Chapter 4
Chapter 4
kallonta ga Maijidda tace da ita. "waye wancan ɗin? tunda naga ke babu wanda ba ki sa ni ba acikin gidan nan saboda shegen shishshigi...cikin masarauta ma idan aka je yanda kike faɗar sunan jama'a kamar kece uwarsu". "kanki ake ji. yanzu amsar tambayarki zan baki ko na jira ki gama neman maganar?". Maijiddan ke maganar tana ta shan mangwaronta. "ki riƙe amsarki kar ki faɗa ai ba damuna yayi ba. dama naga ne ban taɓa ganin irin halittar bane acikin gidan nan tsawon zamana". "to sunansa Turaki". jin sunan da Maijidda ta ambata ya ƙwala ƙarar sautin wani abu acikin kanta, babu shiri ta miƙe a zabure tana gyara ɗaurin zani. "me kika ce?". "ba ki ji me nace bane hala? to nace Turaki ko". lokaci ɗaya idon Fullo ya manne a bayan Turaki da ke tafiya yana kusan kaiwa ga barin harabar ɓangaren masu aikin gaba ɗaya. a hankali kuma idonta ya rufe, cikin duhun idanunta na haska mata sunan Muhammad Turaki da ke jikin farar takardar nan da babu zanen komai ajikinta sai na sunansa. "tashi muje Maijidda". "zuwa ina?". "ina wannan baƙar ledar da na baki ranar bikin gimbiya Safiyya?". "tana ɗakin Yami". "je ki ɗaukota da sauri. ki sameni a bayan tanki cikin lambu, ki taho da ashana dalon Allah". _till we meet in the next page! Your Comment will make me to continue or stop._ *dont forget to vote, react and share to other groups please🙏* [8/6, 18:33] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya *3* *Dare, 20:45pm.* Ƙafafun Hajiya Madina suka shigo cikin ƙaton parlon, wanda ƙamshinsa ya haɗe da sanyin acn da ke hurawa ya haɗu ya bada wani sanyin ƙamshi me motsa zuciya. Jikinta sanye da ash abaya wadda taji adon stones ajiki, ƙyallin stones ɗin sai wurgawa suke ta cikin hasken fitilun parlon. Ganin Ƴaƴanta ya saka ta sakin murmushin da bata shirya masa ba, tana ƙaunar yaran fiye da yanda take son kanta, kowa yasan da hakan, abu ne ma da kamar tayi tambarinsa a goshinta. Tana tsaye daga bayansu tana ƙare musu kallo cike da so da ƙauna, su kuma hankalinsu ya tattara kan tab ɗin da ke kan cinyar Sameer su na kallon pixx ɗin da su kai ɗazu na birthday ɗin Turaki. Gyaran muryar da tayi ne ya ankarar da su zuwanta, suka ɗago a tare su na kallonta fuskokinsu na washewa da murmushi. Ta zauna a kujerar da ke fuskantarsu tana faɗin,"shi ne aka kasa jira nazo, wannan cin amanar har ina?". Tayi maganar da sigar wasa kamar wadda ke tare da ƙawayenta. Samha ta ɗauko tab ɗin ta nufo wurinta tana faɗin,"Maama kinga wanda aka maku ke da Hammah duk yafi kyau wallahi". ta zauna kusa da ita tana nuna mata hoton da aka ɗauka a sanda Turaki ke saka mata cake a baki. Allah ɗaya yasan me taji cikin zuciyarta a wannan lokacin, dan shi kansa murmushin da ya suɓuce a leɓenta bata san da zuwansa ba. Ta kai hannu ta shafa hoton, ƙwayar idanuwanta na haskawa da ƙyallin wata ƙauna da ke tsakanin Uwa da Ɗa wanda Ubangiji kaɗai ya san girmanta. "gaskiya munyi kyau, kamar ban haifi Hammah ba, kalle ni wata ƴar suwet a kusa da shi. Wannan idan sirikata ta gani ai sai tayi jealous idan bata san wacece ni ba". Ta faɗi hakan cike da raha, haƙoran makkan da ke bakinta guda biyu su na bayyana duka a waje. Taci gaba da scrolling har tazo kan wanda su kai gaba ɗayansu,"kai amma wannan ma yay kyau. 1 Family na Baffa kenan". San da tazo kan wanda Turaki yake shi kaɗai ta ƙara cewa,"wannan kam shima