Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 32

Chapter 32

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
Download Book

akan ra'ayinka na cewar kai ba zaka yi aure ba, wannan ma zancen banza da wofi ne...idan ka manta to ka tuna su waye mu, saboda haka wallahi ƙaryarka ka bar mana abin kunya a tarihin sarautarmu...na san idan ta ra'ayin mahaifinka ne sai da ya zuba maka ido, to mu ba zamu zuba maka wannan idon ba kaji ni da kyau". A wannan lokacin idanuwan Turaki a kulle suke, kansa a duƙe yake, yana zaune ne a gefen ƙafafun macen da duk duniya baida kamarta Hajiya Madina. itace ta kawo ƙararsa ba kowa ba, aure take so yayi ya riga yasan da wannan batun ba tun yau ba, ya sa ni shine burinta akansa. to amma me yasa?, me yasa a matsayinta na wadda ta isa da shi bata gindaya masa umarnin hakan kai tsaye ba sai dai ta kawo ƙararsa gaban wanda cin mutumci shine abin yinsa?. wani dunƙulallan abu yaji ya tsaya a maƙoshinsa, zuciyarsa ta katse da raya masa abubuwa a sanda Hakimi ya ƙara yin magana. "Turaki ko dai baka da lafiya ne?, idan kasan akwai wannan matsalar a tare da kai to ka faɗa tun wuri a maganceta, duk da cewar abu ne da kamar wuya namiji kamarka ace yana da matsala makamancin hakan". Boɗejo dake gefe tace,"ah tou dai nima shi na gani. wannan zance dai na batun ba shi lafiya ma ƙarya ne, ni nafi ga wani algungumin ne ya jefe mana shi, tunda dai kaga maitar ibadar nan da yake ma yanzu fa duk ya daina, kuma wallahi ko waye Allah ya isa bamu yafe ba...yanzu duk wani dogon zance ba shi bane, a tashi tsaye a nema masa magani kawai idan aka biye ta uwar tasa da uban nasa ba zasu yi masa wannan abin arziƙin ba". Turaki ya buɗe idanuwansa ya zube akanta, magana ta ke tana ƙara kambaba zancen asiri ne akansa. bai san lokacin da bakinsa ya buɗe ya katseta da faɗin,"Boɗejo ke kuma komai ya faru shikenan sai kice aikin asiri asiri". tayi masa wani kallo ɗaya sannan ta maida kallonta kan Hakimi tace,"me na faɗa maka Yarima Babba tun kamin ayi zaman wannan kotun?, ai sai dai idan ban faɗa ba amma yaron nan sai ya tanka, baka ga kallon da yake min bane kamar ma zai tashi ya rufeni da duka...haka fa ubansa ya koya masa kuma alhalin ni ba irin rainon da nayi muku ba kenan, wallahi duk irin son da yake ma yaransa bai kama ƙafar wanda Ubanku Allah ya jiƙan rai ya nuna muku ba, amma ku dai baku san wani abu wai shi raina na gaba ba, hasalima wallahi baku san babba na magana ku saka baki ba, amma su dai Ƴaƴan Dukko halinsu kenan Babba na magana su nuna bai kai ba...to alhamdulillahi daɗin abin Turaki bani na kawo ƙararka ba Uwarka ce gata nan a kusa da kai, kuma billahillazi da ace lokacin da nake sarauniya ne sai kasan na faɗa ka saka baki". Turaki yay ɗan guntun tsaki, ya ɗago kai ya kalli Hajiya Madina, suka yi ido huɗu da ita. a kallon da yay mata ya gano expression ɗin dake tare da ita. sai yayi saurin kai hannu wuyansa ya shafo shi, ɗabi'arsa ce hakan. yawanci Boɗejo kance wani ƙullin yake shafowa. ya sauke numfashi, muryarsa ta fito a hankali, cikin girmamawa da biyayya yace da Hajiya Madina. "Maama ba sai kin kai ƙarata wani wurin ba. kin isa da ni, kin isa ki bani umarni na bi ko ina so ko bana so, kin isa kija layi kice kar na shata na haƙura dan dole na, bin zaɓinki dole na, yacca kike so nayi haka zanyi muddin hakan zai faranta ranki...". bai