Chapter 133
Chapter 133
tsaye ta dawo kusa da Ilham ta zauna. ta janyota zuwa jikinta cikin sigar lallashi da ban haƙuri tace da ita,"Ilham wannan kukan naki da kika shafe kusan awa guda kina yinsa ba shine zai bawa Mahaifiyarki lafiya ba, saboda haka ki sha re hawayenki ki mata adu'a dan ita tafi buƙata a halin yanzu". maimakon Ilham ta daina kukan sai sabo ya ƙaru fiye da wanda take yi, kuma Kakar tata Hajiya Shema'u wacce take mahaifiya wurin Azima bata ƙara ce mata komai ba, sai bubbuga bayanta da take cike da matsanancin tausayin Ilham ɗin. a lokacinne kuma Ahlan ya iso wajen, ƙani ne a wurin Azima daga ita sai shi. ya zauna akan kujerar kusa da mahaifiyarsa, shima da ka kalla fuskarsa zaka hangi damuwa acikinta. yace da ita,"Umma me likitan ya ƙara cewa?". ta sauke numfashi ruwa na kawowa cikin idonta tace,"tou Me Martaba dai ya tafi wajensa tun bayan da suka fito da ita daga theater room ɗin, ban san yanzu kuma ya ake ciki ba". Ahlan ya sauke numfashi sannan yace,"nima jiya muna tare da jami'an tsaron da suke ta bincike akan accident ɗin nata, kuma har yanzu fa Umma babu labarin driver'n da suka fita tare. anje wurin iyalinsa su kansu sunce satin biyun nan cif ba su saka shi a idonsu ba nemansa suke, itama kuma jakadiyar tata fa har yau ba labarinta". da damuwa sosai Hajiya Shema'u tace,"to Allah masanin abinda ya faru, kuma ni gani nake idan lamari ne na ƴan garkuwa ai ita zasu ɗauke ba drivern ko Jakadiyar ba, kuma idan kidnappers ɗinne da tuni sun kira waya, amma koma mene dai mun barwa Allah, fatanmu Allah ya tashi kafaɗunta". sai kuma ta fashe da kuka sosai tana cewa,"da banyi niyyar faɗa muku ba saboda kar hankalinku ya tashi, sai dai faɗar ya zama dole ko don a tayata da adu'a. likita yace ta kamu da paralyse, ɓarin damanta ya mutu ya gama aiki Ahlan, idonta guda ɗaya ma shima ya mutu wai ruwan ciki ya tsiyaye gaba ɗaya, ƙafar hagun ma yanzu suna bayanin yanketa za'ai, Azima dai na cikin wani hali Ahlan, wannan yarinya sai dai Allah yay mata sakayya da wanda ya zama silar shigarta wannan hali". sosai take kuka sanda take maganar, wanda hakan ya ƙara tsawaita kukan Ilham. Ahlan a razane yace,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, paralyse Umma?, yanke ƙafa?, rasa ido ɗaya?, kai rayuwa kenan kowanne bawa da kalar ƙaddararsa, ita kuma Yaya ga ta yanda tata tazo mata. hasbunallahu wani'imal wakil". shima bai san lokacin da hawaye ya sakko masa ba, tausayin ƴar'uwar tasa yay matuƙar kama shi. Mai Martaba ya ƙaraso wajen jikinsa a mace, yana zuwa Ilham ta taso a jikin Hajiya Shema'u ta tafi ta faɗa jikinsa. ya rumtse idonsa sosai saboda tsananin tausayinta, ya kalli su Hajiya yace,"Dr yace kuna iya shiga wajenta". da sauri kuwa suka miƙe suka nufi wani dogon corridor hanyar da zai sadaka da room ɗin da aka kwantar da Fulani Azima. Mai Martaba ya zauna akan kujerar da suka tashi, ya kwantar da kan Ilham a cinyarsa, yay dauriya da dakiyar maganar da yake jin kamar da kuka a cikinta. yace,"kina so Maminki ta sami lafiya?". tai saurin ɗaga masa kai, yace,"to adu'a za ki mata ba kuka ba, indai kina kuka ba zata sami lafiya ba, kinga dai a halin da take ciki, halin da ko maƙiyinka ba zaka yi masa fatan ya shiga ba". ta ɗago daga cinyar tasa, yasa hannu yana goge mata hawaye, wani na kuma bin wanda yake gogewar. duk cikinsa