Chapter 231
Chapter 231
Fillo yay sanyi tana me tunawa da halin da suka riski Fulani Azima a shekaranjiya da suka je dubata. cikin sanyin murya tace,"Allah ubangiji ya bata lafiya, ko in je in shiryo mu tafi tare?". "a'a ke da kike fama da kan ki, na faɗa miki bana fidda ran ba za ki haihu ba a yau, ƙila ma sai dai ai min waya ace Baby ya sauka. ɗa zu da asuba ai ina tayi miki dariya ta window". Fillo ma tayi dariyar ta ce,"hmmm aikin mijinki ne, haka kawai duk ya jigatar da ni da safa da marwa, ke kinji yanda ƙafafuna ke ciwo kuwa. ai ana kaiwa gobe sai dai kuga na kai kaina asibiti sun yanka ni sun ciro muku yaran ku". "da kanki ma za ki haihu insha'Allah, bari na tafi sai na dawo". "to a dawo lafiya, ki yiwa Mamin sannu don Allah". motar Ilham ta bar compound ɗin gidan, ita kuma Fillo ta shige part ɗin ta. a ɗaki ta sami Turaki zaune yana rubutu a takarda, tun safe yake aikin rubuce rubucen office, tayi wurgi da hijab ɗin jikinta akan gado, kafin ta nemi waje ta zauna ta miƙe ƙafafu. "Jannaty please come and massage my legs, Allah ciwo suke min sosai". ya ɗago ya ɗora idanuwansa akanta, matuƙar tausayinta ya kama shi, in ace yana da ikon da zai fito mata da Babies ɗin nan babu abin da zai yi masa shamaki da hakan, ya ƙagu ta haihu haka ko don ta huta. ya tattara takardun a gefe tukunna ya taso, kafin ya zauna a gabanta ta dakatar da shi da faɗin,"sorry ba ni riyon kayan su Maama". ya ce,"me kuma za kiyi da shi?". tayi masa wani kallo kafin tace,"kaji min mutum, me ake yi da gyara?, yau tun tashina ban gyara musu ba". sai yay zamansa kawai, ta ɓata rai tana faɗin,"zan yi maka kuka". ta faɗa a shagwaɓe. ya ɗago ido ya kalleta, sarai ya san zata aikata hakan, don haka ya miƙe yaje ya ɗauko ƙaton riyon da ke ɗauke da uban kayan Babies a ciki, ya ajiye zai zauna ta ƙara dakatar da shi. "diary ɗi na". ya rufe ido tare da karyar da kai, zai yi magana tayi kalar tausayi tana haɗa hannayenta ta ce,"yi haƙuri Baban Ƴan biyu, ai don Allah nace". sai da ya lakuce mata kumatu kafin ya fita ya bar ɗakinsa zuwa nata ɗakin, san da ya dawo tana waya da Boɗejo wacca ta kira tana tambayar lafiyar jikin nata. ya zauna kawai ya shiga matsa mata ƙafafun, yana tsokanarta da lukutar gombe, bayan sun gama wayar da Boɗejo ta harare shi tare da fizgar diary ɗin tace,"ka duba min sirrina ko?". "oho ke kika sani, ni me zan duba acikin diary ɗin da ake ɓoyewa kamar ana ƙulla munafurci a cikinsa, to ta ina ma zan iya gane watsaltsalun rubutun lukutar Gombe?, rubutun da ba iyawa aka yi ba". dariya tasa Fillo dakatawa daga rubutun data fara,"oho dai duk abin mutum ba zai ga me ke ciki ba, ah tou! sirinmu ne ni da ƴaƴana" "sirri ko munafurci?, yara tun basu zo duniya ba an fara koya musu hali mara kyau, ni dai gaskiya nake faɗa miki ki sauya hali, wannan ba halin zama mother ba ne". ta ƙara yin dariya,"magana ce bata isheka ba sarkin ƴan sa ido, sirrin uwa da ƴaƴa ne dai ba zaka gani ba". ta faɗa tana yi masa gwalo, sai ya sakar mata ƙafa suka shiga kokawa akan sai ya karɓi diary ɗin, ta ƙwalla ƙara babu shiri ya ƙyaleta yana aikin zaro ido da jera mata tambayoyi a hargitse. "menene ya faru Angel?, na bige miki wani wajen ne?". ta kashe masa ido ɗaya da cewa,"kasan