Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 52

Chapter 52

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,221 words 0 views Progress saved
Download Book

Ammi amma ba yanda kike tunani ba ne, yau da safe ko gidan nan banzo ba Allah". taja tsaki tace,"aikin banza. to ka juyo ka kaini unguwa in ka dawo kaje duk inda zaka je". yasa hannu ya shafa kansa tare da rufe idonsa bai ce komai ba kuma bai motsa daga inda yake ba. Ammi ta ƙara cewa,"baka ji me nace ba ne?". yace,"naji Ammi". tace,"ba zaka kainin ba ne?, ko kuma izinin uwar taka zaka fara zuwa ka nema?". ya ƙara sosa kansa yace,"ai Umman bata dawo ba Ammi". da a kusa da ita yay maganar da babu abinda zai hanata buge masa baki, cikin zafin rai tace,"zan zauna zaman jiranka ne ko ya?". yace,"Ammi dan Allah ki kira Aliyu, Inna Wuro ce ta kirani Nuratu babu lafiya zan ɗauketa mu wuce asibiti...". tun bai ƙarasa ba ta dakatar da shi,"ai nasan da Aliyun ban ce shi ba sai kai. Yusuf matarka ko mutuwa zata yi ba zaka je wurinta ba a yanzu sai ka kaini ka dawo, na faɗa maka in ba haka ba kuma zaka sha mamakina, zan maka abinda baka taɓa tsammani ba daga gareni". ƙasan zuciyar Yusuf yaji babu daɗi, bai san ya zai kimanta mata abinda yake ji ba, shi ta barsa yaje yaga kawai halin da Nuratu take sai ya fito ya kaita, hakan ne kaɗai zai basa natsuwar yin driving ɗin da take so, to amma yasan ko me za'ai ba zata yarda ba, kamar yanda ta faɗa ne ko mutuwa Nuratu zata yi, sannan kuma uwarsa ce, jayayya da ita ko bijire mata ya ɗaukowa kansa hanya ta taɓewa ne. dabara ta faɗo masa yace,"Ammi na bar motata a hospital". a fusace tace,"ko da motarka ma kazo ni ba zan shiga cikinta ba, ina da tawa a ita zaka kaini. motarka ai sai Falmata amma ba ni ba, kuma ni dai na faɗa maka ƙafarka ka ɗaga kayi cikin gida to ban yafe ba, idan kaga dama kai ta tsaiwa muna dragging muna ɓatawa junanmu lokaci". Yusuf ya kulle idonsa ya fesar da iska me zafi daga bakinsa, ya katse wayar yana kallon side ɗin Inna Wuro ya koma da baya ya nufa wurin motar. a cikin motar ya sameta a zaune, ya buɗe driver seat ya shiga, bai juya ya kalla back seat inda take ba yace,"Ammi ina yini, kuma ina zan kai ki?". Ammi tace,"gaisuwarka dai ka riƙe, inda zaka kaini kuma kowanne store ya kama, wurin dai da zan samu abinda na fita saya, dawowarmu kuma sai Allah yayi". tana yin shiru yay ma motar key, yay reverse har tayar motar na amsawa, wanda inda ace wajen da ƙasa sai ƙura ta tashi. suna fitowa daga cikin gidan kamar ance ta ɗago kai daga kallon wayarta taga motarsa. tace,"kace a hospital ka bar motar?". sai daya kulle ido sannan ya iya ƙaryar cewa,"dama nace da Mujahid ya kawo min ne". tai murmushi kawai tare da girgiza kai bata ce komai ba. store wurin huɗu suka je, ba dan tana rasa abunda zata saya a kowanne ba, sai dan kawai ta ɓata masa lokaci, dalilin da yasa ta dinƙa gutsira sayayyar kenan, har yamma tukunna suka ɗauko hanya. sai da suka shigo cikin anguwarsu sannan ta ƙara ce masa,"nace maka gida zamu wuce ne direct?, to kai reverse ka kaini gidan Kawun ka". shirunta ya haɗe ta kiran daya shigo a wayarsa, ya kalla sunan dake yawo akan screen ɗin, ganin sunan Inna Wuro ya kulle idonsa da yake jin yana masa zafi, zuciyarsa ta matse hankalinsa