ƴaƴa mata yafi son Ilham saboda sunan mahaifiyarsa da taci, ƙari da kuma da kyan halinta, dan duk cikin yaransa mata tafi kowa haƙuri da biyayya da nuna ita ɗin ba ƴar kowa bace. yana riƙe da hannunta ya nunfasa yace,"ya kamata ki koma gida haka Ilham, ba zai yiwu ki baro mijinki kizo ki tare anan ba, karki damu ko every weekend ne sai kizo kike ganinta kina komawa". tai saurin cewa,"Dad ni ba zan koma ba sai Mami taji sauƙi". yace,"a'a Ilham". cikin kuka sosai tace,"to Dad ai shima yayi min uzuri tunda yasan wacce bata da lafiya, ni dai ba zan koma ba, Allah Dad ba zan iya zama a ko'ina ba yanzu in ba kusa da Mami ba". Mai Martaba yay shiru bai ce komai ba, wucewar daƙiƙa ɗaya ya ɗauko waya ya kira Turaki, yana ɗagawa daga ɓangaren Turaki cike da girmamawa da tsantsar ladabi ya gaida shi. bayan sun gama gaisawa Mai Martaba yace da shi,"Muhammad babu damuwa dai ko idan Ilham ta zauna nan?". Turaki yace,"ba damuwa Dad". "ka tabbata Muhammad?, karka ce zaka yi kara ko kuma alkunya". yace,"ko ɗaya Dad, ai abinda ya zama dole shi ake dubawa". Mai Martaba yace,"to shikenan, Allah yayi muku albarka". daga haka suka yi sallama. su kai shiru daga Ilham har Mai martaba kowa yana jin ransa ba daɗi, in ace suna da iko kwana ɗaya tal ba za'a ƙara ba Fulani Azima zata warke, to amma lamarin ba nasu bane na ubangiji ne, sai dai su roƙe shi ya warkar da ita ba tare da tayi doguwar jinya ba. suna zaune kusan minti goma sai ga Sarauniya Mabruka wato matar Mai Martaba ta farko, ita da ƴaƴanta uku suna biye da ita tare da masu kula da su mutum uku. tun a washegarin ranar da Fulani Azima tai accident aka taho da ita Philippines domin ƙwararrun likitoci su dubata, dan Mai Martaba yana ganin kamar likitocin nigeria ba zasu iya ba, duk da cewar asibitin fada ma ba ƙanan likitoci bane acikinsa, kusan duk ɗinsu a ƙasar waje suka yi karatu, amma shi yafi ganin su taho nan ɗin. kuma families da dama sun so su biyo bayansu Mai Martaba yace a'a su ɗan dakata tukunna, ita kanta Ilham sai da aka kwana biyar sannan suka taho ita da su Hajiya Shema'u da Turaki, kuma shi ranar da yazo ranar ya koma bai zauna ba. kuma sai a yau da suka kwan 21days sannan mai martaba ya bar iyalinsa suka taho, don farko duk bai zaton za'aja haka ba, da zarar an mata aiki a ido shikenan zata dawo normal, to kuma likita sai yazo musu da bayanin duk da ya girgiza su. Sarauniya Mabruka ce ta fara sauka sauran biyun duk suna baya suma tare da nasu ƴaƴan. ta zauna kusa da Mai Martaba tana ɗago da Ilham daga jikinsa ta kwantar da ita a nata jikin, hadiman dake tare da ita suka watse suka tsaitsaya daga can gefe, Yarima Abbas da Yarima Lateef da Yarima Bilal suka zauna kusa da mahaifinsu ta ɗayan ɓarin. Sarauniya Mabruka tace da Mai Martaba,"ya jikin nata?". idonsa na tsaye ƙyam akan wata ƙofa cike da nazari a bisa faruwar accident ɗin ya bata amsa da cewar,"da sauƙi irin na malam bahaushe, zuwa anjima zasu ƙara shiga da ita theater za'aiwa ɗaya idon aiki, shima tana kukan bata gani da shi sosai, sai maƙogaronta da akai hoto akaga still akwai glasses na mota da suka farfashe mata aciki". "Allah ya sauƙe ya bata lafiya don nabiyyurrahmati". ta faɗa tana saka hannu ta goge hawayen da ya sauko mata. lamarin duk yasa jikinsu mutuwa, sosai suke
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243