Chapter 175
Chapter 175
dariya da haƙori ɗaya ko su ciji hancinsu in ba haka ba a dafa su a bawa mage ta cinye, sai suyi ta kuka suna bada haƙori in Baffa yaƙi haƙura sai su ɓuya a lambu, sun sha kwana acan yafi a ƙirga saboda basa son faɗan Baffa da dukansa ko kaɗan. sai ta sami kanta da yin dariya sosai, sai da ya ɗeba mata kewa tukunna yay mata sallama ya tafi, bayan tafiyar tasa duk sai taji babu daɗi, ta dawo ta koma upstairs tai kwanta zuciyarta cike da son ganinta a gida, yanzu ta san su Dadda sun ɗau hanya, tana ta so ta yi waya da Umminta taji muryarta, tun da ta tashi take mugun kewarta. ban da tunane tunane babu abin da takeyi har ƙarfe goma, sai lokacin ta tuna da aiken da ta bawa Baba, hakan yasa tayi saurin saukowa ta fita, tana fitowar kuwa ta tarar da Baba me gadi yana isowa entrance na ɓangarenta, ta tafi da sauri dan karɓar masa kayan, sai dai kamin ta ƙarasa Turaki ya rigata, ta ƙaraso wajen Baban a sanda Turaki ke miƙa masa hannu alama na ya ba shi kayan ba tare da ya ce masa komai ba. Fillo ta haɗe rai kamar ba ita ba, ko kallon in da inuwarsa take bata yi balle kuma shi kansa, tana yiwa Baba sannu da zuwa ta miƙa hannu za ta karɓi kayan taji saukar muryar Turaki a tsakiyar kanta. "idan har kayan nan suka je hannunta, to ka nemi wani gidan ka ci gaba da aikinka". ta dakata da karɓar ledar tana kallon hannun Baba da ke aikin karkarwa, taji mugun tausayinsa ya kamata, tana kallo ya kalleta fuskarsa nayi ma ta nuni da tayi haƙuri ta rufa masa asiri, ta gyaɗa kanta kawai shi kuma ya bawa Turaki ledojin, ya karɓa ya juya ya bar wajen, itama zata bar wajen Baban ya ce,"Hajiya ga canjin ki". ta waigo tana yi masa murmushi ta ce,"ka riƙe Baba". ya waro ido waje yana cewa,"dubu biyar ce fa Hajiya". ta ce,"babu komai Baba". ta faɗa tana barin wajen tare da goge ƙwallar idonta, shi kuma ya bita da kallo yana ta zazzaga ma ta adu'a yana sa ma ta albarka. kai tsaye parking lot ta nufa in da take hango Turaki a wajen motarsa ya buɗe ya shiga ƙafarsa ɗaya a waje, ya ajiye ledar kayan da ya karɓa, ɗaya a ƙasa ɗaya a saman murfin booth, ta ƙarasa wajen motar cikin sanɗa ta durƙusa ta kwashi kayanta, ta yi saurin barin wajen kamar za ta kifa ƙasa, fatanta ɗaya ta isa har ƙofar part ɗin ta bai fito da ga cikin motar ba, abin da ba ta sa ni ba shi ne, tana ɗaukar kayan ta juya shi kuma ya fito daga cikin motar, mamakin ƙarfin hali irin na ta shi ya tsayar da shi kawai yana bin bayanta da kallo, ya kasa yi mata magana balle ya cimmata ya karɓe, shi kallon ma da yake yi ma ta tun jiya kamar da akwai abin da takala. ya jijjiga kansa, koma me take ji da shi zai saitata ne within wani ɗan lokaci. bayan sallar azahar tana zaune kan darduma ta zabga uban tagumi sai taji kamar hayaniya a compound, ta miƙe da azama ta leƙa ta window sai taga su Adda Asma'u ne, ai kuwa babu shiri ta wancakalar da hijab ɗin jikinta ta fice da sassarfa me kama da gudu, saura kaɗan ta zame a steps, ta sauko parlon a san da ta ga ana ta shigo da manyan kuloli na abinci ana wucewa da su