Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 104

Chapter 104

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
Download Book

tabbatar da nauyin sumanta, sannan ya ɗago kansa ya kalla ɗaya daga cikin yaransa yay masa alama da yazo. mutumin da duk cikinsu shine ƙato yazo ya hau kan gadon riƙe da shimfiɗeɗiyar igiya a hannunsa, ya jirkitar da Fillo gefe ya ɗaure mata hannayenta ta bayanta, ya kuma haɗa ƙafafuwanta wuri ɗaya suma duka ya ɗaure, sannan ɗaya daga cikinsu ya miƙo masa masking tape ya nannaɗe bakinta da shi. Sai da suka tabbatar ko da ta farka babu ta yanda zata iya wani ƙwaƙwƙwaran motsi tukunna duk suka fice daga ɗakin suka barta ita ɗaya suka rufe da key. Fillo dai bata farka ba sai da ana tada iƙama na sallar asuba, a hankali ta buɗe idonta da ƙyar ta shiga bin ɗakin da kallo, tana jin kanta yay mata wani irin nauyi, ga warin wani abu a ƙofofin hancinta, gaba ɗaya wani irin ciwo jikinta keyi mata tamkar wadda aka ɗau kwanaki ana duka, ta rufe idonta ta rumtse sose sannan ta buɗe tana jin eyelid nata yay mata nauyi sosai, sai a sannan kuma ta fara bin ɗakin da kallo har ta sauke ganinta akan roof na ɗakin, sose take kallonsa da mamaki sannan ta ƙara juyar da ƙwayar idonta ta sauke akan ƙofar ɗakin, daga roof ɗin har ƙofar basa cikin irin waɗanda ta sani, ba ƙuma sa cikin inda tasan tana kwana. daga paint na ɗakin har kan gadon da take duk bata san su ba, to aina take?. tana ci gaba da bin ɗakin da kallo tana so ta tuna a inda take, da kuma yacca akayi tazo nan ɗin amma ta kasa, ƙwaƙwalwarta gaba ɗaya ta cunkushe taƙi yin tunanin abinda take so. sai tayi ƙoƙarin motsawa don ta tashi amma sai taji ta kasa, ta ƙara yunƙurawa taji babu ta yanda za'ai ko da hannunta ya motsa balle ƙafarta, wannan ya tabbatar mata da cewar a ɗaɗɗaure ta ke gaba ɗayanta. sai sannan tayi ƙoƙarin buɗe bakinta tayi magana shima sai taji bakin a liƙe yake, ta hanci kawai ta ke numfashi banda baki. sai ta rufe idonta tana juyar da fuskarta ɗayan side ɗin sannan ta buɗe idon, nan ta ƙara tabbatar da bata san ina ne nan ɗin ba, take ta fara kokawa da numfashinta saboda tsoro, dai-dai lokacin kuma taji ana sallamewa daga sallah a masallaci, sallar da ta fahimci sallar asuba ce tunda raka'a biyu taji anyi, cikin kanta taji ƙwaƙwalwarta na biyo mata innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, kuma a hankali cikin ikon ubangiji tunanin abinda ya faru da ita ya dawo mata. sai ta rumtse idonta hoton komai na haska mata tarr tun daga ɗora wuƙa a maƙoshinta, da shigar da ita cikin mota, da kuma juyowa da akayi aka toshe mata hanci. take tayi ƙoƙarin ƙwalla razananniyar ƙara sai taji ashe fa bakinta a manne yake. to Ina ne nan ɗin?, waɗanda suka ɗaukota su waye?, me yasa suka yi mata irin wannan ɗaukowar?, nan ɗin da suka kawota me zasu yi mata?, me yasa suka ɗaɗɗaureta haka har da toshe baki?. tarin tambayoyin da ta yiwa kanta kenan, kuma take ƙwaƙwalwarta ta bata amsa da,_"you have been kidnapped"._ take kuma zuciyarta ta ƙara maimaita mata innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. ƙirjinta ya dinga bugawa hawaye nabin kuncinta, tashin hankalinta ɗaya shin wanne hali Kaka ta ke ciki yanzu?, Wanne hali Amir yake ciki?, wanne hali Maijidda da Yami suke ciki?, ya Hajiya Madina zata kasance idan ta dawo taga babu ita?. idan har kidnappers ne suka ɗauketa shin sunyi contacting da wani nata?, wa