Chapter 8
Chapter 8
Ji ta ke kamar ta tashi ta fizge wayar ta rotsa ta a ƙasa, sai taga ta tsiyan shigo mata waje babu sallama. Ta lura ma gaba ɗaya yaran gidan sun maida ita ƴar iska, kowa ya tashi shigo mata waje sai ta kaɗo masa yake shigowa da sallama, sun fi gane su shigo kullum su na ɓaɓatu a waya kamar dan su bature ya ƙera wayar. Yusuf da ya gama wayar sai da yay typing message a wayarsa kana ya sakata a aljihu, sannan ya kai idonsa kan Kakarsu yace,"Ina Kwana". Ba tare da ta dube shi ba a fusa ce tace,"yana kwano". Yay ɗan murmushi ya ƙara cewa,"kin tashi lafiya?". "da baka ganni anan ba ai". Yace,"to Allah ya ƙara lafiya". Bata dai amsa mishi ba taci gaba da kallonta, kallon da gaba ɗaya ba fahimtarsa ta ke ba. Bakinsu kawai taƙe kallo tana yin dariya a inda ya kamata, ta kuma ja uban tsaki a inda akai mata ba daidai ba. Ta gefen ido ta ke ta kallon Yusuf, wanda ya sauko ƙasa ya takwashe ƙafafunsa, ba tace da shi ƙala ba sai da ya janyo flask gabansa sannan cikin hanzari ta dakatar shi. "me haka?, kwanon abincinka ko nawa da zaka wani janyo shi gabanka?, ko kuma Uwarka ta dafa ta kawo min ne da zaka nuna min iko da shi?, salon dai neman magana irin ta bawa...ina ce da ka shigo ko sallama baka min ba balle na sami arziƙin gaisuwa, saboda ka maida ni abar banza shine sai da ka gama waya da wanda ya fini tukunna zaka durfafi abincina...to baka isa ba, kuma ba'ai wannan halittar da zata taɓa min kwano ba, ka tashi ka koma ka zauna ko kuma ka bar min parlo tun bamu samu saɓani da kai ba. Ni bana son tashin hankali haka kawai". Yusuf ya miƙe ya koma kan kujerar ya zauna ba tare da yace mata komai ba, ta kalle shi kaɗan ta kwaɓe fuska kamin tace,"yafi maka dai". "amma dai ina ce bayan na gama wayar na gaishe ki". Yace da ita yana kallonta. "bata yi min bane". "wa?". "ita gaisuwar taka". "ohh to Allah huci zuciyarki". Ta amsa da amin. Yaci gaba da danna wayarsa, tsawon mintina kusan uku yaji maganar Inna Wuro na cewa. "aiko ka akayi ne?". Bai zaton da shi ta ke ba, dan farko ɗagowa yay yana dube duben ta inda zai ga mutum, sai da yaga ba kowa sannan yace. "ba wanda ya aiko ni". "to kuma zaman ma mene?, zuwa da sassafe haka, babu fa jimawa aka gama min gyaran wurin nan. bana son a ɓata min waje dan ni ba fiya son ƙazanta nagi ba...da ba za'a bar mutum ya huta ba dole sai anzo ɗaukar magana". Rufe bakinta kenan Aliyu ya shigo parlon, ta bishi da ido har sanda ya nemi three seater ya kwanta yana ɗora ƙafafunsa akan hannun kujeran. Haushi ya tuƙeta tace,"idan ka tashi Amadu ya gyaran wajen". Shi dai bai kulata ba ya ɗauko earpice a aljihu ya saka a kunne, Yusuf na kallonsa yana mamakinsa, shi dai a wannan zamanin bai ga namiji mara lissafi ba irin Aliyu, yana namiji tunda akai hutun ASUU shikenan ya zama kamar mace, kullum yana gida sai shegen aikin jin waƙoƙin banza, yaƙi sana'ar fari balle ta baƙi, idan anyi magana yace ai Babansa ya tara musu...kuma in ana faɗa masa gaskiya Ammi tace ba haka ba. Ya jijjiga kansa kawai yana jan ƙaramin tsaki na takaici. Aliyu yace da Inna Wuro,"naga mutanen ƙauye sun zo". Tace,"to su tsaya a iya ɓangaren ku bana son gayya". Yay gajeriyar