Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 150

Chapter 150

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,217 words 0 views Progress saved
Download Book

Allllahhhh kikkki yaaafeeee miiiimmmmnn, dddda Allllahhhh kiiii neeemmmooo minnn Haliiimaaaattttuu". sai da aka ɗauki cikakken minti ɗaya da ƴan kai sannan ya iya faɗar kalmar da za'a faɗeta cikin sakanni biyu, yana maganar bakinsa na rawa, haƙoransa na daddatsewa akan harshensa. Hamid yasa handky yana goge masa uban yawun da ya dalala ajikinsa ya ɓata gaban babbar rigarsa kamar an sheƙa masa ruwa. ƙafafunsa suka shiga rawa akan wheelchair ɗin ya kamo hannun Hamid yana faɗa masa,"zaazzzzzannnn saukkkkkaaaa innnneeee miiii yaaaaaffiyyarrrr Dddddaaaada". kaman yanda Kaka ke hawaye haka ma Yami, saboda ƙarya ne ace kaga halin da Hayyo ke ciki baka zubar da hawaye ba. Hamid na kallon Kaka yace,"wai yana so zai sauko ya nemi yafiyarki". tace,"Hayyo ba sai ka sauko ba na yafe maka, ni baka min komai ba dama". ta dubi Hamid tace,"mu shiga". tai gaba suka biyo bayanta, Yami ta tura ƙofar. suna nufar entrance na parlon gidan Ummi ta fito, Kaka ta fara gani wadda ke aikin goge hawaye, bama ta lura da sauran ba, tai saurin ƙarasowa wajenta tana faɗin,"lafiya Dada?, na fito naga ba kya parlon me ya faru?". Kaka bata iya magana ba dan har yanzu a girgiza take, kuma kamin tayi mata nuni da su Hayyo, Ummi taji hannayen mutum a ƙafafunta da ɗigar ruwan hawaye. ta kai idonta kan Hamid dake zube a gabanta ya riƙe ƙafafunta, ba fuskarsa ta kalla ba, saman kansa kawai ta kalla ta shaida ɗanta, sai taji wani abu ya tsarga mata, ta kulle ido tana jin taruwar ruwan hawaye aciki. "Hamid". ta kira sunansa da amon sautin da ya tafi ya taɓa har zuciyar Hayyo. "me kake nema a ƙafafuna Hamid?, laifin me kayi min?, tashi tsaye na ganka ɗana". Hamid ya miƙe yana hawaye, Ummi ta rungumosa jikinta suna kuka tare, wucewar daƙiƙa biyu Hamid ya zare jikinsa daga nata yana bin mahaifiyar tasa da kallo, wadda yaga ta ƙara kyau da girma kamar ba ita ba. "ya akai kazo nan Hamid?, wa ya faɗa maka inda muke?". tambayoyin da tai masa kenan, kuma kamin ya bata amsa idonta ya sauka akan halittar da duk lalacewar da tayi ba zata kasa ganeta ba a kallo ɗaya, tai saurin ɗauke ƙwayar idonta daga kan mutumin da take jin ta tsane shi tsana mafi muni. Hamid ya buɗe baki zai yi magana tayi saurin ɗaga masa hannu cikin fusata, ta kulle idonta tana huci na tsawon daƙiƙa ɗaya, ta buɗe su a sanda ƙwayar idonta ta kaɗa tayi jawur, wannan damuwar da take tare da ita na tsawon shekaru ta taso tun daga can ƙuryar zuciyarta ta mamaye saman fuskarta. da tsananin ɓacin rai a muryarta tace da Hamid,"tunanina duk sanda zan ganka zan zama ina me farin ciki ne". ta faɗa tana ƙara ɗaga muryarta da faɗin,"me yasa kazo min da wannan abin cikin gida?, to idan baka sani ba ka sani, bana so kuma bana ƙaunar sake haɗa ido da azzalumin mahaifinka har in bar duniya, dan haka tun ina shaida kai ɗana ne ka fitar da shi daga gidan nan". tai maganar cikin zafin rai tana yi masa nuni da gate, Hamid ya dubi mahaifinsa da tausayi wanda ke ta kokawa da wheelchair yana so ya sauko, ya koma ya kalla Ummi yace,"dan Allah Ummi...". bata barsa ya ƙarasa ba ta doka masa tsawa. "Hamid ka fita da shi na faɗa maka, ka fita da shi tun ina iya kallonka ina shaida kai ɗana ne, Hamid ina me rantse maka in