ƙarasa ba amon muryarta ya fito da faɗin,"aurenka nake son gani Me babban suna, ina so kayi aure tun ina da rai Hammansu, ka sani ina sonka fiye da numfashina, babban burina a yanzu shine naga aurenka, naga matar da zaka aura, naga jikana, naga kalar rayuwar jin daɗi da kwanciyar hankalin da zaka shimfiɗa da iyalinka...Hammansu wannan auren da baka so shine mutumcin mutum, kuma shine ƙarshen jin daɗin rayuwa...ita rayuwa nan guda ɗaya ce Hammansu, haka ran ɗan adam guda ɗaya ne. lokaci tafiya yake baya jira, so kai enjoying rayuwarka tun lokacin bai ƙure ba, ya zamana kazo baka mori dukkan jin daɗin rayuwar ba...babu wanda aka yiwa alƙawarin kaiwa gobe a wannan duniyar, tsari kawai muke da hange, kuma zata iya yiwuwa mu matu a lokacin da muke ta shirin tsare-tsaren gobenmu, and that will be the end of us, ni kuma ina so mu tafi ne a lokacin da muka bar masu tunamu a kowacce daƙiƙa. da zarar ance babu kai shikenan duk wasu memories daka bari suma sun tafi, amma ɗa fa?, shi ɗaya ne memory da zaka tafi ka bari a kasa mancewa da kai, hakan yasa nake so kayi aure tunda sauran lokaci, auren nan daga zuriya mai ƙarfi irin zuriyarmu, *SARAUTA*, ta yadda zaka bar bayanka, wannan kawai shine burina akanka Hammansu". idanuwan Turaki a ƙasan carpet suke, amma ƙwayar idonsa wasu yatsu ta ke hangowa sirara da suke karkarwa kamar waɗanda ake girgiza su. ya haɗiye wannan yawun dake saman harshensa zuwa cikinsa, sannan ya rufe idonsa ya buɗe a lokaci ɗaya. laɓensa na sama da na ƙasa suka tale, harufan bakinsa suka fito da faɗin. "Aure! zanyi aure Maama, zanyi yanda kike so, kuma insha'Allahu sai na cika miki dukkan burinki akaina, kuma insha'Allahu ba za'a wayi wata rana da za'ace kin rigani tafiya ba, ni nake so na rigaki tafiya Maama, ni nake so, bana so ki tafi ki barni, rayuwar zata yi min tsanani, zan daina jin daɗinta kwata-kwata, zan dinga jinta ne kamar ana min feshi da ruwan dalma, dan Allah Maamaaaa". maganar yake da kakkaryewar kowanne harafi, kuma maganar tasa ta katse gaba ɗaya a sanda yaja sunanta wajen faɗi. lokaci ɗaya ya nemi ya fita hayyacinsa. sautin kuka kawai yake ji acikin kansa, wannan sautin kukan na yarinta da na jarirai, saboda haka yay saurin saka duka hannayensa ya toshe kunnuwansa, tare da kifa goshinsa akan ƙafafun Hajiya Madina da ke zaune tana hawaye. har zuwa lokacin da ya daina jin ihun kukan acikin kunnensa sannan ya ɗauke hannunsa, ya shiga sauke numfarfashi, gaba ɗaya yanayinsa ya sauya, kamar ma ya burkice ne, hannayensa masu rawa a yanzu suka damƙe zanin Hajiya Madina. a jikinta ta ke jin irin rawar da jikinsa yake yi, jikinsa na rawa amma ita a wannan lokacin tata zuciyar ce ta ke rawa, so take itama ta taya shi kukan, irin kukan da yake yi, so take ta taya shi ko yaya ne, ko da sau ɗaya ne. Zaytuna dake kusa da Boɗejo ta taso cikin kyarmar jiki, ta dawo gabansa ta durƙusa, sannan ta shige jikinsa gaba ɗaya itama nata kukan na ƙara ƙarfi, Turaki yay mata wata runguma da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma na riƙe ne da zanin Hajiya Madina da yake jin kamar a lokacin ƙwace musu ita za'ayi. wani tausayi ya ratsa zuciyoyin duk wanda yake zaune a parlon banda zuciyar mutum ɗaya da ke ƙissima tarin abubuwa acikinta. lissafi take, lissafin yanda komai zai tafi, lissafin

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243