Chapter 160
Chapter 160
cewa,"ga shi Dada". ta karɓa ta kara a kunne tare da saka glass ɗinta kamar ganinsa zata yi, bayan sun gaisa tace da shi,"kana jina?". daga ɓangaren Jagarɗo yace,"ina ji Dada". tace,"to ka saka Kakinka na sojoji ku ɗauki hanyar gombe yanzun nan, ka shiga har cikin gidan Alƙali wa yake oho, ka kamo ɗansa da yake auren Fillo kasa masa ankwa sannan ka basa biro da takarda kace ya sakar min jikata, in yaƙi kayi gidan gyara hali da shi da figaggiyar Kakarsa da ta yo min aiken rashin mutunci". Jagarɗo yace,"amma Dada inaga wannan fa sakin nan ba masalaha bane, kar a maida yarinyar nan bazawara tun tana ƙaramarta". ta fusata tace,"a mayar ai bata zama sauran wani ba, ya saketa yau ɗin nan in ba haka ba ai tashin hankalin da ba'a taɓa yi ba". tana faɗin haka ta kashe wayarta, ta kalli Fillo ta doka mata tsawa tace,"ɗago da kanki ki bani lambar mijin naki". Fillo ta ɗago kanta, hawaye duk ya wanke mata fuska, cikin muryar kuka tace,"ban san lambarsa ba". Dada taja tsaki tace da Raudha,"kira min AbdulHamid a waya". ko sallamar Hamid ɗin bata amsa ba sanda ya ɗaga wayar, tace da shi,"ka turo min da lambar mijin Fillo yanzu yanzu". sanin wace Dada yasa ko tambayar ba'asi bai yi ba, haka kuma bai jinkirta ba wajen turawar, dan duka 2 numbers ɗin ya tura mata, gudun ma kar ta ƙara kira ta zazzage shi tace ya tura mata ta ƙarya. Fillo ta miƙe tayi bed room ɗinsu tana jin zuciyarta kamar zata fito, har sau biyu kiran wayar Turaki na shiga bai ɗaga ba sai ana uku, lokacin suna tare da Bello a office, ganin lambar saudia ce yasa bai hanzarin picking ba dan bai san ko waye ke kiran ba. yana ɗagawa yayi sallama Dada ta amsa kamar abin arziƙi, daga can ɓangarensa ya kurɓi ruwa sannan yace,"wake magana?". Dada tana kalla Raudha tace,"munafuka mene ma sunan shi?". baki na rawa Raudha tace,"kamar Turaki naji suna faɗa". Dada tai gyaran murya sannan tace,"Turaki ne?". yace,"ehh ni ne". tace,"yauwa to suna Hassana Kakar Fillo ta wurin uba, Fillo uwar gidanka da bata tare ba har yanzu ka shaida?". Turaki ya gyara zamansa yana rissinar da kai kaman a gabanta yake yace,"Allah sarki Dada ina yini". tace,"lafiya". Turaki ya shafo wuyansa yana jin nauyi da rashin dacewar abin da yayi, tun ranar sadakar uku da ya baro Taraba bai ƙara waiwayar garin ba balle ta kan Fillo da ya san ya baro acan, ya sani tana da hakki akansa amma fushin da yayi da ita baya jin zai iya ƙara nemanta sai idan ita ta neme shi, shi ba lusarin namiji bane da zai bari son ƙanƙanuwar yarinya yake walagigi da shi, dalilin da yasa ya banzatar da ita da lamarinta kenan, kuma ya ɗau alwashin indai ba gajiya akai aka kawo masa ita ba shi dai da kansa ba zai nemeta ba, Maama tayi fama da shi har ta haƙura ta zuba masa ido, shi yanzu yaji ma da bala'in Boɗejo na kullum kullum, da fitinar da Ilham ta tsira ba dare babu rana, ta wanni fannin ma sai yaga barin Fillon acan shi yafi akan ya ɗaukota ya kawota nan ɗin, dan bai san abunda Boɗejo da Ilham zasu aikata ba. yace,"Dada dama...". tayi saurin katse shi da cewa,"riƙe dama ɗin ka, zatonka biko na zo?, a'a ko ɗaya wallahi ajinmu da girmanmu ya wuce nan, kiranka nayi dama in sanar maka da cewa Kakarka ta kira waya tayi mana kowanne irin kalar rashin