Chapter 1
Chapter 1
[8/5, 18:59] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _Na fara da sunan Allah mai Rahama mai jin ƙai. Tsira da aminci su ƙara tabbata ga Fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW._ *1* *APRIL 20th 2021.* *American Hospital Dubai, 2:30pm.* _"hey don't move, we are us navy seals...God! Damn it...we have a tango in the north wing every week. stop! stop! stop!...great team work guys, yeah we will mark you for the assist on this one."_ sautin da ke fitowa kenan daga cikin ƙatuwar plasma ɗin da ke manne a bangon ofishin, cikin wani american film me suna Steel Brigade. dai-dai lokacin da sojojin suka kama mutumin da ke sanye da mask, dai-dai lokacin Yusuf da ke juyi akan kujerarsa yasa tafukan hannunsa duka biyu ya shafo fuskarsa tare da fitar da iska daga bakinsa. "ohh dammm it". "ai na faɗa maka sai sun kama shi". Kalid wanda har yanzu bai ɗauke idonsa daga kallon tv ɗin ba ya faɗa a sa'ilin da duka haƙoran gabansa ke bayyana a waje alamar yayi farin ciki da abinda ya faru. Yusuf ya ƙara juyawa akan kujerarsa zuwa gefe guda sannan yay guntun tsaki yace,"ko waye producer ɗin nan sam bai iya tsara film ba". "hhh to ai hakan shine dai-dai, kai kana kallon sojojin nan kasan bana banza ba ne...kuma gwara a kama shi tun a farko, wasan zai fi tafiya dai-dai". "kuma wataƙila ya suɓuce masu ba". "ta ya ya?, macece fa ai da kamar wuya ta iya ƙwacewa". "wannan ai ba mace ba ce". "bari su buɗe fuskar zaka gani, ai yanayin gudun kaɗai zaka fahimci macece, itama ba me kamar maza ba". shirun Kalid ɗin ya haɗe da sanda sautin maganar film ɗin ta ci gaba da tafiya, nan sukai shiru suna ci gaba da kallon. _"get the mask!!...there is no harmful in the air we already checked, expect for the thorpe's breath."_ ɗaya cikin sojojin yay maganar a tsawace inda a take ya fizge mask ɗin daga fuskar mutumin, kuma lokaci ɗaya zaton Khalid ya bayyana, hakan kuma ya wanzar da dariya a fuskarsa, nan ya juyo ya kalli Yusuf dake aikin jan gajeran tsaki babu ƙaƙƙautawa alamun ba hakan yaso ba. lokacin da Yusuf ya buɗi baki zai yi magana lokacin ƙofar ofishin tayi ƙara, aka turota a hankali inda wata matashiyar budurwa ta bayyana hannunta riƙe da wasu takardu, jikinta kuma sanye da unifom na ma'aikatan jinya. ta mayar da ƙofar ta rufe sannan ta ƙaraso cikin ofishin tana ƙarasawa gaban tebirin da Yusuf ke zaune kan kujera yana juyawa gefe zuwa gefe a hankali. cike da girmamawa ta rissinar da kanta tare da aje fayel ɗin hannunta akan teburin tana tura su zuwa gaban Yusuf. "Ranka ya daɗe ga result ɗin da aka samu". ta faɗa sanda ta ke harɗe hannayenta zuwa baya. "ta farka ne?". Yusuf ɗin ya tambaya a sa'ilin da ya buɗe fayel ɗin yana dubawa. "ehh ranka ya daɗe ta farka wajen ƙarfe ɗaya da minti goma sha biyu, amma bata fi sakan huɗu ba ta koma, da alamu dai har yanzu da saura kamin ta dawo hayyacinta". shiru ya biyo bayan maganarta, idon Yusuf ta cikin farin gilishin da ya manna na bin rubutun da ke cikin fayel ɗin, karantarsu yake da fahimta, wucewar daƙiƙa 1,2 Yusuf ya ɗago kansa akan fayel ɗin, ya kai hannu ya shafo goshinsa sannan ya jinginar da kansa jikin kujera yana mai sauke gajeran numfashi. _"huuuuhh"._ hucin iska ta fita daga bakinsa. *"EXOGENOUS DEPRESSION".