dada tare da ƙara yi mata ta'aziyya, Dadan ta amsa tana yi mata godiya sosai. matar tace mata tare da mijinta suke, Dada tace taje ta shigo da shi,ba jimawa sai gasu tare, suka gaisa da Dada wadda ke ta sanya masa albarka. "Dada wajen kuma da zafin rana da kin koma daga ciki". tace da shi,"zanje dubo yaron Hayyo ne, zafin mutuwar uban ya taɓata shi yana can asibiti kwance rai hannun Allah, Belɗo nake jira yanzu zai fito". daga nan suka yi mata sallama suka wuce. a ƙofar gida sanda su Ummi suka fito zasu tafi motar su Hajiya Ramla tayi parking, tun ranar ɗaya da suka zo suka koma sai yau suka dawo, Ummi ta ƙarasa wajensu tana yi musu barka da zuwa, su kuma suna ƙara yi mata ta'aziyya, Ummi tayi musu godiya sosai da sosai akan irin kyatatawarsu gare su. Hajiya Madina da damuwa a tare da ita tace da Ummi,"to ya jikin Fillon?". Ummi tace,"Alhamdulillahi da sauƙi, yanzu ma can zamu je, wataƙila ma dai zuwa dare su sallamota". Hajiya Madina ta kalla Hajiya Ramla tace,"to ko ni na bisu ne?". Hajiya Ramla tace,"ah ki dai bari mu shiga muyi gaisuwan, idan muka fito tafiya sai mu biya ta can ɗin ko". Hajiya Madina tace,"to shikenan". sai kuma tace da Ummi,"Me Babban suna yana nan ɗin ko yana can asibitin?". Ummi tace mata,"acan asibitin yake kwana ai, ya hana kansa natsuwa kwata-kwata, jiya ma nayi ta fama da shi kan ya

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243