na ƙara tashi. minti goma sha biyar suka ɗauka kamin su iso cikin unguwar gargajiyan, da ƙyar motarsa ta shiga cikin layin, daga bayan gidan yay parking motar. yana kallon Ammi ta mirrow ta buɗe motar ta fita ba tare da tace masa ƙala ba, yaji kamar ya fashe da kuka. sai da ta kai ƙofar gidan tukunna ta sami yaro ta nuna masa mota tace yace da mai motar ya miƙo mata jakarta. a lokacin hannu kawai Yusuf ke jira ya ɗora akansa ya saki kuka, ya san da biyu ta manta jakar. jakar kawai ya bata ya juya ya koma mota, Yusuf tun yana kallon wucewar sakanni har ya koma yana kallon adadin mintuna, minti 1 zuwa 5 suka wuce har aka tafi goma Ammi bata fito ba, lokacin ne kuma ya ɗauko wayarsa da niyyar kiranta sai yaji anyi knocking glass, yana ɗaga kai yaga Kawunsu wanda yake Yaya ne a wurin Ammi me suna Malam Mudi. cikin sauri ya buɗe motar ya fito ya duƙa yana gaida Kawun kansa a ƙasa. "Yusuf gidan baƙonka ne daka ƙi shiga ka zauna a mota?". Yusuf yasa hannu ya sosa ƙeyarsa yana neman abinda zai ce, kan yay magana Kawun ya ƙara cewa,"ai Zainab ɗin ke cewa kai ka kawota kana waje, shiru shiru baka shigo ba shine nace to bari nazo naji ko munyi maka wani laifinne". Yusuf yace,"a'a wallahi Kawu babu komai, dama na ɗan tsaya ne muna waya da abokin aikina, shiyasa ban shiga ba amma dama yanzu nake niyya". tare suka jera suka nufa gidan, suna tafe suna tattaunawa akan wasu batutuwa har suka shiga gidan, da yake Malam Mudi mutum ne me sakin fuska. acikin gidan Umma Ladi taitawa Yusuf tsiya tana cewa ko dai sirikinta zai zama ne bata sani ba da ya maƙale a waje yaƙi shigowa, shi dai murmushi kawai yake har suka fito. da suka koma gida shi ya kwashi siyayyar da Ammi tayi ya kai part nata, sannan ya fito ya wuce na Inna Wuro, yana tafe yana duba agogo, daga lokacin da ta kirasa zuwa yanzu awa biyu kenan. hularsa ya ɗaga ya sharce gumin daya haɗo masa duk da cewar ba zafi akeyi ba, amma halin da yake ciki na rashin sanin a wanne hali Nuratu ke ciki yasa shi haɗa zufa. babu kowa a parlon lokacin da ya shiga, tsaye yayi kawai yana kallon trolly ɗin kayan Nuratu dake tsakiyar parlon a ajiye. mamakinsa ya tsaya akan Inna Wuro dake janyo ƙaramar trolley tana fitowa daga cikin ɗakinta tana maganganun ƙasa-ƙasa, har ta ƙaraso gabansa bai iya ɗauke idonsa daga kanta ba, amsar tambayar dake ransa kawai yake so ya samu tun kamin yayita. bata lura da shi ba saboda sababin da take tayi har sai da ta zo gabansa, shima warin asibitin da taji ne yasa tasan da tsayuwarsa a wurin. ta ɗago tai masa kallo ɗaya ta ɗauke kai. "ashe kazo, nai zaton ai ko ka zama tarihi da nake ta danna maka kira kana ƙin ɗauka. baka san ni ba wata tsiyar zance kayi min ba, idan ka manta na tuna maka ɗana me wannan ƙaton gidan ya tara abinda kai baka da shi, dan haka nafi ƙarfin roƙo a wurinka Yusuf". tasa ƙafa ta tura masa duka trollys ɗin gabansa tana cewa,"gasu nan, dama niyya nake na fita da su na ajiye su daga bakin ƙofa sai kuma Allah ya kawoka ka rage min aiki". Yusuf dai kallonta kawai yake yi, sai da tai shiru sannan yace,"kiran da kika min na mene?". jin yanda yay maganar ta ɗago ido ta kallesa ta taɓe baki sannan tace,"naga duk ka firgice kamar wanda ya tsarewa

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243