idan baka daina takura min ba zan kaiwa Ilham jinginar ka, ka kwana dubu saba'in baka ganni ba". "Allah ya baki haƙuri yallaɓiya ranki shi daɗe me girma uwar gida, da ki hora ni da rashin ganinki ai gwara ki zane min ɗuwawu na kasa zama, rashin ganinki ai azaba ne a gare ni". "idan na mutu fa?". sai ya ɗago yana kallon fuskarta da ta ƙara kyau yace,"ban hana ki yi min zancen mutuwa akan ki ba". "Allah ya baka haƙuri ranka ya daɗe". ta faɗa da murmushi a fuskarta. bayan ta gama gyaran kayan Babies ɗin take ba shi labarin irin satar kayan da akayi ranar zaman sadaƙar bakwai ɗin Hajiya Madina. "Daddyn Maama ka san me?, ina sabon less ɗin da na ɗauki zaninsa nace za'a ɗinkawa little Maama riga da shi?, to wallahi har da shi aka ɗauke, daga in ɗauko in ajiye kan gadon Mum in shiga toilet, ai kuwa na jera Allah ya isa babu adadi, saboda les ɗin nan Maama na sonsa". yace,"Allah ya kyauta, rashin tsoron Allah ne duk yake saka sata a gidan mutuwa, Allah ya shirya masu yi kawai". ta amsa da amin kafin ya kamata ta yunƙura su miƙe tare, toilet suka shiga domin yin wanka, acikin banɗakin sai da aka ɓata tsawon awa guda ana shan soyayya, sannan suka fito suna dariya, ita tana faɗin idan ya ɗauketa a yanda take yanzu ƙasusuwansa duk sai sun ɓalle, yayin da shi kuma ke faɗin ya sani, hannun lukutar gombe tsaf zai ɓalla shi ya ɓalle gaba ɗayansa.. kamar kullum yauma suka shirya kansu, ita ta saka wata ƙatuwar bubu da ta ɗauka acikin kayan Maama, kuma rigar sai tayi mata kyau sosai, saboda girman cikin jikinta sai awon yayi daidai da ita. "amma dai ba zaka jima ba ko?". amon muryarta ya fito a lokacin da take ɓalle masa maɓallin rigarsa. ya ce,"No yanzu zan dawo babu jimawa, takardun nan kawai zan kaiwa Khaleel, don't be lonely, am always with you, ina cikin nan". ya faɗa yana pointing saitin zuciyarta. tayi wani kalar murmushi tana kamo fuskarsa cikin tafukan hannunta biyu ta ce,"ina sonka mijina, ina ƙaunarka". "ni ma ina yi miki tsananin so matata, Allah yayi miki albarka, yasa ki haihu da ranki da lafiyarki". "amin amin Daddyn little Maama". furuncin nata ya saka shi yin murmushi me faɗi, tare da duƙawa ya ɗage rigar jikinta ya yiwa cikin kiss, sannan ya ɗago suka yi kissing juna. da ƙyar ya iya sakinta yaje yana tattara takardun cikin sauri, ita kuma tana bashi labarin cewa,"Jannaty ka san me?". ba tare da ya juyo ba yace,"ban san may ba sai dai june". murmushin tayi sannan yace,"to ka san june?, tunda nake a rayuwarta ban taɓa hango kaina a matsayin uwa ba, ban taɓa tunanin zan ɗauki ciki ba balle har akai lokacin da zan haife shi". sai tayi shiru, yace,"ehen ina jinki lukutar Gombe". murmushi ya kasa ɗaukewa a saman fuskarta, tana kallon bayansa ta ƙara cewa,"sai ga shi Allah ya ƙadarta min ganin samun cikin, har zuwa watan haihuwarsa, zan haife ƴaƴa biyun da nagartaccen mijina ya bani su, na ƙagu in haife su Jannaty, ina tsananin son su fiye da kaina". cikin sigar zolaya yace,"har ni kin fi son su akaina?". ta ɗan taɓe baki tana kallonsa, da irin wasan da ke tsakanin mata da miji tace,"waye kai?". ya ƙaraso ya zauna kusa da ita ya mintsinin leɓenta, ya ɗora hannunsa a saman nata dake kan cikin.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243