Chapter 73
Chapter 73
wurin ta kunna turaren ƙamshi. Turaki yayi sallama a ƙofar ɗakin idonsa na mannewa akan yagalgalallan labulen ɗakin, Kaka ta taso da sauri tazo ta buɗe labulen tana faɗin,"Barka da zuwa ranka ya daɗe". ta yaye masa labulen shi kuma ya shiga, sai bayan ya zauna sun gaisa da Kaka sannan ya fara tunanin acutual abinda ya kawosa. tun bayan gaisawar su da Kaka ya kafe ƙofar ɗakinta da ido, ta yanda ba zaka taɓa fahimtar ga inda yake kallo ba, sama da mintina goma shiru bai ga alamar Fillo ko inuwar Fillo zata fito daga cikin ɗakin ba, kuma motsi kaɗan zai ji daga waje sai ya juyar da ƙwayar idonsa zuwa bakin ƙofa yaga ko ita ce, but sai yaga babu kowa. ya sauke numfashi a daidai sanda zuciyarsa ke ayyana masa tasirantuwar wani abu, kuma lokacin ne Maijidda ta shigo ɗakin tana ta mita. ganinsa yasa tai saurin zube gwiwoyinta a ƙasa tana gaida shi. bai amsa mata da baki illa kansa kawai da ya ɗaga mata. ya miƙe ya yiwa Kaka sallama ya tafi, Kaka ta bawa Maijidda furar da ta dama ta bisa da ita. daga can ɗakin Hajiya Madina Fillo ce zaune a gabanta, kanta a ƙasa, idanuwanta sun cika da ruwan hawaye, tana jin kanta na mugun sara mata kamar zai faɗo ƙasa, maganganun Hajiya Madina nema suke su juyar mata da dukkan wani tunani nata, a yanda dukkan zancen Hajiya Madina suka ratsa jikinta bata jin zata iya ko da ɗaga ɗan yatsa guda a yanzu dai. Hajiya Madina da idanuwanta ke manne akan Fillo itama nata idanun na zubar da ruwan hawaye tace,"wannan shine dalilin da yasa nace miki ina so ki nutsu kiyi karatu, kuma wannan aikin shine wanda nake faɗa miki zaki yi min Fillo, tun a kallon farko da nayi miki zuciyata ta faɗa min zaki iya, hakan yasa na zaɓe ki, ina fatan kuma zaki warware komai cikin sauƙi ba tare da abunda nake gudu ya faru ba". a wannan karon da Hajiya Madina tayi magana, sai Fillo taji kamar tana neman ta tarwatse gaba ɗayanta ne. manyan idanuwanta suka maƙale a kan ƙafar Hajiya Madina dake cikin wani tsadaddan takalmi, so take ta haɗe dukkan maganganun Hajiya Madina wuri guda sannan ta watsar da su a gefe ɗaya, domin bata tunanin akwai ta yanda zata yarda cewar wannan jarumar matar dake gabanta ba itace mahaifiyar Turaki ba. amma dolenta a yau kuma a yanzu ta yarda da hakan, ta yarda da wannan macen ba ita bace asalin mahaifiya wacce ake kira uwa a wajen su Turaki ba. "ban san me zance miki ba Maama, abu ɗaya kawai da na san ya zama dole shine jinjinawa, dole zan jinjina miki, kamar yanda na jinjinawa masu farautar rayuwar Turaki". ta faɗi hakan tana me ɗagowa ta sanya idanuwanta cikin ƙwayar idon Hajiya Madina, sannan ta iya miƙewa jiki a saɓule tana jin kamar ba zata iya tafiya ba, ta bar ɗakin tana barin Hajiya Madina a cikin tsananin tashin hankalin da ba zai misaltu ba. a parlo ta tarar da Samha zata hau stairs wurin Maama, tana jinta tana yi mata magana tayi mata banza bata ko kalleta ba. ta baro side ɗin cike da mamaki da tunani kala-kala acikin ranta, kuma cike da tsoron ɗan'adam, ko waye shi kuma ko ya kuke da shi. a coumpound ta tarar da Ɗausiyya acan wajen bakin famfo tana wanki, ta ƙarasa wurinta tana ce mata. "idan teacher yazo ki faɗa masa bani da lafiya, ba zan iya karatu ba yau. please ki basa assignment ɗina kar yay zaton ko saboda shi naƙi zuwa". Ɗausiyya na kallonta