Chapter 125
Chapter 125
madafarta. har tsawon awannin da jinin ya ɗauka yana fita daga jikinsa ya shiga jikinta bai ɗauke idonsa akanta ba. da ƙyar kuma ya yarda ya fito daga situation room ɗin yabi bayan nurse ɗin da tazo tai disconnecting abin shigar jinin daga jikinsa. yabi bayanta zuwa office din Dr Yusuf, ya same shi zaune akan kujerarsa ya riƙe kansa da duka hannu biyu, wanda kallo ɗaya zaka yi masa kasan cewar yana cikin matsananciyar damuwa. Turaki ya ƙaraso ciki jiki a saɓule jiri na ɗibarsa, ya nemi waje ya zauna sannan ya ɗauki maltina ɗin da nurse ta ajiye masa akan table ya fasa ya shanye. ya ɗora idonsa akan Dr Yusuf yana me cike da taraddin jin abinda zai fito daga bakinsa. Dr Yusuf ya furzar da iska daga bakinsa sannan yace,"zamu jira nan da 30mints muga abinda Allah zai yi". "insha'Allahu ma lafiya zata tashi". daga nan kowannensu sai ya ɗauki wayarsa ya shiga kiran lambar da ya nema a contact list, daga ɓangaren Dr Yusuf matarsa Nuratu ta ɗaga kiran tana sallama acikin muryar bacci. ya kalla agogon hannunsa yaga ƙarfe biyu da rabi na dare a lokacin, a sanyaye yace da ita,"Farha har tayi bacci ne?". tace,"ban sa ni ba wallahi, na barta tare da Mommi na shigo ɗaki saboda kaina da ke ciwo, your Excellency ni dai gobe zuwa zanyi na nemo mata maganin kuka gaskiya". yay guntun murmushi yace,"ba wani magani da za'a bata, kowanne jariri ai yana kuka dama". Nuratu na noticing yanayin voice ɗin nasa tace,"ehh amma nata kukan yayi yawa". sannan ta daɗa cewa,"your excellency lafiya kuwa naji muryanka so sad?". yace,"lafiya lau". ba don ta yarda da cewarsa ba tace,"as early morning zaka dawo ko?". yace,"ehhh may be". tace,"Inna Wuro ma fa ta dawo, daga saukarta ta biyo ta nan wai anan zata kwana can gidan aljanu sun shiga, sai surutai ta-ke wai Aliyu ya kaɗe aljanu sun tafi da shi zasu ɗauki fansa, fatan ta Allah yasa kar su kashe shi tunda ya kashe ƴar sarkin aljanu, da gaske ne yay accident ɗin?". yace,"Allah ya gyara Inna Wuro, yanzu kina jina?, zan aiko driver ya ɗauke ku, sai ku shirya ku taho tare da Mommi". tace,"ni dama from your voice na gane babu lafiya, meke faruwa Dr?, kar dai da gaske Inna Wuro ta ke yi". jin duk tabi ta rikice yace,"relax, yarinyar bata mutu ba ai. akan maganar da nayi miki kwanaki ne". tace,"wai Dr nah kana ganin hakanne kuwa?". yace,"i pray so hakan ta faru, na gwada jinin yarinyar ɗaya yake da na Mommi, Swty sai dai kinzo xaki ga abinda nake faɗa miki, dan Allah kuyi da sauri ina so ku ƙaraso before yarinyar ta farka. kuma karku taho da Inna Wuro tazo ta ishi patients da zance, ki bar mata Farha itama kar taita kuka". daga haka ya katse wayar yana kallon Turaki dake yiwa Maama bayani. "ban san ya akai ba Maama, asibiti sun kira ni kawai, yanzu haka har an sanya mata jini likitan kuma yace zata farka nan da 30minutes". daga ɓangaren Hajiya Madina tayi magana sannan ya ƙara cewa,"ehh naga Dsp nata kirana amma ban ɗaga ba". tace,"tom gamu nan Me Babban suna, plss take care". yace,"Maama kizo da sauri dan Allah". ya kashe wayar ya saka a aljihu tare da miƙewa ya fita daga office ɗin ba tare da yace da Dr Yusuf komai ba. Fitar tasa babu jimawa Dr Yusuf ma ya biyo bayansa. inda ya same shi tsaye a bakin ƙofar room ɗin da Fillo ke ciki yana leƙenta ta cikin wani glass. daidai da ƙarasowar Daddy da