Chapter 123
Chapter 123
Fillo tace,"kidnappers ne suka ɗauke ni". Hajiya Ramla tace,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yi haƙuri ki daure ki tashi muje kinje, kin san hanyar da zamu bi muje asibiti?, domin kina da buƙatar ganin likita ƴata". Kuka ya kubcewa Fillo tace,"Mum ai ba zan gane hanya ba, ban san nan ɗin ina bane dare yayi sosai". Hajiya Ramla tace,"kamar kin ban waya ɗazu ko?". kai kawai Fillo ta iya ɗagawa dan ƙarfinta ya ƙare bata jin akwai sauran yawu da ya rage a bakinta da zata yi magana. tasa hannu a rigarta ta zaro wayar Hajiya Ramla ta karɓa, ta danna 0 tana ƙoƙarin tuna lambar Baffa ko ta Maama amma sai taji ta kasa, tai ta trying taji ba zata iya rubuta duk wata lamba da taɓa sani ba". tace,"ƴata na mance lambar kowa da na sa ni, amma naji kina ta ce min Babana da Zaytuna banji kina min maganar Madina da Khalil ba, dan Allah suna ina?". Fillo ta kasa magana kwata-kwata. Hajiya Ramla ta yunƙura ta miƙe tare da kamo hannunta tace,"yi haƙuri ki daure mu bar wajen nan, idan muka isa titi Allah zai kawo mana mafita". Fillo ta ɗaga kanta kawai. "mu nufi gabas insha'Allahu sa'a ce zata fitar da mu". Fillo ta daure da ɗan sauran kuzarin da ta-ke da shi suka ci gaba da gudu, sanda suka fara hango titi dai-dai lokacin ne kuma mota ta shigo layin da wani mahaukacin gudu irin tuƙin ƴan wiwi, tsoro yasa su kasa kaucewa gaban motar, haka ma Aliyu dake driving rikicewa yasa shi rasa yanda zaiyi, ganin motar tayo kansu gadangadan babu ta yanda zasu kuɓuta Fillo ta ture Hajiya Ramla daga kusa da ita, dai-dai lokacin kuma Aliyu yabi ta kan Fillo ta gangara gefe ɗaya. cikin tsananin tashin hankali, ɗimauta da gigita Hajiya Ramla ta ƙwala ihu tana ɗora hannu akanta ta kurma salati, kafin tayi kan Fillo a guje tana ɗagota zuwa jikinta, ganin uban jinin dake zuba yasa ta fashewa da matsanancin kuka tana ƙara ambaton innalillahi. Aliyu ya fito daga mota a hargitse yana furta,"innalillahi wa'inna ilahi raji'un". Inna Wuro ma ta fito daga bayan motar ta taho da sauri tana faɗin,"shikenan ka shiga uku kai ɗaya Aliyu dan ban dani wallahi, yanzu ai kaga amfani jin maganata ni da kake ɗauka a watse, tuƙin mutuwar da nake hanaka kana maida ni gantalalla kana ƙara wani akai ga shi nan yau yaja maka masifa ka bige aljanu". tayo wajen da Aliyu ke tsaye ya rasa abinyi, jinin dake zuba jikin Fillo ya rikitar da shi tashin hankalinsa ɗaya kar ace ya kashe rai. ya zaro wayarsa a aljihu ya kira wayar Ammi, tana ɗagawa cikin dauriya da ƙarfin hali irin namiji yace,"Ammi ki fito na kaɗe wata yarinya, kuma kamar ta mutu Ammi". Hajiya Ramla kuwa sai kuka take yi tana jijjiga Fillo akan ta tashi, Inna Wuro ta ƙaraso wajen da Hajiya Ramla ke zube a ƙasa da Fillo akan cinyarta, ta tsaya daga ɗan baya tace,"bayin Allah aljanu kuyi haƙuri dan Allah, ni wallahi babu ruwana, saukata kenan daga saudiya ko awa ɗaya banyi ba, aka tura wannan gantalallan yaron yaje ɗauko ni, alhalin tuntuni na faɗawa ubansa ya daina aika shi taho da ni tunda baida hankali, to da yake dai nayi rashin sa'ar haihuwar ɗa me jin maganata sai ta ƴaƴansa, in gaya miki sarauniyar aljanu tun daga iya fat Aliyu yake fafara wannan tuƙin mutuwar da ni, ina ta roƙarsa Allah Annabi ya tsaya yaƙi tsayawa saurarena saima ƙara wani da yake yi, yanzun ma ina ta ce