Chapter 90
Chapter 90
mugun nisa, wani irin zafi take ji a zuciyarta kamar ana rura wuta, in ace ta ɗago a ɗazu da tabbas babu abin da zai hana hannuwanta shaƙe Turaki, in yaso suyi accident ɗin da gasken gasken. kafaɗarsa ya janye nan take kanta ya ƙwalu da kujeran, ta buɗe ido a hankali tana kallon inda suke, bata ko motsa ba har ya fice daga motar, tana kallo ya saka lock ya wuce ya barta, ita kuma ta rakasa da ido. tana ganin yacca ƴan tsirarrun staffs da basu wuce ba kowa na gaida shi, shi kuma yana ɗaga musu hannu. duk ƙoƙarin da tayi don ganin lock ɗin motar ya fita ta kasa, kenan rufeta yayi a motar ya tafi ya barta?, koma me zai faru da ita ya faru da ita?, to me yake nufi da ɗaukota ɗin?, ga shi ya kashe Ac balle ta samu sauƙin zafin gari da na zuciyarta da take ji. wani malolon baƙin ciki ya tokare mata zuciya, sai ta kifa kai da gwiwa ta fashe da kuka, kuka take sosai har tana jin kamar zata shiɗe, ga kanta na uban sara mata, ga zufa duk ta wanke mata jiki, sai da tayi me isarta tukunna ta ɗago tana goge hawayen, tana jan majinar hancinta ta ƙara trying buɗe motar amma taƙi buɗuwa. sai kawai ta jinginar da kanta jikin kujerar ƙirjinta sai bugawa yake, ta cikin glass ɗin ta fahimci magriba ta gabato saboda yanayin yacca garin ya lulluɓe, zuwa lokacin duk staffs sun ɗaɗe sai me gadi kawai da take iya hangowa ta cikin mirror. ta rufe idonta tana bin suratul Yusuf dake tashi cikin ƙira'ar Yousuf Kalo. Turaki kuwa tunda ya shiga office ɗinsa zama yay kawai ya rufe idonsa, yayi hakan ne kawai saboda temper ɗinsa yay cool, dan in yaci gaba da kasancewa tare da ita a yanda yake mugun jin haushin abin da tayi ba abin da zai hana sa illata ta. sai da ya ɗauki tsawon awa guda bai motsa a yanda yake ba, yana kallon kira daga different numbers na shigowa wayarsa amma babu ɗaya da yay picking. Fillo dai har sannan tana zaune sai wurga idanu kawai take yi, Allah ɗaya yasan yanda take ji a cikin ranta, taja Allah ya isa tafi kai ashirin, in ace da wani abu da zata iya fasa glass ɗin tuni ta fasa ta fita ta windown. tana cikin tunani a ranta sai taga Turaki ya fito daga wani building daban da inda ya shiga ɗazu, cikin sauri yake tafiya yana sauke hannun rigarsa da ye tattare, da alamu alwala yay zai wuce masallaci tunda ga ruwa nan a fusakarsa. bata ɗauke idonta akansa ba har sai da ta daina ganinsa, bayan minti goma sai taji lock ɗin motar ya fita, kuma kamin ta kai ga buɗe murfin idonta taji ƙofar side ɗin da take ta buɗe. "out". taji muryarsa ta shiga kunnenta san da take buɗe idonta duka. kamar tayi banza da shi sai kuma taji tana tsoron yin hakan, Allah shahidi bata tsoron uban kowa a duniyar nan amma tana mugun shakkar Turaki. ta tattaro mayafinta tana ƙudundune jikinta sannan ta fito a cikin motar ta tsaya a gefensa, tana fitowa ya rufe yay gaba yana cewa da ita,"follow me". tabi bayansa tana ɗan kalle-kalle, sai yaba kyan company ɗin take yi, daga waje ma kenan ina kuma ga an shiga ciki. suka shiga cikin office ɗinsa sannan suka wuce cikin wani ƙaton parlo, inda anan ne yake Turaki ke hutawa. "kiyi sallah". abinda yace mata kenan ya wuceta ya zauna kan ƙaton farar cushion. Fullo ta kalla haɗuwar parlon ta ƙara kallo tana