Chapter 67
Chapter 67
mata kamar ba zata iya komai ba, tana jin yanda idanuwanta ke faɗa mata kamar ba ita ta haifi ƴaƴan dake zaune a gabanta ba, tana jin yacca ƙwaƙwalwarta ke faɗa mata rayuwar Turaki ita tafi cancanta da ta ingata sama da ta sauran, cikin kanta na lissafa mata kamar yanda take jin bata da kowa a duniyarta sai Turaki, haka shima Turaki ke jin ba shi da kowa a duniyarsa sai ita, ita ɗaya jallin jal. ƙwayar idonta ta wulƙita ta kalli Zaytuna, sannan ta kalli Nihal, tukunna ta sauka akan Samha, duka Yaran suna daga kan gadonta ne suna hira cike da soyayyar junansu. Samha kawai take iya gani a lokacin, kallon yarinyar take da irin kallon da ita kaɗai tasan ma'anarsa, ta kuma san manufarsa, ta kuma san lissafin da ƙwayar idonta ke yi akan yarinyar, ta kuma san ciwon da kallon nata ke hifarwa da ƙwayar idonta. da ace zata iya, tabbas da tace komai ɗin da take ji take gani ƙarya ne, to amma bata isa ba, bata isa ta kira abubuwan da tasan suna tafiya ba a matsayin ƙarya, ita gaskiya take bi, kuma gaskiyar ta sani, kuma gaskiyar zata bi. sanda ta rufe idonta tana sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya, sannan ne wayarta dake kan cinyarta tayi ƙara, ta ɗaga tana kallon screen ɗin da sunan THE BEST ke yawo ajiki. lokaci ɗaya taji duk wani ɗaci da ɓacin ranta ya gushe, tana jin wani ɓari na damuwar da take ciki ya yaye, fuskarta ta bayyana jin daɗin ganin kiran nasa, sai ta ɗaga tana faɗin. "Me Babban suna kana ina?, ina ta kiran wayanka baka ɗauka ba, na kira Bello yace bakwa tare, ina ka tafi?, Khalil yace baka je office ba yau, ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya, duk inda kake ka dawo gida yanzu kaji, ina nan na kasa samun nutsuwa tun kiran farko da nayi maka ban samu ba, yau na kiraka yafi sau goma kiran baka picking, tukunna dai kayi lunch?". maganar take muryarta na bayyana tsananin damuwar dake ƙunshe a cikin ranta, ba don komai sai dan rashin sanin halin da yake ciki tun safe da ya bar gida. haka take ita, indai ya fita a gida basa 1hour basu yi waya ba taji ya lafiyarsa, idan kuma yana gida to jiddan walahairan yana part ɗinta, suna tare ko a parlo ko kuma a bedroom ɗinta, sai dai idan ranar yana jin miskilancinsa har da ita to sai dai ita ta bisa part ɗinsu. ta kan tsokane shi da cewa,"Hamman'su kana juya ni kamar waina a tanda". Fillo da ke tsaye tana sauraren maganar Hajiya Madina, tausayin matar yay bala'in kamata, sai ta kasa yin ko da motsi, tai shiru ta kasa yin magana, tabi inda Turaki yake yashe kawai tana kallonsa, me yake faruwa da rayuwarsa ne?, me zata faɗawa Hajiya Madina yanzu?, ya zata yi idan taji a halin da ɗanta yake ciki?. sai ta tuno yacca Hajiya Madina ta shiga tsananin tashin hankali a wata rana da ya yanke da wuƙa yana yanka lemu, ta dinga kuka akan ɗan jinin da ya zuba daga jikinsa, ta tuna yanda Hajiya Madina ta koma bata iya nutsuwar minti ɗaya babu Turaki a kusa da ita a lokacin, ta tuna yacca duk bugawar sakan, duk wani motsi nasa sai tace,"menene me Babban suna?, me kake so?, me zan maka?, ciwon yana zafi?, sannu kaji, Allah ya baka lafiya". haka ta dinƙa ririta shi kamar jariri sabuwar haihuwa a lokacin. sai Fillo taji inaa ba zata taɓa iya kasassaɓar sanarwa da Hajiya Madina halin da Turaki yake