Chapter 111
Chapter 111
nishi hawan jininka zai tashi, inga me zaman jinyarka yau". tana gama faɗar hakan ta kama hannun Turaki, kamar wani ƙaramin yaro haka ta ja shi suka fita daga parlon Baffa na bin bayanta da kallo, ko kaɗan bai mamakinta ba dan dama yasan za'a rina, in ace dai Turakin yana son yarinyar yasan babu abinda zata ce balle har ta tada jijiyar wuya haka, amma akan hakan yau ɗaya har tana faɗar wai yana ƙuntatawa ƴaƴansa, when akai haka?. acan parlonta ta tarar da duka yaranta zaune sunyi jungum-jungum, Khalil da Nihal da Zaytuna, Samha da Sameer basa nan dan basu dawo daga ƙasar da suka tafi ƙulla mugun nufinsu ba. ta shigo tana ta masifa, Khalil ma yay tsaki yace,"gaskiya, gaskiya abinda Boɗejo tayi bata kyautaba sam. wannan wane irin aure ne tsakani da Allah?". Nihal ma na turo baki tace,"yanzu dan Allah duk burin da muka ci akan auren Hammah sai azo mana da shi a irin haka?, shirin me muka yi tsakani da Allah, ni wallahi wannan tsohuwar dama ta mutu". Zaytuna dai ba tace komai ba illa kallon Turaki da take tayi ƙwayar idonsa kamar ba nasa ba. Nihal ta miƙe ta isa kusa da shi tana ɗora hannunta akan nasa tace,"Hammah kai kace kana son auren da har tai mana wannan shirmen?". bai ce komai ba, lokacin Hajiya Madina ta ƙaraso wajen riƙe da cup a hannunta da ruwan sanyi aciki, ta zauna tana tallafo kan Turaki ta bashi ruwan ya sha. bayan ya sha ta ajiye cup ɗin tana faɗin,"suje can suyi bikinsu su kaɗai, ni da ƴaƴana dai babu mai zuwa, wanda ya fasa cewa ina baƙinciki ba ɗan halak ba ne. kuma kaima ana ɗaura auren kayo kwana ka dawo gida". Nihal na matsar ƙwalla tace,"yanzu Maama sai kace bamu da gata sai ayi bikin Hamman'mu a haka babu shagalin komai?, duk fa ina ta cewa friends ina idan Hammanmu zai yi aure kowa zan gayyace shi. shi Baffan dan tana babarsa kawai kuma sai ya wani kama biyewa rikicin tsufanta, ni taja ma wallahi har Ilham ɗin na tsaneta, ƙilan ma harda wannan munafukar Babar tata aka haɗa baki". Hajiya Madina tace,"kwantar da hankalinki Nihal, shi da yake da ikon auran mata har huɗu, Allah ya kaimu nan da ranar da zai hango zaɓin ransa. anan za'aga inda ake aure, lokacin zamu yi namu shagalin bikin akan matar so, kuma ko a yanzu ina da arziƙin da zan iya yin bikin da zaici uwar nasu acikin kwana biyu cal, sai dai ba zan ɓarnatar da dukiyata ba akan auren matar shige". ta kalli Khalil tace,"kaima uban ƴan ladabi da biyayya, ka sake nai kiciɓis da kai zaka je wurin ɗaurin aure gobe babu abinda zai hanani sa maka kafa na fyaɗeka a ƙasa, in taka ƙafar in karya banza". Nihal tace,"dama ni wallahi babu inda zanje dan ɓuya ma zanyi ko Baffa ya kira wayata Allah ba zan ɗaga ba. dan dana hau whatsapp naga Marfu'a(Yayar Ilham wadda itace ta farko a ƴaƴansa mata), ta ɗora invitation card na dinner da cocktail ranar saturday da sunday". Hajiya Madina da har yanzu ta ke a fusace tace,"sa ji uwar kunya kuwa, dan gobe ma zamu bar ƙasar ni da shi, sai su nemi uban da zai yi replacing angon, ai insha'Allahu duniya sai ta gane auren cusa kaine, ango ba so yake ba". tana kallon Zaytuna tace,"kema uwar rawar ladabi da biyayya, Allah sa inga kin shiga lamarin bikinsu kiga asalin ɓacin raina". ta faɗa tana maida hannunta kan goshin Turaki da take jin zafin kan na ratsa fatar hannunta, a lokacin Turaki ya buɗe idonsa yana