Chapter 130
Chapter 130
shiga nuna mata su Nihal tana faɗa mata sunayensu, tai mata nuni da Ilham dake gefe ɗaya ta rakuɓe sai kallonsu take tana murmushi. tace,"ga inlaw ɗinmu can". Mum tace,"really?". Maama tace,"ga zahiri na kunya nan kina gani". ai nan da ko Mum ta buɗe mata hannu tace ta taho gareta, ta rungumeta da tsananin farinciki sai saka mata albarka take yi. kuma sai a lokacin Mama ta lura da rashin Zaytuna, sai ta miƙe tana dube dube dan dama tuni ta san da ƙullatar da Zaytuna tayi da Mum. ta ganta tsaye can gefe ta haɗe rai fuskarta a gefe ɗaya, ranta ya ɓaci sosai taji tama kasa magana, hakan ne yasa Hajiya Ramla fahimtar komai musamman da ta ɗaga ido ta kalli photocopy ɗinta, ba sai an faɗa mata ba ai tana kallonta tasan itace jaririyarta da ta tafi ta bari. Turaki ma ya dinƙa kallon Zaytuna yana tuna lokuta da dama da take ce masa,"ka daina damuwa da ita Hammah tunda ai itama bata damu da mu, ni fa Hammah Allah ko ace ta dawo inda take ba zan kalla ba balle na raɓeta". sai kawai ya miƙe ya nufi wajenta, yana jin Maama cikin muryar ɓacin rai tana cewa,"wannan ba itace tarbiyar da na baki ba Zaytuna, kuma ko ki ɗago ƙafa kizo mahaifiyarki tasa miki albarka ko kuma wallahi in ƙaraso nan inyi miki duk abinda zuciyata ta sani, dan ba ki isa ki lalata mana farin cikin da muke ciki ba". Tayi shiru a sanda Turaki yaje gaban Zaytuna ɗin ya kamo hannunta, har ta cije tana neman ƙwacewa, ban san me ya faɗa mata a kunne ba yasa ta biyo shi. suna zuwa gaban Mum Turaki ya zube duka gwiwoyinsa a ƙasa, yaja hannun Zaytuna da ta tsaya ƙiƙam itama ta zube nata gwiwoyin, dama wannan ranar ya daɗe yana jira, dama wannan lokacin yake ta jira, dan haka kawai sai ya haɗe hannayensa duka biyu alamun neman yafiya cikin amon sauti me mugun ban tausayi yace,"Mum dan Allah dan Annabi ki yafe mana, ki yafe min dan girman Allah, wallahi tallahi ban san ta yacca akayi wutar ta kama ba, da sanina ba zan haddasa gobara ba Mum kema kin san banda fitina, amma ina neman yafiyarka dan Allah Mum". yay maganar hawaye na sakko masa hoton komai na wancan lokacin na haska masa musamman a sanda yabi Mum ta hankaɗo shi ta rufe ƙofa ta tafi ta barsu. Hajiya Ramla ta fashe da kuka, kukan da ya tafi ya shiga kunnuwansu ya daki zuciyar Turaki da Zaytuna, suka yi saurin ɗago ido suna kallonta, a ɗazu zai faɗi duk wani saukar hawayenta da sunan hawayen farin ciki, amma wannan kukan da ta kasa riƙe ƙarfin sautinsa na shaida masa so take ta yishi iyakar gwargwado, ta yanda zata samu ta rage raɗaɗi da baƙin cikin wani abu dake ranta. to me ya kawo hakan?, shi da yayi mata laifi. kuma kafin ya gama karantar dattin baƙin cikin dake saman fuskarta sai yaga ta sauko daga kan kujerar, itama ta zube nata gwiwon a ƙasa ta rungumo su jikinta tsam. tana kukan sosai tana faɗin,"Babana babu abinda ka yi min, baka min laifin komai ba Babana. ni ce nayi muku laifi wanda har ba zan yafewa kaina ba sai in kun yafe min, dan Allah, dan Annabi Babana kai da Zaytuna ina baku haƙuri, ina roƙonku ku yafe min da nisanta daga gareku da nayi, sharrin shaiɗan ne". Zaytuna ta fashe da kuka tana shigewa jikin Mum ɗin sosai, cikin muryar kuka suka haɗe baki ita da Turaki suka ce,"Mum ke fa Uwa ce akan me za kike neman yafiyarmu bayan baki yi mana