mutunci, tace muddin Fillo bata rabu da kai ba to mu kuka da kanmu da duk abinda zai biyo baya, tace babu batun tarewarta a gidanka in ba haka ba zata cinnawa gida bom, tace ba zai yiwu daga auren ƴar sarki a ɗauko ƴar aiki ace za'a haɗata da ita a matsayin kishiya ba, itama kuma matar taka tace ba zata zauna da kishiya ba Fillo ta nemarwa kanta mafita tun bata yi mata lahani ba, to shiyasa na kiraka in faɗa maka cewa ka sakar min jika saki uku rasss domin tafi ƙarfinka ta kuma fi ƙarfin zaman gidanka ba wai dan muna tsoro ko kuma muna gudun abunda zai je ya dawo ba, a'a wallahi fin ƙarfinka tayi in ma faɗa maka gaskiya, akan me zata zauna a gidan daƙiƙi da daƙiƙiya alhalin ita da iliminta, to dan haka idan da kana tunanin cewa bata da gata shiyasa ka maki giya kaje aka maku kalar wannan watsatstsen auren to yanzu ka sani da gatanta, mutuwar ubanta ta bankaɗo mata daraja da ƙima da mutuncin da take da shi, ita ba salwantacciya bace da za'a kaita gidan da wata figaggiyar tsohuwa can zata ke kallonta banza a wofi, gwarama in saboda matarka ce nace Fillo ta daka shegiya daidai gwargwadon ikonta dan babu matsoraci a zuri'armu. in taƙaita dai, Turaki kake ko waye yanzu da muke wayar nan ka rubuta takardar saki uku rerass ka yo min aikenta, idan kuma kaƙi sakar min jika aradun Allah zan sa a ɗaure kaff zuri'arku, dan bani da kyau, mutunci ba isata yayi ba". Turaki ya rumtse idonsa sosai, farar ɗaya ciwon kai ya kama shi, ya rasa me zaice da Dada, idonsa ya dinƙa haska masa irin jalalar da Boɗejo ta dinƙa yiwa Maama da Mum akan auren nan da zancen tarewar Fillo da akai, cin mutunci babu kalar wanda bata yi musu ba, har da cewa zata sa Baffa ya sakesu su kama gabansu, tana faɗin wai Ilham ba zata zauna da kishiya ba itama ai ita ɗaya ta zauna, in ace dai wata Turaki ya aura to in goma zai yi babu abinda ya dameta, amma akan Ilham zata iya cinnawa kowa wuta a ƙone, sai taga ta inda wata shegiyar ƴar aiki zata raba miji da Ilham, banda ma dai ana so a bar masu abin kunya ace za'a haɗa ƴar sarki da ƴar aiki, to ba'a isa ba, yanzu dai baida sukuni ta hanasa sakat, bini bini ta kira shi tace ya saki ƴar aikin da yaje ya aura a titi babu waliyi. ya furzar da iska daga bakinsa yana ambaton innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, in da yasan haka auren yake me zai kaishi yin auren duka biyun. Bello nata tambayarsa me ke faruwa bai iya ce masa komai ba, har sai da Dada taji shirun yayi yawa sannan tace da shi,"baka ce komai ba, sai fa ka sakar min jikata, kaima ai ba ƙaunarta kake yi ba munafiki algungumi, kayi zaton gata ne bata da shi kaje ka maki giyarka ka aureta ta yanda zaka wulaƙantata, har da wani cewa tausayinta da taimakonta yasa ka aureta, a gidan uwar wa kake tausayin nata, yaushe rabon da ka waiwayeta?, ai dama duk me hankalin da yaji kalar wannan auren ya san na cin mutunci ne, to aradun Allah ko ka sakar min jikata ko babbar kotun duniya ta rabani da kai". a hankali Turaki yace,"kiyi haƙuri dan Allah Dada...". ta ɗaga murya wajen saurin katse shi da cewa,"kai bafa sulhu na kiraka muyi ba, in sulhun zan nema in kira waccan jarababbar Kakar taka mana, to ka daina bani haƙuri dan babu shi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243