dariya sannan yace,"ya za'ai su zauna a ɓangarenmu?". Tace,"nima ya za'ai su sauka a ɓangarena?, Ni dai magana ta Allah idan kaje ka faɗawa Uwarka kar a soma turo min kowa, dan wancan karan banji daɗin zuwansu ba. Banda Amadu ya gina masai babba da ban san yanda zanyi ba, abunda ban taɓa gani ba sai a lokacin kashi har bakin masaina. Ɗoyi kuwa iri-iri babu kalar da ban guntsa ba, inda ace Uwarku ce kaɗai a gidan nan ai da warin kashin yaran ƙauyen nan shi zai zama ajalina. To sai Allah yasa akwai Falmata, tazo da kanta wallahi ta wanke min banɗaki nan ta sanya masa turaren wuta". Aliyu yace,"itama Ammin ai zata yi miki, dan dai bata sa ni ba ne, kuma ai da sai ki faɗa mata". Ta kama baki tace,"to ina ma ta ke zuwa waje na balle na sanar mata. ni fa idan kaga mun haɗu da ita Amadu ne zai yi tafiya mu haɗu a wajen masa rakiya kamar kishiyoyi, amma ni ina nake da wani arziƙi a wajen Zainabu...kana dai kallo ko gaisuwar safe". Bai sake cewa da ita komai ba, don sam ba ya son abin da take yiwa mahaifiyarsu. Ta miƙe ta ɗauki flask ɗin abincin da aka kawo mata tun ɗazu bata ci ba ta wuce da shi kitchen, dan idan ta barshi Aliyu ma saka masa hannu zai yi, shi kuma ba jin magana yake ba. Fridge ta buɗe ta saka yanda ma ko da wani ya shigo kitchen ɗin ba zai gani ba, har ta nufi ƙofa zata fita sai ta tuna ta dawo ta sakawa fridge ɗin key dan lemon da yake ciki sauran guda uku, Amadu bai san ya ƙare ba kuma cikin Ƴaƴansa babu mai ɗaukowa a ɓangarensu ya kawo mata, basu iya kawo mata komai ba amma sun iya suzo su cinye mata duk abinda aka ajiye mata. Bata dawo parlo ba sai da tayi sallar walha, tana zuwa ta tarar da Yusrah ta shigo, ta bita da kallon sama da ƙasa ta ƙarasa bakin ƙofar ta jawo ta rufe tana faɗin,"kamin na huɗu ya shigo, ba dan ba dan ba sai nace Amadu gidan taron jama'a ya buɗe min". Ta murza key tana mitar,"kai da ɓangarenka amma ba za'a barka ka huta ba". Sannan ta saƙala key jikin abin maƙale labule tana cewa da su. "idan zaku fita ga key ɗin anan, idan zaku fita nace ba wai idan kunji knocking ba". Cikinsu babu wanda ya tankawa maganar da ta ke, dan haushi kamar ta rufe su da duka. ta kallesu su duka tace,"Amadu kuka share bani ba". Sannan ta juya ta koma ɗakinta. Yusrah ta zauna kan kujerar da Inna Wuro ta tashi, ta buɗe jakarta ta ɗauko office pins tare da madubi, ta shiga ɗaura ɗankwali. Tana ɗaurin ta ke cewa Yusuf. "Yaya ashe ka shigo. Ɗazu Ammi ke cewa ƙila har ka koma ba lallai ta ganka ba...idan ka gama abinda kake naji dai tana batun zuwa abuja yau". Ya ɗago da ido ya kalleta yace,"me zai kaita Abuja?". Time da ta ke gama ɗaura ɗankwalin tace masa,"biki mana...daughter ɗin ƙawar nan tata da aka haɗaku kaƙi, ita ce zata auri ɗan gwamnan jigawa". Ya maida idonsa kan wayarsa yace,"When will she come back?". Tace,"I don't know. but i heard her saying sati guda za'ai ana bikin". Karo na biyu ya ɗago ya sake kallonta. "kuma Daddy ya barta?". "kai dai Yaya babu ruwanka. Ka barta taje tai hidimanta ta dawo". Still yana kallonta yace,"ki shirya ku tafi tare". Tayi saurin kallonsa da cewa,"niii babu inda zanje.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243