masa zai buge mutane yaƙi jina ashe da rabon manyan zai shafce, rashin jin maganata yasa ya buge ƴar sarkin aljanu dan ba tsautsayi bane yana sane, dan haka wallahi kuyi masa duk abunda kuga dama baida kirki ko kaɗan, ko ƙafarsa ce ma ku shanye ta yanda zai daina tuƙa motar, kuyi haƙuri aljanu ni dai banda laifin komai Aliyu ne ku kumbura masa ciki wallahi tunda ya kashe muku ƴarku". duk wannan maganar da take idonta rufe yake, sai yanzu ta ɗan buɗe ɗayan kaɗan tana kallon Mum, ita tsakaninta da Allah ta-ke maganarta aljanu suka bige, saboda yanda taga yalwataccen gashin Mum har kusa da ɗawawu, ga shi duk da uban dafewar da tayi hakan bai sa tsananin hasken fatar da ta-ke da shi ya dusashe duka ba, hakanne ya ƙara tsorata sosai ta-ke zaton aljanu ne musamman da taga dare ne yanzu, mai lafiya dai ba zai fito a yanda suke ɗin nan ba duka babu ɗankwali gasu a hargitse kamar sababbun kamu. ta durƙusa a ƙasa tana yin alamar roƙo tace,"me girma aljana kiyi haƙuri ki daina tunanin yanke hukunci da ni, ki sunkuci ƴarki ku ɓace kuyi nahiyarku dan Allah. idan kuma ba za ki haƙura ba wallahi na goyi da bayanki kici uban Aliyu dan ko kaɗan baida mutumci, ga gidansu can ubansu shine ɗana ni na haife shi da cikina, amma ba kiga yanda ake wulaƙanta ni ba a gidan, matansa biyu ɗaya me mutunci ɗaya watsatstsiya, amma duk su ɗin sai suka haifi gantalallun yara ba kiga yanda suke bani wahala ba wallahi har kuka sai kin yi min idan kinga a yanda nake zaune a gidan, ni kuma kamar mayya na kasa barin gidan saboda duk cikin yarana gidan Amadu ne kaɗai kullum ake shan shayi da ƙwai da naman ganda da safe, sauran gidajen ƴaƴan ko daga ɗumame sai koko babu ko sikari aciki, to ba zan mutu a wahala ba na dawo gidan Amadu ake ban kayan daɗi ana gani min azaba". Mum ta ɗago jajayen idonta tana kallon Inna Wuro, hakan yasa Inna Wuro zabura taga da baya tana faɗin,"wa'innahu min sulaimana wa'innahu bissimillahir Rahmanir Rahim". Mum na kuka sosai tace,"yanzu ba zaku taimaka min ba sai na rasa ƴata?". Inna Wuro na adu'a a bakinta tace,"ku kuwa kuna da taurin kai mutanen ɓoye, kawai kiyi siddabarunku ta tashi shine har sai anje asibiti salon dai aja kuɗin ɗana Amadu, kuma na faɗa miki indai Aliyu ne ku tafi da shi can nahiyar taku kawai kuci ubansa wallahi, ƴaƴan Amadu da yawa ba shi ɗaya ya haifa ba". Mum na kuka ta kalli Aliyu da duk yake a ruɗe, shima tsoron ya fara kama shi yana ganin kamar ta bakin Inna Wuro aljanun ne. adu'a kawai yake yana ƙara kiran wayar Mum da bata ɗagawa, Hajiya Ramla ta miƙe ta sunkuci Fillo da ƙyar zata goyata a lokacin ne Daddy da Ammi da me gadi suka iso wajen cike da tashin hankali. Aliyu yace,"ban san garin ya ba Daddy, nayi ƙoƙarin ƙwacewa na kasa". Daddy ya ɗago yayi masa wani kallo, sannan ya doka masa uwar tsawa yace,"dan uwarka baka da hankalin da zaka iya ɗaukarsu zuwa asibiti ne da har sai ka kira?, ko baka ga jinin dake zuba daga jikin yarinyar bane shashashan banza, comon zo karɓeta ku sata cikin mota". Aliyu ya taho cikin mutuwar jiki suka kama Fillo shi da me gadi suka saka a mota. cikin hanzari Daddy ya shiga driver seat sannan Ammi ma ta shiga gaban motar, Aliyu da Mum kuma sauka zauna da Fillo a baya, Daddy nata bawa Mum ɗin haƙuri, Ammi dai ta kasa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243