Chapter 230
Chapter 230
ƙarshe ma take ce masa. _"to ni ina ta lissafina ma, wa ya sani ko ba lallai ba ne na kai wannan lokacin, Allah dai ya san adadin shekarun da ya ɗiba mana a rayuwa, ni dai idan na tafi ku yafe ni Me Babban Suna ko da nayi muku laifi bisa kuskure"._ sai kawai yaji ya rasa dukkan dauriyarsa, ya manta shekarunsa, yana tunawa cewar shi fa ɗan Maamansa ne, kuma Maaman ta rasu a yau, bai san lokacin da wani matsanancin kuka ya kubce masa ba, ya shiga rero shi tamkar yaro sai dai gaba ɗaya babu sauti, illa tarin ruwan hawayensa da ke sauka su na jiƙa bedsheet ɗin. har aka tura ƙofar ɗakin aka shigo tsakanin Turaki da Khalil babu wanda ya sani balle ya ɗago. Fillo ta ƙarasa ta zauna akan gadon, tana zama kuma Turaki ya ɗago kansa ya ɗora akan ƙafafunta, ya damƙe cinyoyinta yana wani irin girgiza. sai taji sabon kuka yazo mata, tunawa da tayi Nihal na can an rirriƙeta sai surutai take yi. saboda haka sai ta nutsa yatsunta acikin kansa tana motsa yatsun. *BAYAN SATI BIYU.* [9/7, 03:10] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *60* *Jarabawa daga Mahaliccin mu.* Rayuwa tana cike da nasara da kuma faɗuwa, kuma akwai lokutan da gwaje-gwajen da ake yi mana kamar ba za su ƙare ba. A cikin Alkur’ani me girma, akwai ayoyi da dama da Allah ya yi magana a kan hanyoyi daban-daban da za a gwada mu, amma kuma ya ba mu ƙunshin kulawa da zai taimaka mana mu bibiyi waɗannan lokutan masu wahala a gare mu. Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce:“Babu wata musiba da za ta samu musulmi face Allah ya kankare masa wani abu daga cikin zunuban shi, ko da kuwa tsinuwar ƙaya ce”. (Bukhari Wa Muslim). haƙiƙa jarabawa ba azaba ba ce daga Allah, tana daga cikin rahamarsa marar iyaka. Musulmi ko wanda ba Musulmi ba, babu makawa kowannen mu yana fuskantar jarabawa a rayuwarsa. Rayuwa ba gadon wardi bane ga kowa, Akwai mutanen da ke fama da talauci, akwai masu fama da lafiyarsu, sannan akwai masu fama da danginsu, akwai masu fama da mutuwa a jere a jere. Jarabawar ubangiji ta bambanta ga ɗaiɗaikun mutane daban-daban, an yi su ne bisa la'akari da irin ƙarfinmu da rauninmu. Abubuwan da suka zama kamar gwaji a gare ni, wataƙila ba za su dame ku ba, nima akasin hakan. tambayar gama gari da kowa ke yi a lokacin da ya shiga wani hali shi ne; me ya sa Allah ya sa na shiga cikin wannan halin? Me ya sa ba zan iya zama mai farin ciki a ko yaushe ba?, Menene na yi don cancantar wannan jarabawar? Me yasa Allah ya jarraba ni?. kuma rashin sanin amsar waɗan nan tambayoyi wani lokacin yana iya nisanta mutum daga imaninsa. jarrabawa na iya haifar da mummunan tunani mai tayar da hankali wajen mutum ya aikata saɓo, kamar faɗin Allah ba ya so na!. ko ma mafi muni mutum yace Allah ba ya yi mini adalci(astagfrullah). Amma Allah shi ne Al-Adl, Mai adalci, kuma shi ne Ar-Rahman, Mai jin ƙai, wanda ba ya ya nufin cutarwa ga bayinsa, face yana son alheri a gare mu. Akwai hikima a yanayin da ya ke sa mu a ciki, duk abin da muke buƙata mu yi shi ne haƙuri. Akwai dalilai da yawa a cikin Alqur’ani da hadisi da suke taimaka mana wajen amsa tambayar dalilin da ya sa ake jarraba mu. An halicce mu ne domin mu bautawa Allah, wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa ake jarabtar mu. tabbas an halicce mu ne domin mu bautawa Allah, kuma dukkanmu mun yi