Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 14

Chapter 14

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,239 words 0 views Progress saved
Download Book

ta jinginar da kanta ajikin bango, her breathing slows down, abu kamar almara sai taji ciwon kan da ya addabeta tsawon sati biyu ya fara tafiya, har ma tana neman ta rasa shi gaba ɗaya. Hatta wannan nauyin da jikinta yay shima ya fara saki, to 10minutes sai taji komai yayi sauƙi kamar ba ita ba. Maijidda tayi sallama cikin ɗakin daidai da buɗe idon Fillo, ta ajiye ƙwaryar furar tana zama kusa da Fillon. "sannu". Tace da ita kamin ta juya gun Amir tace mishi,"sannu da zaman jinya Amir". Yay murmushi kaɗan sannan yace,"yauwa Kuluwa". Ya faɗa da zola dan bata son sunan, tace,"ni dai daga yau idan ka ƙara kirana da wannan sunan sai na rushe gwamnatin da ka kafa a zuciyar ƙawata". "yaushe kika yi wannan isar?". Yay tambayar yana kallon inda Fillo ta ke, wadda ta samu relief a yanzu, dan har idanuwanta sun yi tangarau, tana kallonsu ne kawai bata cewa komai. Maijidda tace,"ka dai bi a hankali kawai, ita masoyiyar taka ai tasan girman isar da nake da ita". "ah lallai ne mai girma Kuluwa". Suka yi gajeriyar dariya su duka. Amir yace da Fillo,"ya kike ji yanzu?". Idonta akan ledar magungunan da ke can bayansa tace,"idan ka tashi tafiya ka tafi da waccan ledar ka jefar a bola". ya waro ido waje yace,"haka likitan ya karanta mana dama?". ta ɓata rai tace,"koma me ya karanta ni dai a zubar da su kawai, ai naji sauƙin". Maijidda tace,"ai sai ki bari idan Kaka tazo kyayi mata wannan bayanin". Sai kawai Fillo tayi narai-narai da idanuwa, fuskar nan a marairaice tana duban Amir kaɗan tace,"dan Allah Amir...wallah idan Kaka tazo ba zata bari a zubar ba, ni kuma naji sauƙi". Tana yin shiru ya ɗauki ledar ya saka a aljihunsa yana faɗin,"yanda kika ce ranki ya daɗe". Wayarsa tayi ƙara ya ɗauka, ƙaramar waya ce ba wata babba ba, yayi shiru yana sauraron maganar cikin wayar kamin yace,"tom shikenan Bandirawo ina kan hanya insha'Allah". ya ƙara yin shiru for seconds kan yace,"ahh mai jiki da sauƙi, yanzu haka ma ina wurinta". "tom zata ji insha'Allah, mun gode". Ya katse wayar ba tare daya dubi Fillo ba yace,"Bandirawo ne, yana yi miki sannu da jiki". Tace,"ina amsawa". Sannan ya miƙe yana roƙonta akan ta daure taci abinci, gyaɗa kawai tayi, ta yunƙura itama zata miƙe dan yi masa rakiya yace a'a ta koma ta zauna. Zuciyarta na harbawa da soyayyarsa ta sunkuyar da kanta ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, cikin sanyayyan muryarta da ciwo yaywa lahani tace,"na gode". Ƙwayar idonsa akanta da tsananin shauƙinta yace,"da me?". Still idonta kan yatsunta tace,"ni dai kawai na gode, Allah ya bada lada". Ya sauke numfashi yace,"amin". Sannan ya nufi ƙofa, ita kuma tana ce masa ya gaida su Inna. Bayan fitarsa Maijidda tace,"ke kam Fillo kin more da mijin aure, Amir mutumin kirki ne, ki ga fa tun da kika kwanta yake sunturi akanki". Fillo dai bata ce mata komai ba, don ita tunaninta ma na wani waje can na daban. Dogon tsakin da Fillo taja na takaici shi yasa Maijidda saurin kallonta da mamaki. "shi kuma tsakin fa?". Fillo tayi shiru tana jin wani ɗaci a cikin ranta, tunda tazo gidan nan bata taɓa shiga ɓangaren masu gida ba, kai hasali ba matar gidan ma bata taɓa ganinta ba balle ƴaƴanta, idan aka cire wadda tazo ranar nan ta kawo musu kwancen