enlargement ɗinsa zan bada a ƙara min, Hammah yayi kyau sosai kamar wani magidanci". Sameer yace,"Maama wai duk sai kin cika bangon ɗakinki da parlonki da hoton Hammah ne?". "ƙila hakan ce zata kasance, dan sai dai idan bai yi sabon hoto shi ɗaya ba". Sai da suka zo ƙarshe a kallon hotunan sannan ta ƙara cewa,"gaskiya Hammah ya dawo ya fito min da matar aure, dan na ƙagu naga sirikata". nan dukansu suka haɗa baki wurin faɗin,"aiko dai Maama ya kamata ace Hammah yayi aure, sai tsofewa yake yi". Kallon da tayi musu ne yasa babu shiri suka gimtse bakinsu, saboda kalmar tsufa da suka jinginata da Turaki. "Hajjah nyamdu mae henyi". (Hajiya abinci ya kammala). Mai aikin da ta ƙaraso wurin a yanzu ta faɗa sanda take tsugunawa a gefen hannun kujerar da Hajiya Madina ke zaune. Ba tare da ta juyo ta dubeta tace,"usema be habdugo". (sunnu da ƙoƙari) "aha Hajiya Miyetti". (yauwa Hajiya na gode) Daga haka ta miƙe ta bar wajen cikin azama dan barin musu wajen. Hajiya Madina ta ɗauke tab ɗin daga kan cinyarta tana ajeta kusa da ita, sannan ta kalla ƴaƴan nata tace da su,"my bloved ones dinner is ready". Tare suka miƙa kaf ɗinsu suka nufa dining area, warm coolers na abinci ne zafafa masu kuɗin gaske, an jere akan dining table ɗin wajen kala shidda, kowanne cooler da kalan abinci da ke ɗauke acikinta, ta yanda kowa idan zai ci abincin zai ci favorite nasa ne. Zaytuna ta buɗe flask ɗin da ke ɗauke da Mandi rice ta zuba a plate ta miƙa shi gaban Hajiya Madina, sannan kowa ya shiga zuba nasa abincin. Tunda suka fara ci babu wanda yay magana sai ƙarar cokula da kake ji har su ka kammala, wanda Hajiya Madina ce ta fara gamawa, ta yagi tissue ta goge bakinta. "albishirinku". Ta faɗa tana jefa tissue ɗin cikin durstbin. "goro Maama". Suka faɗa bakunansu a haɗe. "this time Baffa yayi suprising namu, mo don dow lawol vartugo". (yana kan hanyarsa ta dawowa). "na jam kam?". (amma dai Lafiya ko?) "jam saliiman, mo vii mo yenwi Muhammad mako tan". (Lafiya lau. Kawai yace yana kewar ganin Muhammad ɗinsa ne) "daɗin biyu kenan, to Baba ma yiidama to Dada ma kam yiidima". (Idan Babanka baya sonka to Mamarka na sonka). Muryar Khalil da ke shigowa cikin parlon a yanzu ta amsa lokacin da shima yake jan kujerar dining zai zauna. Idon Hajiya Madina ya maƙale akansa tana cewa,"dume a tammi". (me kake nufi?) Khalil yay murmushi kamin yace,"banda nuna launiyar warin fata kawai Baffa sai ya dawo gida saboda mutum guda, hala mu dama ya manta ya haifemu?". Maganar yake cike da zolaya. Hajiya Madina tayi murmushi kaɗan tace,"me yasa baka yi zuciya kazo a na farkon ba?". Shima yana murmushin yace,"to yanzu dai ba sai ya dawo ba ya tarar Hamman baya nan. Dole dai ni zai gani ai". "Jealosy". Ta faɗa tana binsa da wani kallo. A rayuwar Hajiya Madina babu abin da take so irin ta ganta cikin ƴaƴanta, kuma kowanne cikin farin ciki da jin daɗi ba a cikin damuwa ba. Suna cikin tattaunawa akan batun gobarar da ta kama ɗazu wajen ɓangaren Lambun gidan, take basu labarin aima har an sallami me gadin wajen, saboda sakaki da yake akan aikinsa. Inda dukansu suka ce hakan yayi daidai, duba da ko lokacin da aka zo wajen bama ya cikin gida gaba ɗaya, baima san da kamawar wutar ba, balle yasan abin da ya haddasa kamawarta. Wata matashiyar budurwa baƙa ta faɗo parlon cikin sauri me
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243