ciki ba a yanzu, ba zata iya ba har ga Allah, bata son taga uwa ta shiga tashin hankali, balle kuma Uwa irin wannan da lokaci ɗaya take fita daga hayyacinta akan ɗan da ta ƙwallafa rai akansa duk kuwa da tana da wasu Ƴaƴan da Allah ya bata. Hajiya Madina ta rufe ido ta buɗe tana kallon agogo, ƙarfe biyar na yamma, yau watarana ce da ta kafa tarihi a tsakaninta da Turaki, rana ta farko da Turaki ya saɓa umarninta a iyaka tsayin rayuwarsa, to amma me yasa?. sai kawai ta rufe ido ta ƙara buɗewa tana sauke ganinta a daidai lokacin da agogo ya nuna biyar harda minti ɗaya, sai taji ranta ya ɓaci. kuma cikin nuna ɓacin ran tace,"baka taso a stubborn ba, kuma duk cikin ku shida kai nafi karewa daga duk abinda zai sa ka zama stubborn, amma me yasa sai daka girma?, kana so ka zama Stubborn kamar Khalil ko?. saboda nace duk sanda ka fita ya zama kuna tare da shi ko ina zaka je, ba wai ina nufin ka zama mara ji ba kamarsa, na sani da takurawa ace lallai duk inda zaka je sai da ƙaninka alhalin ka mallaki hankalin kanka, amma ka sani ni uwa ce da ba zan so wani abu ya cutar da ɗana ba, ya kamata ka tuna da akwai masu faraurar rayuwarka a kullum, dalilin da yasa nace duk sanda ka fita ya zam kana tare da Khalil ko Bello duk da nasan dabarata bata isa ta hana faruwar abunda Allah ya shirya ba. amma dai atleast kasancewarka tare da wani zai sa suke tsoron tunkararka. kuma sai da kayi min alƙawarin ba zaka saɓa umarnina ba akan hakan ba, Me Babban suna me yasa yau rana ta farko ka saɓa umarnina?, Khalil yace ko minti 2 baka yi a office ba ka fita, Bello yace kana ɗaukosa a airport kuka rabu. ina ka tafi tun bayan rabuwarku?, me yasa baka dawo gida kaci abincin rana ba?, me yasa kaƙi ɗaga wayata?, me yasa kake son haddasa ciwona ya tashi?, me yasa tun ɗazu ina maka magana kayi min shiru?, rashin maganar na menene?, lafiya?". tunani da lissafi dake a cikin kan Fillo ya tarwatse, gabanta yay dukan tara-tara, kallon Turaki take yi tana tuna irin tarin tasa soyayyar wa mahaifiyarsa, zuciyarta na faɗa mata taje ta same shi ta faɗa masa Maama ce, Maama na son yin magana da shi, zai farka idan yaji hakan, tabbas zai farka. ta isa gabansa tana jijjigasa a hankali daidai kunnensa tana faɗin,"ka tashi ga Maama". a zatonta ko jin hakan zai sa ya farka daga dogon suman da yayi, amma inaa kamar ma da gawa take magana. sai kawai wani kuka ya kubce mata. cikin kiɗima Hajiya Madina tace,"innalillaihi wa'inna ilaihi raji'un...". ko salatin bata ƙarasa ba Fillo tace,"Maama ki zo". ta faɗa tana kuka sosai. daga ɓangaren Hajiya Madina ta zabura ta miƙe daga kan kujera, cikin gigita da tsananin tashin hankali na farat ɗaya, me kunnenta yake ji ne?, kamar kukan wani take ji kuma kamar ana so ace mata tazo ga Turaki babu lafiya. "waye ke magana?, ina Muhammad ɗin?, ke wacece?". kukan Fillo ya ƙaru tace,"Maama ni ce, Hammah ɗin ya faɗi ya suma Maama kizo da sauri". wayar dake hannun Hajiya Madina ta nemi ta faɗi a ƙasa, Samha da idonta ya kai wurin tai saurin taro wayar sanda ta sauka daga saman gadon. ta taro wayar a lokacin da itama Hajiya Madina ke neman faɗuwa, Nihal tai saurin riƙota. Samha tace,"Lafiya Maama, menene?". Hajiya Madina ta kalleta ido a waje, a hankali
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243