Chapter 233
Chapter 233
zasu ce ba su taɓa irinta ba a tsawon zaman su, hirar da ta yiwa kowannensu daɗi matuƙa. kan Fillo na saman ƙirjinsa yayin da yake shafa gashin kanta, duk hirar da suke yi muryarta na fitowa ne tana ratsa dukkan ɗakin a hankali, cikin wani amo na rauni da ya gaza ɓoye dauriyar ciwon da ke cinta. ana sallar magriba ciwon naƙuda me tsanani ya ɓallewa Fillo, lokacin tayo alwala kenan ta fito daga banɗaki, tayi saurin dafa bango tare da duƙawa a wajen tana dafe bayanta, a lokacin wata azaba ta tsarga jikinta, sai taji numfashinta kamar ya tsaya cak a maƙogoronta, taji kamar duk wani ɓurɓushi na halittar jikinta yana barinta gaba ɗaya. ta rumtse ido na tsawon mintuna tana ambaton Allah cikin wata rarrauniyar murya, wani sabon bala'in zafi taji ya fara bin dukkan jijiyoyinta, sai taji ina ma ta kwasa a guje ta bar cikin ɗakin ta fita waje ko zafa sami sauƙi acan, sai dai ko yatsanta guda ta kasa motsawa, ji take yi tamkar an saka ƙaton dutse an danneta. muryarta tun tana fita da ƙarfi har ta zo ta daina fita, lokacin Turaki ya shigo ɗakin kamar an hankaɗosa, dama tun san da zai tafi masallaci yaji hankalinsa bai kwanta ba, yaji gaba ɗaya ba ya so ya tafi masallacin gwara yay sallarsa anan, amma sai ta hana shi, ta tilasta masa akan sai ya tafi masallaci ya sami jam'i. cikin tsananin tashin hankali ya ƙaraso in da take, cikin bala'in ruɗu na farat ɗaya yace,"kin gani ko, sai dai na faɗa miki ba zan fita ba". "ka kaini a cire min su Jannaty, ba zan iya ƙara kwana a haka ba, don Allah ka taimaka min, zan mutu...".. Sauran harufan suka katse sakamakon wani sabon ciwon da ya murɗa mata, taji kamar an saka kibiya an soketa a tsakiyar cikinta da mararta. "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Fulani Nah daure mu fita". ta kalle shi cikin hasken da zata ce a matsayin mutum uku take ganinsa, ta tattaro dukkan sauran ƙarfinta da ya rage mata ta daure, ya kamata ta yunƙura ta miƙe tana dafa kafaɗarsa, zafin ciwon da ya ƙaru yasa duhu ya wanzu a cikin idonta, ta daina ganin komai, tabbas bata iya ganin komai harta mijinta da yake riƙe da ita, sai dai kunnenta na iya jiyo mata sautin muryarsa dake fita cikin tsananin tashin hankali. Allah ya taimaka musu a bedroom ɗin ƙasa ne, da basu san ta yanda za'ai su sauko daga saman ba. Turaki yaji tayi masa wata muguwar damƙar da zai rantse ba ita ba ce, domin ba ƙarfinta ba ne, bata da wannan ƙarfin ya sani. "ka ɗauko riyon Babies mu wuce asibiti". "ba zan iya tafiya na barki ba a haka". "zan iya Jannaty, zan iya daurewa, zan daure har ka dawo". nan da nan Turaki ya haye sama ya tattaro duk wasu abubuwa da za'a buƙata a asibiti, ya kira Ilham a waya ta taho part ɗin, tana shigowa parlon ta tarar da Fillo durƙushe a ƙasa tana ambaton Ya salamu, Ya Salamu ka kawo min da sauƙi, idan na kasa ubangiji ka bani dauriyar da zan iya. tayi kanta da sauri, Turaki ya sauko ya dire kayan hannunsa. "kira yaran nan su kai mota sai ki zo mu kamata". hankalin Ilham a tashe ta shiga ƙwalawa su Sakina kira, bata ma iya yi musu magana da baki ba sai nuni da tayi musu da hannu. fitowarsu compound Boɗejo ta iso gidan ita ma duk a ruɗe, tana ganin yanda suke tafiya da Fillon a hankali