tace,"tun jiya kike kuka Fillo, kuma na tambaye ki kince ciwon kai ne kawai, ni dai wallahi ban yarda dake ba. dan Allah ki faɗa min ko da wata damuwar, mun riga fa mun zama ɗaya". Fillo tace,"kawai bana jin daɗin jikina ne, zanje nasha magani jiyan ban sha ba dama. nasan Adda Zaytuna zata neme ni kice mata Kaka ce tayi kirana". tana faɗar haka ta juya zata bar wurin, lokacin ne motar Zaytuna tayi parking a compound ɗin tana fitowa daga cikin motar, ta ƙwala mata kita hakan yasa Fillo dakatawa da tafiyar ba don taso ba. taje wajen motar tana yiwa Zaytuna sannu da zuwa, Zaytuna ta tsaya tana kallonta da son karanto matsalar dake damunta. "what is the problem?". Fillo ta girgiza mata kai tana faɗin,"nothing Adda". yanayinta kaɗai shi zai ƙaryarta furucinta, Zaytuna tace,"ki ɗauko leda a backseat ki biyo ni da shi". ta faɗi hakan tana wucewa ta barta a wurin. ta ɗauko ledan kayan dake rinjayar ƙarfinta. ko da ta shiga part ɗin su Zaytuna bata sameta ba don haka ajiye kayan kawai tayi ta fito, don yanzu ita sam bata son abinda zai kaita wannan part ɗin ita ɗaya ba tare da wani ba, tun abunda ya faru a jiya take jin tsoron ƙara shigowarsa. haka ta sakko daga upstairs ɗin zuciyarta cike da tunani kala-kala. ta biyo ta corridor ɗin da zai fitar da kai ta baya, sai dai tana zuwa wajen ƙofa taja tayi turus tayi saurin laɓewa saboda abinda ta gani da kuma abinda take ji. tsabagen girgiza da Al'amarin bata san lokacin da ta zube a ƙasa ba tana saka hannu ta toshe bakinta gudun kar numfashinta dake neman tsarƙewa ya fallasata. ta rumtse ido da kyau cikin ranta tana ta adu'a Allah yasa kar a ganta, tayi shiru tana sauraron dukkan zantukan da ake yi, lokaci ɗaya ta ƙara girgiza taji kamar kunnenta ba daidai yake jiyo mata ba, cikin azama ta miƙe tabar wajen da sauri ta koma ta parlo ta bar side ɗin gaba ɗaya sai haki take yi. ta jima a compound zaune a wajen flowers tana ta mayar da numfashi, kafin ta iya miƙewa ta nufi part ɗin su Turaki, cikin sanɗa kamar wacce ke gudun wani ya ganta. tana shiga ta tarar da Khalil a parlo yana kallo, ta tsuguna ta gaida shi cikin rasa makamar abinda zata ce ya kawota. sai kuma taji Khalil ɗin yace,"ke Maama ta aiko?". da sauri ta ɗaga masa kai tace,"ehh". yace,"to kinga ba wani gyara ne me yawa ba, toilet kawai zaki wanke min kinji, yaron dake mana aiki ne bai da lafiya". ta miƙe tana cewa,"tom Hamma". Khalil ya bita da kallo har ta ɓacewa ganinsa, ganin yacca take tafiya kamar mara gaskiya. bata ɗauki lokaci ba ta kammala wankin toilet ɗin Khalil, tana gamawa kuma ta faɗa bedroom ɗin Turaki, da shigarta shima ta wanke nasa sannan ta kimtsa ɗakin gaba ɗaya, ta saka masa turare me ƙamshin gaske. kwalbar turaren dake kan dressing mirror ta ɗauka ta riƙe a hannunta, design na kwalbar yayi matuƙar burgeta, sai dai ƙamshin har yanzu bata ƙaunarsa, kamar wacca taga kashi haka take aikin yamutsa fuska still tana riƙe da kwalban, can kuma sai ta saki kwalban ya faɗi ya fashe, ya fashe a sanda take ƙara saka ƙasan takalminta ta murje kwalban sai ɓata rai take. ƙarar fashewar ya haɗe da rufe ƙofar ɗakin, ta ɗago kai da sauri tana kallon door ɗin sai ganin Turaki tayi ya jingina jikin ƙofar, ya rungume hannayensa a ƙirji yana kaɗa one
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243