kaya, abunda kawai ta san bakin kowa na faɗa shine Uwar ɗakinmu Hajiya Madina. Amma haka kawai ta ke jin bata son mutanen gidan, dan ta ra'ayinta da tuni sun bar aiki sun koma wani wajen to dan Kaka taƙi ne. To dan me yasa ma ba zata ji zaman gidan ya fice akanta ba yanzu?, sanadin fa taimakon ɗansu ta shiga halin da ta shiga. sannan again tana kwance cikin wannan halin sun zo sun ɗauke mata Kaka sun mayar da ita aiki ɓangarensu, aikin da idan ta fita tun safe sai dare zata shigo, ta lura sam bata samun hutu da can ɗin. Akan me ma zuciyarta zata so matar gidan?, tuwo ne a idonta da ta kasa ganin girman tsufan Kaka da har suke loda mata uban aikin da zai gajiyar da ita. Ko da yake in aka ce baka da shi dama shikenan taka ƙararriya ce, talaka dai na ganin rayuwa. "salamu alaikum". Maijidda ce ta amsa sallamar da aka yi daga ƙofar ɗakin, Fillo kuwa a ciki ta amsa, sai bin ƙofar ɗakin da tayi da ido. Wata tsohuwar mata ta leƙo kai cikin ɗakin tana kiran sunan Kaka. Maijidda tace,"ki shigo bata nan". Ta shigo ɗakin tana faɗin,"bata nan?, ina lafiya dai ko?, kwana biyu banga gimlawarta ba acikin ɓangaren nan". "lafiya lau, ta koma cikin gida da aiki ne shiyasa". Maijidda ta bata amsa. Ta ƙara cewa,"Allah sarki shi yasa ashe, ni fa naga kwana biyu bana ganinta a wurin aiki. Kuma da yake ta saba leƙowa a gaisa ko da ba ranar aikinsu ba shi yasa ma nace bari na leƙo naga ko ba lafiya ba". Maijidda ta ƙara cewa,"lafiya lau, idan ta tafi ne bata shigowa sai dare". Matar tace,"to kwa sanar mata na nazo idan ta dawo, kuma kuce ina yi mata barka an samu ci gaba". "to insha'Allahu za'a faɗa mata". Yanzu ma dai Maijidda ce ta amsa, dan Fillo ma babu alamar zata yi magana. Matar har zata fita sai ta dawo tana cewa,"kinga na manta fa ashe Fillo babu lafiya, kusan ni ɗaya ce ban shigo dubata da jiki ba". Ta kalla Fillo da ke kumbure ta haɗe gira duka biyu tace,"ya sauƙin jikin naki Fillo?". Ba don taso amsawa ba tace,"naji sauƙi". tace,"to Allah ya ƙara lafiya...sai anjimaku". Da haka ta fice tana fita Fillo taja uban tsaki tace,"har ga Allah haushin komawar Kaka aiki cikin gida nake, gaba ɗaya an riƙeta da aiki ba'a barinta ta huta. su ko tausayinta ma basa ji, ko ba su da tsohuwa ne oho?, tun fa da ta fara aikin nan idan ta fita da safe bana ƙara ganinta sai wata safen, dan kamin ta shigo nayi bacci, jiya har kusan goma da rabi bata shigo ba...jiya da ta dawo ina ganinta tana miƙa tsabar gajiya, kawai don bana cikin hayyacina ne amma da sai naje gidan nace su sallamemu". Ta gama ƙorafinta cikin masifa, Maijidda dai bata ce ma ta komai ba, sai ma ƙwaryar furar da ta janyo tana sha. ruwan hawaye ya kawo idon Fillo, muryar in breaking tace,"ni ban san ba ko basu ga yanda Kaka ta tsufa ba ne...amma me suka ɗauki kansu?". Maijidda tace,"masu kuɗi mana. kuma dai ba za ki ce su na sahun masu kuɗi marasa kirki ba. za ki so kanki ta wannan ɓangaren in kika faɗi haka...ke dai ki yiwa Kaka adu'a kawai, banda ke sanin kanki ne ba zata juri wannan bautar ba tunda ta tsufa da yawa". Bata ce komai ba, Maijidda ta ƙara cewa,"ga furar kisha da sanyi". "aina kika samu ƙanƙara?". "Yami ta aike ni ɗazu na ganta shi ne na sayo, nasan za ki so". Fillo tayi shiru, idonta na kallon yatsun ƙafarta. "ni dai kici abinci kar naci amanar Amir". "ba zan iya ci ba Maijidda sai Kaka

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243