me jinjina uban yawan dukiyar da aka kashe wajen ginin company ɗin da kuma abinda aka zuba acikin office ɗin, wato kuɗi dai suna inda suke, talaka da baida su ne yake ganin kamar babu su kwata-kwata. kanta a ƙasa ta fuskanci kujerar da yake zaune, muryanta a hankali tace,"banda alwala". yanda tayi maganar kawai yasa shi ɗago da kansa yana kallonta, ko kurma yaji sautin murayar nata yasan da ɓacin rai aciki. sosai yake kallonta da son gano abin da yasa tayi uban hasken da yake gani ajikinta, ba haka yasan asalin hasken fatarta ba, to daga ina wannan mugun farin?. jin yay shiru ta ɗago kanta karaf suka haɗa ido, ta tsuke fuska da baki tana ƙara ɓata rai. shi kuma yay mata nuni da hannu yana mata nuni da toilet. bata motsa ba kawai ta tsaya, ita ba zata iya shiga toilet yana zaune a wurin nan ba, sai dai in su shekara a haka, in yaso daga baya ta rama sallolin. da kansa ya gane manufarta, hakan yasa ya miƙe ya fice bayan yace mata,"don't waste my time". yana fita ta shiga toilet ɗin, cikin toilet ɗin kansa mugun ƙamshi yake kamar ba'a shigarsa. tai alwalan ta fito, mayafinta ta yafa ta tayar da sallah akan darduman da ta gani. la'asar da magriba tayi a haɗe, bayan ta idar ta duƙar da kanta saboda mugun sarawar da taji yana yi, ga jikinta ya fara zafi alamun fever na son kamata. ita kanta ta san ma dole tayi zazzaɓi da ciwon kai ko saboda kukan da tasha a yau. minti 1,2,3 har minti ashirin suka wuce Turaki na zaune office yana jiran fitowarta amma shiru. cikin ransa ya ayyana duk yanda akayi jira take ya koma yace mata ta fito, tsaki yaja ya tashi ya koma cikin parlon. zaune ya ganta har sannan akan darduman kaman me lazimi, to amma jin motsinsa bai sa ta ɗago ba, alhalin ya santa da shegen tsoro, ya tsaya yana kallonta yaga dai durƙushen kanta kamar ba na lafiya ba tukunna ya ƙarasa ciki ya zauna kan kujerar dake kusa da ita. yasa hannu ya ɗago kanta looking at her innocent face da yay ja, with the other hand ya taɓa forehead nata yaji zafi rau. ya rufe idonsa kaɗan ya buɗe yana ganin yacca hawaye ke suntiri akan kumatunta, kallon hawayen yake yana hango lokacin da yake zaune a gaban Hayyo yana faɗa masa cewar,"ehh kamar uba nake a wurinta amma ni ba mahaifinta ba ne, wannan yarinyar da kake gani ai ƴar zina ce, ƙwarai ƴar gaba da fatiha ce ranka ya daɗe, mahaifiyarta ma mahaukaciya ce, garin haukar nata ta gudu shekaru da yawa har yanzu bamu ganta ba, kuma har yanzu ni ban saketa ba. amma dai saboda a rufawa yarinyar asiri indai da gaske kake sonta ranka ya daɗe kawai ka biya sadakinta yanzu a take, batun sauran kayan al'ada da ake yi duk ba sai kayi mata ba, tunda dama ba faɗar addini bace, sadakin dai nata kawai ka kawo itama idan an bata babu hankalin riƙe su, tunda dama ni ne maɗaurin aurenta, babu wanda ya san danginsu tunda a titi na tsinci uwar naji tausayinta na aureta. ita kuma tsohuwar da kake cewa Yarinyar na hannunta gaskiya to ban ma san wace ba, ƙila ma ko irin tsaffin nan ne macuta". ya ƙara hasko lokacin da yasa hannu a aljihunsa dan ɗauko kuɗi, amma sai yaji babu komai. sai ya ƙara kallon Hayyo wanda ya gano tsananin kama ta Fullo a tare da shi, ya sauke
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243