kallonta muryarsa a raunane yace,"Maama da gaske ne kun fito da yarinyar nan ta ɓata?". ta ke Hajiya Madina ta fashe da kuka tace,"ko dan wannnan dalilin tashin hankalin da nake ji ai yaci ace a tsayar da maganar auren ɗana?. banda ma dai Baffan Baffa ne ai sai ya miƙe tsaye yace ko za'ai a bari aga yarinyar mutane dana fita ta ɓatar tukunna, amma har shine yana min tsawa yana cewa babu ruwan auren ɗansa da ɓatan yarinya. yanzu fisabillah me Kakar yarinyar nan zata ɗauke ni?, ba sai su koma min kallon matar banza ba azzaluma na ɓatar musu da ƴarsu nazo ina shagalin bikin ɗa, wallahi ni dai sanyin Baffanku ba komai bane fa ce cutarwa". ya rumtse idonsa ya buɗe tukunna ya ƙara cewa,"garin ya akayi ta ɓata?". nan ta kwashe labarin komai ta ba shi. "to su police ɗin suna cewa wai sun fi tunanin kidnappers, ka faɗa min Hammah idan kidnappers ne tuni basu kira waya ba, amma fa shiru shiru har zuwa yau babu wanda ya kira waya, ko'ina an duba babu ita kamar ɓacewar aljani, har yanzu dana sanin fita nake da yarinyar nan, dan Kakarta da wanda zata aura zasu ga kamar da gangan hakan ya faru, kasan zuciya bata da ƙashi". ta faɗa tana kuka sosai. Idonsa a lumshe yace,"ki daina kuka Maama, insha'Allah an kusa a ganta". dukansu suka amsa da amin. sannan ya miƙe yace,"zanje in kwanta, kaina yana ciwo sosai". tace,"tafi ɗakina, kuma ka cire damuwar komai a ranka. yanda kake da gatanka zakai auren gata nan da wani lokaci insha'Allah. Dikko ne yay sirika ba Madina ba". Turaki ya wuce ya hau upstairs yana jinsa kamar ba shi ba, yana jin komai kamar a mafarki. kuma kafin ya kwanta sai da ya kira Bello ya sanar masa, tsaban shock Bello ashar ya ɗura a lokacin, har bai san sanda yay formating document da yake haɗawa ba. kuma Turaki bai jira cewarsa ba ya kashe wayarsa. *Washe gari, Juma'a, Masarautar Kaltungo, Ƙarfe Ɗaya da rabi na rana.* ana idar da sallar juma'a a masallacin aka ɗaura auren Muhammad Habib Lateef da Rumana Hashim Lateef akan sadaki dubu ɗari uku. ɗaurin auren da ya samu halarta manya manyan ƙusoshin ƙasar nan, dan duk wanda yake da faɗa aji a ƙasar nigeria da wajenta sai da Mai Martaba ya gayyace shi ɗaurin auren, kuma cikinsu babu wanda ya turo wakilinsa duk da kansu suka zo. duk girman masallacin fada sai da mutane suka cika shi taf, ciki da wajensa babu masaka tsinke, ango dai yana tare da mahaifinsa dan babu abokinsa ko ɗaya, Bello ma da yace zai biyo jirgin safe Maama ce tayi sai taci ubansa matsawar yazo. ango dai kamar ba ango ba dan fuskarsa babu walwala, ga shi dai acikin mutane kuma inda ake ɗaura aurensa, amma hankalinsa gaba ɗaya na can kan Fillo, ina take? da kuma halin da take ciki. bayan gama ɗaurin aure aka tafi reception, inda ɗumbin jama'a suka ci sukai hani'an, dan babu wanda zai ce bai goge haƙori da naman kaza ba. ana dawowa daga reception kuma aka koma can gidan mai martaba, cikin masarauta kenan, duk ta yanda Turaki yaso ya zame ya zille ya tafi gida abin yaci tura, dan Baffa na riƙe da hannunsa sai nunawa jama'arsa shi yake cike da tsantsar farin cikin da ba zai misaltu ba, shi kansa Turakin sai da yaji tausayin mahaifinsa, bakin Baffa sam yaƙi rufuwa, da zarar sun gaisa da mutum zai nuna masa Turaki yace,"shine babban ɗan nawa, asa masa albarka". haka
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243