Chapter 232
Chapter 232
"yau kin ji sun juya?". ta ɗaga masa rigar tana faɗin,"kalla fa yanda suke ta ƙiriniya, duk sai duka suke kai min ta ko'ina, suma ai sun gaji da zaman". Turaki bai iya cewa komai ba illa shiru da yayi yana ta kallon cikin dake motsi, yana jinjinawa girman ƙudirar ubangiji. gaba ɗaya sai yake jin tamkar yasa hannu ya buɗe cikin ya ɗauko yaran, Fillo kuwa kallon cikin kawai take yi a gefe guda zuciyarta na saƙe-saƙen yacca rayuwar zata juya, yanda komai zai koma saɓanin tunanin su da hasashen su, yacca komai zai faru anan gaba kaɗan, nan da ɗan lokaci kaɗan ba me yawa ba, hakan take taji a jikinta. "ba fa na so yarana su yi kama da mijin lukutar gombe saboda bana so su yi muni, ka daina kalle min su". ya rungumota jikinsa yana cewa,"wallah ki roƙi Allah su yi kama da ni kiga yanda za'a dinƙa miki layi a ƙofar gida, in kuwa su kai kama da ke to kin shige su, ƙila sai dai mu ke kulle su a store". bayan fitarsa ta zauna a gefen gado, ta rufe idanuwanta a hankali, yayin da hannayenta ke ɗore akan ƙaton cikinta, ita ɗaya ke ta saƙawa wai yanzu halitta ce a cikin cikinta, halittar da ya girma kuma zai fito nan ba da jimawa ba, shikenan da zarar sun fito ita ma ta samu nata babies ɗin, irin wanda take gani daga nesa don bata iya ɗaukar jariri, za su fito a matsayin nata, yayin da zata amsa wannan sunan mafi daraja na Uwa, ƴaƴan su ita da Turaki, Ƴaƴan su ikon su. sai taji ƙwalla na neman taruwa a cikin idonta, ƙwallar da take ta zallar farin ciki da wani bala'in jin daɗin da ba zai misaltu ba. ta lumshe idanunta, ƙwaƙwalwarta na haska mata hoton yaran acikin kanta, ana jibi Hajiya Madina zata rasu ana scaning sai taji tamkar ta ɗauko su a wannan lokacin, babies ɗin su na kwance a cikinta gwanin sha'awa, ga sunan clearly a jikin screen cikin hoton black and white, kansu a haɗe su na ta watsal-watsal yayin da hannun kowanne ke gefen bakinsa, idanunsu a buɗe tarr tamkar kayi musu magana su amsa maka. kawai sai ta fara hasko yanda kammanin babies ɗin zai kasance, bata san ya Allah ya tsara halittar kamannin nasu ba, wataƙila su yi kama da su, wataƙila kuma su ɗauko kamannin su daban, sai dai a son samunta duk su ɗauko kamannin Turaki, ta yan da zata dinƙa kallonsa a fuskarsu idan baya gida, ba ya ga hakama idan suka ɗauko kamanninsa zasu fi kyau, irin wannan kyan da sai ta dinga tofe su da adu'a a kaɗawar kowanne sakan na agogo. tashi tayi akan gadon, ta isa gaban dressing mirror ta ɗauko diary ɗinta, sannan ta duƙa ta ɗauki riyon kayan babies, ta fita a ɗakin Turaki ta isa zuwa nata. wadrobe ta buɗe ta ɗauko wasu set ɗin kayan sanyi da Hajiya Ramla tayo mata aiken su a jiya, sannan ta fita ta nufi ɗakin kusa da na Turaki, ɗakin da suka ware domin yaran su, ɗakin da Turaki ya rufe mata ido ya shigar da ita sannan ya buɗe yana nuna mata yana faɗin for our coming kids. ɗakin tamkar already dama yara na rayuwa acikinsa, domin anyi decorating ɗinsa da duk wasu kayan wasan yara, komai na cikinsa pink and white, kayayyakin da almost siyayyar Marigayiya Hajiya Madina ne, sai ta isa gaban gadajen guda biyu, a wannan lokacin babu abin da ƙwayar idonta ta haska mata irin hoton yaran a zahiri, ta