alƙawarin yin haka kafin a aiko mu a duniyar. Jarabawa hanya ce a gare mu don cika wannan alƙawarin. jarrabawa ita ce hanyar da Allah ya ke bambanta mu, domin tana taimakawa wajen bayyanar da imani da rashin imani. Allah yana jarrabar mu, ya tsarkakemu ya kuma wanke mana zunubai. jarabawa gwaji ce ta maye gurbin wani mummunan bala'in, tabbas da munsan musibun da Allah yake kare mu, da ba za mu taɓa rasa sallah ba, kuma ba za mu taɓa son ɗauke goshin mu daga sujjada ba. Gwaje-gwajen da ke ɓata mana rai na iya zama nau'i na kariya daga wani abu mafi muni da wataƙila ya same mu. Allah yana so ya tsarkake mu, daga soyayyarsa da rahamarsa, domin mu samu ba Aljanna kaɗai ba, har ma da mafi girman darajar Annabawa da salihai. Gwaje-gwaje su na fallasa kurakuran mu da kasawarmu, kuma sanin hakan yana ba mu damar mai da hankali da himma wajen gyara waɗannan ɓangarori na halayenmu. Allah yana jarrabar wanda yake so. Annabi(SAW) yana cewa: "Duk lokacin da Allah ya nufi mutum da alheri, sai ya sanya shi cikin tsanani".[Bukhari]. me yasa?, domin idan bawan ya amsa jarabawarsa da haƙuri, da gamsuwa da hukuncin ubangiji, hakan yana kusantar da bawa zuwa ga Allah, Kuma Allah yana son masu haƙuri. Ibn Al-Qayyim (rahimahullah) ya ce idan aka yi mana jarrabawa, muna fuskantar zaɓi guda biyu; muyi haƙuri ba rashin haƙuri ba. muke sauraren Alqur'ani da yawaita ambaton Allah saboda wadatar zuci, domin karanta alƙur'ani yana ba da wadar zuciya, addu'a don neman taimakon Allah, da ƙarfinsa, da samun sauƙi daga jarrabawa. mu tunatar da kanmu jarrabawar da Annabawa suka yi, sun ba mu kyawawan misalai na juriya. mu tuna cewa kowanne mutum guda ana gwada shi ta hanyoyi daban-daban. mu tuna babu wani abu a cikin wannan rayuwar da ke dawwama, don haka jarrabawar za ta ƙare insha Allah. domin ko acikin alƙur'ani Allah yace,"Lallai ne tare da kowane wahala akwai sauƙi". ubangiji ba ya ɗaurawa wani rai face abin da zai iya ɗauka, Allah ya amince da mu, don haka mu ma muna buƙatar mu amince da iyawarmu ta cin jarabawa. Allah yasa mu da ce!. ƙarfe goma na safe a lokacin, Ilham ta fito daga ɓangarenta tare da wata yarinya da ba zata wuce shekara 8 ba. yarinyar ƙanwar Fulani Azima ce, aka bata ita kafin akaita makaranta, kasancewa yarinyar ta gama primary a halin yanzu. yarinyar na riƙe ne da jakar Ilham, tabi bayanta zuwa baƙar motar da taga ta shiga, sabuwar motar da me martaba ya bata kyautarta. a san da suka iso bakin gate domin fita, a sannan ne Fillo ke baro wajen Baba Me gadi da turtsetsen cikinta, da lokacin haihuwarsa kawai ake jira. Ilham ta zuge glass su na gaisawa da Fillo, da siririyar dariya a fuskarta tace da ita,"kin ga kuwa yacca kika koma?, Allah each and every day cikin nan kumbura ki yake ƙara yi". Fillo na kallonta tace,"ban da sharri dai". "Allah babu zancen sharri, jiya da muka ci dinner ba ki kumbura haka ba". Fillo tayi murmushi ta ce,"in ace ana mayar da cikin jikin wani ai ke zan mayarwa, ke ma ki ɗanɗana, ko da yake kwana nawa ne Allah na tuba, ina daga balcony zan ke hango ki a field kina aikin patrol". Ilham tayi dariya sosai tare da cewa,"Allah dai ya raba lafiya, ni ban ma fidda ran ba za ki haihu ba a yau". sai kuma ta nunfasa ta ce,"zan je gida ne, an yi min waya jikin Mami ya ƙara tashi". jikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243