baka fitar da wannan matsiyacin mutumin daga gidan nan ba zan tsine maka". Kaka tayi saurin shiga maganarta da cewa,"kul, kul Halimatu, shi me yayi miki da zaki nemi ki sauke fushinki akansa". Ummi tace,"wallahi tallahi in har don inci gaba da kallon wannan azzalumin mutumin a inda nake ne to gwara in yafe Hamid muddin bai fitar da shi daga gidan nan ba, na tsani mutumin nan na tsani ganinsa, inata roƙon Allah kar ya ƙara haɗani ko da ace da inuwarsa ne shine Hamid saboda ba ya ƙaunata zai ɗauko shi ya kawo shi inda nake salon zuciyata ta buga". Yami tace,"kiyi haƙuri Ummin Fillo, ki tsaya ki saurare shi har yanzu shi ɗin mijinki ne, kuma kar ki manta shi uban ƴaƴanki ne, Allah ma muna masa laifi ya yafe mana, to kuma ina laifin wanda ya gane kurensa yazo neman yafiyarka". ta girgiza da kanta cike da takaici da ƙunar rai,"Yami baki san waye wannan mutumin ba, wannan da kike ganinsa azzalumi ne, mugu ne, macuci, dan Allah ku fitar da shi daga gidan nan tun ban faɗi na mutu ba". sai kawai ta fashe da kuka me cin rai, tana jin wani abu me ɗaci na taso mata, tana jin kamar ta shiga ciki ta rarumo duk abinda ta gani tazo taita rotsawa Hayyo. faɗowar Hayyo daga kan wheelchair yasa hankalinsu ya kai kansa, Hamid ya tafi da sauri ya ɗaga kujerar da ta danne shi, jikin Hayyo duk karkarwa yake, yana jan jikinsa a ƙasa yana so ya ƙarasa gaban Ummi, Hamid ya fara hawaye ya ɗagosa ya mayar da shi kan kujerar, sannan ya turasa ya kaisa gaban Ummi. gwanin ban tausayi hawaye ke sauka akan fuskar Hayyo ya haɗe hannayensa alamar roƙo, bala'in nadama da danasani shimfiɗe a fuskarsa, cikin ƙinƙina mesa zuciyar mutum ta tsinke yace,"dan darajan Allah ki yafe min Halima, ki tausayawa halin da nake ji, ke kaɗai kika rage ki yafe min acikin waɗanda suke raye, kuma muddin ba ki yafe min ba nasan ba zan gama da duniya lafiya ba, domin nasan na aikata miki abubuwan da Allah ba zai barni ba, dan Allah ki yafen ko na samu sassaucin bala'in da nake ji a tare da ni". Ummi na kallonsa da tsantsar tsana tace,"kai yanzu Hayyo har kana da idon da zaka kalleni ka buɗi baki kace in yafe maka?, yaushe kasan Allah da yau kake roƙon wani da shi?, to bari kaji na faɗa maka, banda idon da zan dubi halin da kake ciki in tausaya maka balle na yafe maka, ka cire batun yafiya tsakanina da kai dan ko da ace yafiyata ta rage maka shiga aljannah Hayyo ba zan yafe maka ba". Kaka, Yami da Hamid su kai ta roƙon Ummi akan ta yafe masa, amma sam taƙi, ƙarshe ma sai ciki ta shiga ta ɗauko mayafi ta fito tana kallon kowa tace,"in har ba zaku ɓadda shi daga inda nake ba to ni zan bar muku gidan". sannan ta kalli Hamid tace,"kai kuma ko a mafarki ka ganni karka nuna ni a matsayin mahaifiyarka, tunda kaima baka tausayina". tana zuwa bakin gate Fillo na turo ƙofa ta shigo, niƙab ɗinta a hannu tana yamutsa fuska alamun ta gaji, farat ɗaya hankalinta ya tashi ganin Umminta na kuka, gabanta ya faɗi tana tunanin me zaisa mahaifiyarta kuka a yanzu kuma?, ai tayi zaton zubar hawayenta ya ƙare kuma tunda har ta rabu da Hayyo. sai ta ƙanƙance ido tana bin kowa da kallo, ta tsayar da idonta bayan Hamid da bata ga fuskarsa ba, zuciyarta bata gama tunanin ko waye ba ya juyo, ta ware ido tana faɗin,"Hammah". ta faɗa murmushi na ƙwacewa a fuskarta, harta ɗaga ƙafa zata wuce wurinsa sai kuma idonta

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243