komai ba. to ma idan kinyi ɗin menene ai girmanki ne da cancantarki, balle ma har duniya ta naɗe ba za ki taɓa yi mana abinda zamu kallesa a matsayin kin mana laifi ba". furucin nasu sai ya zama kamar haɗin baki ko kuma tun can dama sun tsara hakan. sukai shiru suna barin jikinta, Turaki yasa hannunsa na hagu a gefen fuskarta ta ɓarin da yake, itama Zaytuna haka. suka ƙara haɗa baki da faɗin,"muna miki tsananin so, farin cikinki shi ne muce mun yafe ko?, to mun yafe miki Jarumar mata". sukai kissing nata a goshi suna jin wani irin shauƙi na daban da basu taɓa jinsa ba mara misaltuwa na bin jinin jikinsu. gaba ɗayansu kuma har Mum ɗin sai suka saki murmushi me faɗi, har haƙoransu duka na bayyana a waje. Hajiya Madina da su Neehal sai suka koma ƴan kallo, dukkansu sai murmushi suke yi, kuma har sannan Hajiya Madina bata bari Baffa ya sani ba saboda sanin irin fushin da yake da Hajiya Ramla, ta bari ne kawai sai dai ya gansu a gida. Zaytuna taƙi sakin mahaifiyartata tace,"Mum yau a jikinki nake so na kwana, yau ba zanyi bacci ba Mum zan zauna inta kallonki". suka riƙo hannunta ta miƙe ta koma kan kujerar ta zauna, sannan ne ta kalli Hajiya Madina da zolaya tace,"Madam kisa ƴaƴanki su sakeni in tafi wurin sabuwar ƴar da nayi". aiko karaf Neehal tace,"ki tafi ina Mum?". ta faɗa tana turo baki tai saurin zagayowa ta zauna kusa da ita tana kama hannunta da cewar,"ai mu daga yau kina manne wajenmu kuma". bata bar murmushi ba tace,"to zanje in duba patients ɗina, a ban izini dan Allah". Kusan duk a tare suka haɗa baki wajen faɗin,"patient kuma Mum?". tana kallon Hajiya Madina tace,"wata yarinya ce da ta taimaka min muka fito daga cikin jeji mota ta bigeta, tun ɗazu munfi 1hour amma shiru, tace min ƴar aikin gidanmu ce, dan tunda ta ganni ma take cewa muna kama da Zaytun". a lokacinne kuma sai ga Fillo nan tazo wajen kamar tasan zancenta akeyi, tana riƙe da hannun Ummi ta ƙaraso da kumburarriyar fuskarta da taƙi barin murmushi. ta saki hannun Ummi ta nufi wajen Hajiya Madina wacca ta buɗe mata hannu, ta shige jikin Hajiya Madina ita kuma tana rungumeta tare da faɗin,"hasken gidan Alƙali Dikko, haƙiƙa ke ɗin haske ce a tare damu Fillo". Fillo tace,"Maama nima ga Ummina na gani, ashe bata mutu ba". ta saketa tana faɗin,"haba dai". tabi Ummi da kallo kafin ta isa wajenta da sauri tana gaisheta suna yiwa juna barka da farin cikin da suka tsinci kansu a ranar yau. Turaki dai sai yabi Fillo da kallo, ba wai ya manta da ita bane, tun ɗazu hankalinsa na kanta, kawai dai ba zai iya barin Mum bane, amma Allah Allah yake yaga Dr Yusuf yazo wajen. ji yake kamar yaje ya sunkuceta ya ɗauketa ya kaita inda zai zama daga shi sai ita, silent place ɗin da ba za'aji sautin komai ba sai na dariyarta, dan tabbas zai ƙara yalwata wannan annurin da yake gani shimfiɗe a saman fuskarta. zai ajiyeta akan cinyarsa yayi mata godiya da irin salon da ba'a taɓa yiwa wani mahaluƙi shi ba duk girman matsayinsa da mulkinsa kuwa. Mum ta dubeta tace,"zo nan ƴata". Fillo ta isa wurinta zata tsuguna tace,"a'a zo nan". ta faɗa tana yi mata nuni da kusa da ita, yayinda take kallon Turaki tana cewa,"Babana matsa". Turaki ya matsa Fillo ta zauna, Mum na kama fuskarta tace,"how are you
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243