gama ba su nono ta zo ta kwantar da su tana yi musu wasa, idan zata yi aiki sai ta saka musu karatun alƙur'ani kafin ta fita. yayin da suka girma su fara kiranta da Ummi, mahaifin su kuma su kira shi da Abie, ƙwayar idanunta ta ƙara haska mata lokacin da zata fara shirya su cikin kayan makaranta, ta ba su lunch box na abincin su, sannan tayi driving ɗin su zuwa makaranta, yayin da suka dawo ta zauna domin yi musu home work ɗin da aka ba su, idan weekend ya zo sai su dinƙa yada zango a field su na yin wasa tare da ita, ko kuma suke shiga cikin swimming fool. ita dai ta riga ta gama tsara yacca rayuwar jin daɗi zata kasance tsakaninta da ƴaƴanta, ba zata zamto ɗaya daga cikin irin uwayen nan da basa jan yaran su a jiki ba, ita zata zam yaranta na liƙe da ita ne ko da yaushe, ta dinƙa jin damuwar su suma su na jin tata, zasu zama manyan aminanta kamar yanda zata zame musu. sai taji kamar zuciyarta ta ƙara girma da tsiron wata sabuwar ƙauna ta daban, ƙaunar abinda ke cikinta ya mamaye dukka ilahirin jikinta, irin wannan ƙaunar ta ɗa da uwa, irin ƙaunar da zaka ji kamar zuciyarka na fitar da tiriri na son tabbatar da abinda kake so, Allah shahidi, shi zai yi mata shaidar irin son da take yiwa yaran, tana ƙaunar su fiye da ranta, a yanzu su ne rayuwarta, in har babu su tabbas babu ita. har ƙarfe uku tana ɗakin yaran a zaune, sallolinta duk anan tayi, abinci ma da aka kawo mata anan taci, ko ƙwalli ɗaya bata bari ya zuba ba gudun karta ɓata musu ɗaki. zuwa lokacin kuwa sun yi waya da Turaki yafi sau goma, bini-bini sai ya kirata yace ga shi nan yana hanya, kuma taji gaba ɗaya hankalinsa a tashe yake tun san da tace masa tana jin mararta na ciwo sosai, kamar dai zata fara labour. cikin mintunan da ba zasu wuce biyar ba bayan wayar su ta ƙarshe sai ga Turaki ya dawo, yana shiga ɗakin yaran ya ganta zaune akan darduma tana goge hoton enlargement ɗinsu ita da shi, fuskarta ta washe da murmushi, wani murmushi da Turaki zai iya cewa bai taɓa ganinsa a saman fuskarta ba. "welcome back". ya ƙarasa ya zauna a gabanta yana tankwashe ƙafafunsa, ya ƙura mata ido sosai yana ganin yanda take cije fuska, tana so ta ɓoye masa zafin ciwon da ke cinta, tana so ta ɗauko ƙarfin hali domin ta nuna masa babu komai, babu wani abu da yake damunta, babu wata matsala, duk saboda hankalinsa ya kwanta. "kin ci abinci?". "na ci, me ka taho min da shi?". ya matso da ledar da ya shigo kusa da ita yana buɗewa. "irin naman da kike so". ai ko nan da nan ta warci ledar, ta miƙa masa enlargement ɗin tace,"maƙala musu wannan, an manta jiya ba'a saka shi ba, mp3 ɗin su na karatun alƙur'anin ka bar shi a ɗakinka, ka ɗauko sai a ɗora musu a saman wancan table ɗin, ungo wannan diary ɗin sa min shi cikin wadrobe ɗin su, kasa shi ƙasan kayan Aayan". duk maganar tayi ne a lokacin da ta fara cin naman, Turaki ya miƙe yayi duk abin da tace, san da ya kammala har ta gama cin naman, ya shiga tsokanarta da kura, kasancewar naman yana da yawa sosai. sai da suka ƙara kimtsa ɗakin sosai sannan suka zauna a tsakiyar gadajen biyu, suka shiga hira, wata iriyar hira suke yi mai ratsa jiki, hira da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243