ta ɗaga murya wajen ce musu,"kai ai zuwa zaka yi ka kawo motar nan kusa, sai mun hanzarta kar ta haihu a mota". tsabar ruɗewa Turaki ya manta da tunanin hakan, don haka ya sakarwa Ilham ita ya wuce cikin sassarfa yana haɗawa da gudu. asibiti mafi kusa suka isa, su na zuwa aka karɓe su saboda ganin yacca Fillo ta gama galabaita cikin mintunan da gaba ɗaya ba zasu kai rabin awa ba, ƙari kuma da uban kuɗin da suka ji an sakar musu duk da cewa dama asibitin private ne. wucewar wasu mintuna da ba zasu wuce goma ba Dr ya fito yana shaida musu cewar ba zata iya haihuwa da kanta ba sai dai ayi mata CS. "in har zata haihu lafiya ku yi mata koma menene, ina da buƙatar matata don Allah". furucin ya fito daga bakin Turaki murya a kakkarye. Dr ya ba su takardar da za su yi signing akai, Turaki yay signing ɗin a san da hannunsa da jikinsa duka ke rawa. kafin Dr Yusuf ma ya karɓa yay sigining a ɓangaren signature na mahaifinta. cikin wasu ƙalilan ɗin mintuna aka shiga preparation ɗin yiwa Fillo tiyata. lokacin duk ƴan gidan su Turaki sun iso asibitin, da Ammi mahaifiyar Yusuf, da wasu ƙannen Hayyo mutum biyu da suke anan garin gombe Safna da Alawiyya. duk ɗinsu su na zaune a ƙofar labour room ɗin da aka shiga da ita tun ɗazu, kowa yay jugum jiki duk a sanyaye, babu wanda zaka kalla kaga kwanciyar hankali a tare da shi, mahaifiyarta sai kiran waya take yi ana faɗa mata ko tiyatar ma ba'a shiga ba har yanzu. Turaki kuwa zama da tsayuwarma sun gagare shi sai zarya yake tayi, time to time sai yasa hannu ya sharce zufar da ke saman goshinsa. motsin buɗe ƙofar labour ɗin da aka yi yasa duk suka tattara hankalin su gun, Dr ya fito cikin sauri ya nufi side ɗin operation thiater, a san da nurses biyu ke turo gadon da Fillo ke kwance akai, tana sanye cikin uniform ɗin da ake sawa na CS, nurses ɗin suka tsayar da gadon a san da suka ƙaraso saitin family ɗin nata. Mum ta fara duba tace,"Mum kun zo?". kallo ɗaya zaka yi mata ƙwalla ta cika idanunka, duk suka taso suka iso wajenta, ɗayan hannunta da babu canular shi ta dinƙa miƙa musu su na gaisawa tana amsa tarin adu'oin da suke tayi mata. tana duban Ammi ta ce,"Ammi Ummi bata zo ba?". "bata zo ba Fillo, muna dai tayin waya da ita, tana ta yi miki adu'a, tace kar ki yawaita raki kiyi ta adu'a". "Ammi ina ta daurewa amma na kasa yin nishin da suka ce, kamar dai ko ba zan haihu ɗin ba ne". "za ki haihu kar ki damu, insha'Allahu ƴaƴanki za su fito". "Allah yasa Ammi. don Allah a ki kira min Ummina". ta furta hakan ƙwayar idonta na mannewa akan fuskar Turaki da yake tsaye yana kallonta ya kasa tahowa wajenta. bayan sun gama wayar da Ummi, nurses ɗin su ka cigaba da tura gadon, suka tsayar da shi a gaban Turaki. duk sun kasa ɗauke ido daga na juna, ita da take cikin ciwo ita ce me ƙarfin halin yi masa murmushi, don a wannan lokacin Turaki baya iya jin ko murmushin menene zai iya yi, ko da ace kuwa haihuwar tayi, har sai ya ga ta koma asalin Fulaninsa da ya sani, ba wannan Fulanin da yake gani ba me ƙarfin hali. ta miƙa masa hannunta ya kama ya riƙe, ya zubar da gwiwoyinsa a gaban gadon yana ce mata,"sannu Fulani Nah, sannu ƴar aljannah". sai fuskarta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243