* ya faɗa cikin amon sauti na tausayawa haɗe da kulle murfin idonsa. furucin nasa kuma yasa Kalid maido da kallonsa gare shi. "tana cikin matakin biopolar kenan?". Yusuf ya jijjiga kansa tabbacin hakan ba tare da ya ce komai ba, na tsawon wasu sakanni ya ɗaga ido ya kalli Nurse ɗin yace,"kuma iyaka binciken da jami'an tsaro suka yi babu wani danginta a ƙasar nan?". "ƙwarai ranka ya daɗe sun bada tabbacin hakan...ni kaina lamarinta na ɗaure min kai". Kalid yace,"gaskiya da sake a wannan lamarin, su ƙara bincike domin idan ba zaman ƙasar nan take ba to wa ya kawota ya ajiyeta kuma ya tafi ya barta cikin wannan mawuyacin yanayin?". Yusuf ya ƙara fitar da iska daga bakinsa kamin yace da nurse din,"Ƙarƙashin kulawar wa ta ke?". "Ranka ya daɗe tana ƙarƙashin kulawar Dr Nameer, sai dai gaskiya tana fuskantar matsala". "wanne irin matsala?". "Dr Nameer yana da zafi, so kuma shi yace muddin babu wani nata ba zai bata wani kulawan da ya dace ba...infact yanzu ma yaƙi rubuta alluran da suka kamata ayi mata saboda wai ko ya rubuta bata da me saya mata". karo na babu adadi Yusuf ya ƙara girgiza kansa tausayi fal ransa, sannan ya ɗauki ƙaramar takarda yay signing a jiki ya miƙa mata tare da fayel ɗin. "kije Pharmacy Sumayya, ayi dukkan abinda ya dace akan matar nan, zan saka maki kuɗi a account, dan Allah ki kula da ita ni kuma nayi miki alƙawarin biyanki da kauri". ta rissina ta ɗauki fayel ɗin tana yi mishi godiya sannan tayi musu sallama ta fice daga ofishin. bayan fitarta da wucewar minti uku Yusuf ya miƙe yana kafa hular zanna bukar a gashin kansa, fuskarsa na bayyana ainihin damuwar da ke cikin ransa. "tashi mu tafi Kalid". "a'a ba kana da sauran aiki ba?". "ba zan iya komai ba Kalid, kaina ciwo yake. zan yiwa Dr Yusrah magana". Kalid ya miƙe tsaye shima, suka nufi ƙofa yana cewa da Yusuf. "Dr ka rage saka damuwar wani a ranka...". kuma bai ƙarasa maganar ba Yusuf ya tari nunfashinsa da cewa. "Kalid idan har matar nan tana da miji a raye to ya cika azzalumi, idan ma yana raye ne ko ya mutu to tabbas ƴaƴanta salwantattu ne, basa neman albarka kwata-kwata, basu san darajar uwa ba, domin ko kaffara ba zanyi maka ba ta dalilinsu ta shiga wannan bala'in rayuwar, kuma duk san da nayi tozali da wani ɗa nata sai nayi shari'a da shi". maganar yake cikin zafin rai kamar zai kaiwa bango duka. "tabbas ba zai wuce takaicin miji ko na ƴaƴanta ne ya zama silar wannan ciwon nata ba...amma ni abun mamakin ace tana cikin wannan mawuyacin halin kuma babu kowa nata a tare da ita". Kalid yay maganar a sanda suke sauka daga kan steps su na ƙarasowa cikin reception kamin su sa kai su fita gaba ɗaya daga asibitin. kuma har suka isa bakin mota cikinsu babu wanda ya sake magana. on their way to hotel wayar Yusuf tayi ƙara, ya kai hannu ya cirota daga aljuhunsa, ya ɗaga vedio call ɗin da ya shigo yana mai raba hankalinsa gida biyu, ɗaya ga tuƙin da yake, ɗaya kuma ga fuskar matarsa da ta bayyana a cikin wayar. "You Excellency what am i seeing on your face?, whats wrong?, are you oak?, wani abu ya faru ne?, what is the problem?". tarin tambayoyin da suka fito daga bakin Nuratu kenan zuwa ga mijinta, cikin kiɗima da bayyanuwar tashin hankali na farat ɗaya, dalilin damuwar da ta gani a tare da shi ta haddasa ma ta ruɗewa na neman fitar hayyaci. kallo ɗaya na yanayin da take ciki zaka yi kasan macece mai tsananin so da ƙaunar mijinta, gami da tausayinsa,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243