suka tuntuɓa?, adadin nawa suka nema kuɗin fansarta?, wa zai biya maƙudan da suka ambata?, sai brain ɗinta ta ƙara biyo mata innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Hasbunallahu wani'imal wakil. ta buɗe idanunta ruwayen hawayen ciki na samun damar gangarowa, kuma a sannan ta fahimci hasken dake ta wajen window da take gani gari ya fara wayewa kenan?. take kuma ta tuna da cewar fa bata yi sallar magriba da isha'i ba, ga asuba ma a kunnenta akayi amma bata yi ba. taja ƙafafuwanta da suka sandare tana so ta lanƙwasa su sai taji kamar zasu karye idan tayi hakan, saboda azabar ciwon da suke yi mata. babu ta yanda zata iya miƙewa ta tashi ko da zaune ne, balle kuma ta iya sauka daga kan gadon, dan haka kawai sai ta fashe da kuka sosai, can bayan wasu awanni taji muryar mutane ƙasa-ƙasa a bakin ƙofar ɗakin. Ta juyo da fuskarta tana kallon ƙofar, tana kallo aka turo ƙofar mutane uku suka shigo, Ƙaton cikinsu shi ya fara shigowa tukunna wasu sirara suka biyo bayansa bayan ɗayan cikinsu ya maida ƙofa ya rufe. tana kallo su suka ƙaraso bakin gadon, Ƙaton ya jawo wata kujera ya zauna yana facing ɗinta, tana kallo yaywa ɗaya daga cikinsu alama wanda shine duk yafi siranta a cikinsu, ya zagayo daga bayansa ya hau kan gadon ya ɗagata ya zaunar da ita, sai a sannan ta sami damar ƙarewa inda take kallo da kyau da kuma mutanen dake tare da ita fuskokinsu duka a rufe. ƙatoton ya auna Fillo da bakin bindigar da take hannunsa yace,"zamu buɗe maka bakinka, idan har muka buɗe kayi wani yunƙuri na yin magana ko kuma ihu sai na fasa kanka da alburushi". Ya faɗa muryarsa da ƙarfi har tana amsawa a ɗakin, sai dai kana jin hausar tasa kasan riƙaƙƙen inyamuri ne. hawayen Fillo ya ƙaru akan fuskarta, tana jijjiga masa kai alamar taji me yace cike da tsanin tsoro gami da tashin hankali. Ƙaton ya kalli tsamurmurin dake kan Fillo tsaye yay masa alama da bakin bindigarsa. take tsamurmurin yasa hannu ya ɗaye masking tape dake manne da bakin Fillo, tsananin azaba yasa ta rumtse ido don ji tayi kamar ya haɗo da fatar bakin nata ne ta cire. so ta ke tasa hannu ta shafa wurin ko ta sosa amma babu dama, tunda basu kunce mata hannu ba, saboda haka sai ta rumtse idonta sosai tana jinginar da kanta da bango har sai da taji zafin ya lafa tukunna ta buɗe. ta buɗe ido ta sauke kan ƙaton mutumin dake latsa waya, rabin fuskarsa rufe take da hanky, tana kallo ya ɗaga hannunsa, ɗayan mutumin dake tsaye tun ɗazu a bayansa ya zagayo ya dire kwanon abinci a gabanta da pure water guda ɗaya. sai tabi kwanon abincin da kallo sannan ta ɗago ta kalli ƙaton dake saita da ita da bindiga, ya zare mata manyan idanuwansa yace,"buɗe kaci". tana ƙoƙarin danne kukanta tace,"dan Allah zan fara yin sallah tukunna". mutumin ya sunkuyo da fuskarsa kusa da tata, a tsawace yace,"kaga nayi kama da wanda ke yin Sallah?, to nan wurin da kake gani ba'a sallah, ko adu'a muka ji kayi sai mun ɓula kanka da alburushi. adu'a ɗaya muka yarda kayi shine a biya kuɗin fansarka, daga wannan bamu yarda da kowanne kalan adu'a daga bakinka ba, do you hear me well?". da sauri ta ɗaga kanta sai dai bata jin zata iya ta zama haka ba tare da sallah ba, don haka ta ƙara buɗe baki tace,"nayi muku alƙawarin wallahi ba zanyi wani motsi ba, ko adu'ar ficewata daga nan ma ba zanyi ba muddin ba zaku cutar da ni ba, amma don girman Allah

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243