Ammi wajen, Yusuf ya isa wajensu yana kallon Aliyu da ce masa,"Malami ka kwantar da hankalinka, kayi adu'a kawai Allah yasa ta farka". Aliyu ya sauke numfashi yana komawa da baya ya zauna kan kujera. Yusuf yace da su Daddy,"na fito ai tun ɗazu ban ganku ba". Ammi tace,"gida muka koma, da dukkan alama mutanen acikin tashin hankali suke, dan sai bayan zuwanmu da muka shigo cikin haske naga alamar hakan a tare da mahaifiyar yarinyar, ashe ko ɗankwali ma babu a jikinta, haka ma sarƙa ce ɗaure da hannunta. shine naga babu dacewar mu tsaya da ita a haka tunda mutane kowa na wucewa, dalilin da yasa muka koma gida kenan". Yusuf yace,"Ammi wannan matar fa ba mahaifiyar yarinyar bace, ni har na fara ɗaukar maganar Inna Wuro fa, saboda ita wannan yarinyar ta taɓa kwanciya a asibitin nan, tana da matsalar aljanu da suke yawan ɗaukarta su kaita wani wajen, shi yasa nafi tunanin nima ko aljanar tata ce ta fito a siffar mutane". Daddy yace,"a'a wannan matar mutum ce, kun riga kun san baiwar da Allah yay min, da naga aljani na san shine. ta bakin nata dai tace wasu mutanene suka sace su shine suka samu suka gudu". Yusuf ya sauke nunfashi yace,"ofcourse an kidnapping yarinyar in ban manta ba 1month kenan". Ammi ta nemi wuri kusa da Aliyu ta zauna, bayan ta dube shi da tausayawa ta kalli Yusuf tace,"ya jikin yarinyar?". yace"da sauƙi, nan da mintuna kaɗan ma zata farka". Daddy yace,"mun biya ta station sun kwance sarƙar hannun matar, da ƙyar suka yarda da mu akan hakan dan tunanin su ma wai ko me laifi ce ta gudu, to amma duk da haka sun haɗo mu da police ɗaya sannan sun shigar da report wai should incase. yanzu please kasa nurse ko kuma kai da kanka kayi ƙoƙarin mata treating hannunta, tsintsiyar hannun duk ya farfashe yay caɓa-caɓa da jini wallahi, abin tausayi". ya juya yana kallon Ammi yace,"tana ina?". tace,"gata can wajen corrido ɗin can tana sallah, naga hankalinta duk yaƙi kwanciya, ni tausayi ma ta-ke ban wallahi". Dr Yusuf ya kira wata nurse, yayi mata nuni da inda Mum ke zauna yace ta ɗau kayan aiki taje wajenta. ba ɓata lokaci Nurse ɗin kuwa tai treatment duk inda wani ciwo yake ajikin Mum, dauriya irin ta babba shi kaɗai ya hanata yin kuka, dan sosai take jin zafi da raɗaɗi, har aka gama ƙwayar idonta na kallon gefe ɗaya, sai bayan an gama tukunna ta ɗago tana kallon duka hannayen da aka ɗaure wajen bandage kaɗan ba mai yawa ba. a lokacin Turaki ya bar jikin ƙofar ya shiga kaiwa da komowa a wajen hannayensa sarƙe a bayansa, idonsa ya kai bayan Mum da har yanzu ke zaune bata tashi daga wurin da tayi sallah ba, adu'a kawai take akan Allah ya tashi kafaɗun Fillo, har ga Allah tana so ta nemi ahalinta a wannan lokacin to amma ba zata iya ba har sai Fillo ta farka, yarinyar ta taimaka mata a lokacin da take neman taimako. duk da bayanta yake kallo haka yayi tsaye sai kallonta yake ya kasa ko da motsi, ya kuma kasa ɗauke idonsa akanta, yana jin wani irin abu na shigarsa, yana jin kamar yana so yaga ko wace, gaba ɗaya bai san dai taƙamemen abinda yake ji a tare da shi ba. yay ajiyar zuciya ya juya ya koma bakin ƙofar, yaci gaba da kallon Fillo yana ta adu'a cikin ransa, bini-bini sai ya kalli agogo ya duba time, cikar lokacin da likita ya ɗiba kawai yake jira, da dukkan fatansa na in lokaci
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243