kitchen, taji Inna Hajar na cewa da masu shigar da kayan,"kar ku saka su da ga in da babu iska kayan gara ne". ta yi tsallen murna da farin ciki ta faɗa jikin Raudha, duk su ma sauran sai suka maƙalƙaleta anata Allah sarki ƴar marainiya, sai kuma aka ɓige da yi ma ta tsiya ana tsokanarta amaryar ƙamshi, har ta fara kumatu, ta harari Maijidda da ke ta kallonta tana murmushi. ta zame da ga wajensu san da Adda Asma da Dadda ke shigowa, ta tafi da sauri ta faɗa jikin Dadda, sai ga hawaye kamar da ma jiran ganinta su ke. Adda Asma ta ce,"yau naga tsiya, to in dai kuka za ki yi kam sai mu juya". ta yi saurin goge hawayen tana faɗin,"ku yi haƙuri Adda Asma na daina". ƙememe Adda Asma ta hana su Raudha zuwa bedroom ɗin Fillo, kamar ta san gulma ce zata kaisu, ta ce wallah duk wanda ya kuskura yaje ma ta ɗaki sai ta ɓata masa. ita dai Fillo ba ta ce komai ba, daɗi duk ya isheta saboda ganin ƴan uwanta, ji take kamar kar lokacin tafiyarsu ya yi, Dadda tasa su Raudha suka shiga kitchen ɗinta su ka ƙara gyara ma ta shi da cikin store, su kuma suka haura sama zuwa bedroom ɗinta, wasu kayan da aka zazzo ma ta da shi aka ƙara kimtsa ma ta su, da aiken Dada da ta bayar a ƙawo ma ta, sannan su ukun duk suka zauna suka ƙara yi ma ta ƴan nasihohi da ba'a taɓa daina yiwa ƴa mace in har an aurar da ita. a parlo suka zauna akai ta hira har akai sallar magriba tukunna suka yi haramar tafiya, Fillo ta riƙe Maijidda akan lallai ba zata tafi ba, ta rakosu compound tana ta kuka irin na jiya. bata ƙara jin kewarsu ba sai da magriba ta yi, lokacin ne kuma ta fara jin yunwa ta shiga kitchen, ta buɗe freezer taga babban botiki na miya da su ka zo ma ta da shi ɗazu, ta ɗauko flask ɗin da Inna Hajar ta faɗa ma ta akwai ferfesun kifi a ciki, ta zuba kaɗan ba da yawa ba, ta buɗe oven ta ɗauko gasassan biredi, sai dai ko da ta zauna sai taji kasa ci, dole haka tasa hijab ta fita ta kaiwa Baba me gadi. tana zaune a parlo har akayi sallar isha'i, a lokacin tsoro ya fara kamata, tayi azamar barin parlon ta koma upstairs ta kulle ɗaki, ta dunƙule akan gado tare da toshe kunnuwa dan sam ko ƙarar AC bata son ji, kamar dai yanda ta kwana jiya ita ɗaya haka yauma ta kwana ita ɗaya, cike da tsoro fal kamar zuciyarta zata bar ƙirjinta. *Masarauta Kaltungo.* wani mugun ɗoyi ne ke tashi a cikin turakar ta Fulani Azima, tana can da ga kusurwar ɗakin an kwantar da ita akan gado, ba ma lallai ka lura mutum ba ne idan ka shigo, halittarta tayi mugun muni kamar ba wannan macen ƴar gayu da ƙwalisa ba, me ji da mulkinta da kuma girman izzarta. idanuwan da suka firfito waje kamar na ƙwarangwal sai kallon Ilham take yi wacce ke durƙushe da ga can bakin ƙofa, tayi tagumi tayi nisa acikin tunani, taji bala'in tausayin yar tata ya kamata, ta sa ni alhakin mutane da dama da ta ɗauka ba lallai ya bar ɗiyarta taji daɗin zaman gidan aure ba, ko me ya faru da ita ta san ita ta janyo ma ta, ga shi ba ta da bakin maganar da zata nemi yafiyar mutanen da ta cuta su yafe ma ta ko ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243