Chapter 226
Chapter 226
komai ba sai kin kawo mata, bari na tasheta yasin tun zafin flask bai jiƙa shi ba". "no barta tayi baccinta please, abu da an kusa la'asar, lokacin sallah nayi za ki ga ta tashi". bayan wucewar mintuna goma hannayen Turaki su ka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakin, ƙafafuwansa suka shigo cikin ɗakin yayin da sanyin Ac ke ratsa shi. ƙwayar idonsa bata sauka akan kowa ba sai Maama da ke kwance kan gado tana bacci. A lokaci guda yaji jikinsa yayi wani irin sakayau tamkar an zare masa lakar jikinsa, abun da bai yi tsammani ba sai yaji yawun bakinsa ya bushe, Me ke shirin faruwa ne?. ya saki handle ƙofar da yake riƙe da shi, ya kasa ɗaga ƙafarsa yana jin wani abu ya wuce ta maƙogwaronsa, wani irin abu mai nauyin gaske, yana jin yanayin bugawar zuciyarsa na sauyawa, yana jin faɗuwar gabansa na ƙaruwa. ya san da cewa don mutum yayi bacci ba wani abu ba ne, dan bacci wani abu ne da ɗan adam ke yinsa a kowanne dare, to amma ba zai iya cewa ga ranar da Maama tayi bacci ba da rana, iyakar tsayin rayuwarsa zai iya faɗin hakan, ko da ace kuwa tana cikin halin jinya ne, baccin rana ba ya daga cikin al'amarin rayuwarta. to amma yau ɗaya, rana guda, rana ta farko kawai sai ta kwanta irin haka?, ƙarfe ɗaya da rabi na rana, har tayi irin baccin da bata ji buɗewar ƙofar tasa ba, kuma a lokacin da ya san tana zama tayi lazimin sallar azahar?. kawai sai ya ji wani abu ya motsa a ƙasan zuciyarsa, yaji kamar rauni na shirin kama shi, sai dai kamar ko da yaushe a rayuwarsa, yayi ƙoƙarin tattaro dukkan nutsuwarsa da dauriyarsa tare da dakiyarsa, ya maida ƙofar ɗakin ya rufe. "me ya sami Maama?". ya jefa tambayar ga Fillo da Nihal yana tsaye a gefe guda. "bacci take yi, aiki tayi ta gaji". "aiki!?, ina ma su aikin?". "part ɗin Baffa ne fa Hammah, ka san bata barin ƴan aiki su je can". "gajiya bata sakata baccin rana, tasha magungunanta?". "lafiyarta fa ƙalau Hammah, kawai muna zaune muna hira tace bari ta kwanta kafin ta gaban goshinta ta ƙaraso". ya shiga girgiza kansa, ƙafafunsa na ɗagawa da ƙyar, haka ɗaya Maama ba zata yi baccin rana ba, no matter what bata baccin rana, bai yarda da wannan baccin nata ba. "kar ka damu lafiyarta fa ƙalau, ban da yanayin ciwon kai da sai ka tashe ta". kunnuwan Turaki su ka tsinci muryar Fillo a cikin iskar ɗakin. ta karɓi ledojin da ke hannunsa tana ƙara faɗin,"Allah lafiyarta lau, amma idan kana ganin a tasheta ɗin to". "a ƙyaleta?". ya gyaɗa kansa kawai, sannan a hankali ya tafi zuwa gadon, da tafukan hannunsa guda biyu ya kama kan Maama ya gyara mata kwanciyar. ya zauna akan bedside drower yana kallon fuskarta, kamar tayi haske?, kamar kuma ta ƙara yin kyau?, sai yasa hannunsa a saman goshinta ya goge guntun gumin da yake ganin kamar idanuwansa na haska masa. wucewar minti ɗaya!, biyu, uku har zuwa biyar, zuciyarsa ta kasa samun natsuwa da baccinta, saboda haka sai ya kai hannunsa gefen filon, ya shiga dukan filon a hankali yana faɗin,"Maama, Maama, Maama". ya kira sunan sama da sau goma amma shiru bata buɗa idanunta ba. a yanda ya sani, duk tsananin baccin da Maamansa ke yi kiran suna ɗaya ne ya farkar da ita, balle ma ita bata da irin nauyin baccin nan, hasalima ko baccin take aka murɗa ƙofa aka shigo sai ta farka, ko kuma idan taji motsi. dan haka zai iya cewa bai san lokacin da ya miƙe daga kan drower ɗin ba. kuma maimakon zama a bakin gadon kamar yanda yayi niyya sai ya tsinci gwiwoyinsa da zubewa a ƙasa, kafin yaji wani nauyi ya ziyarci hannunsa, irin nauyin da sai da ƙyar ya iya ɗaga shi ya taɓata. "Maama". hannunsa ya sauka akan jikinta da yay sanyi, a yanzu da ya taɓata bai ga ta farka ba, haka bai ji ta motsa ba, sai yaji adadin faɗuwar gabansa ya ninku da kusan kaso tamanin da biyar. sai kawai ya tsinci kansa da shiga tashinta kamar ƙaramin yaro, babu abinda yake da buƙata a yanzu irin ta tashi, ta buɗe idonta, ta kalli cikin ƙwayar idonsa kamar yanda zai kalli tata, ta faɗa masa wannan maganar da tace zasu yi idan ya dawo, bai taɓa jin ya damu da baccinta ba irin yau, bai taɓa jin baccin wani ya tsorata shi ba irin yau, bai yarda da wannan baccin ba, bai yarda da shi ba sam. girgiza ƙafafunta kawai yake yi yana kiran,"Maama, Maama, Maama ki tashi na dawo, kin ce Papaya ta ƙare na taho miki da ita ga shi na siyo, ga takardar scaning ɗin jikokin naki ma na karɓo, su biyu ne kamar yanda kika gansu a mafarki. kuma mun yi magana da Baffan yace za'a buɗe makarantar islamiyar, idan ya so sai a haɗeta da boko, kuɗin da kika ce na kai gidan marayun na kai ga receipt ɗin, amma sun ce na faɗa miki akwai yara guda goma sha biyar da aka kwantar a asibiti, to sai naje asibitin na biya bill ɗin da ake buƙata, waɗan nan yaran ma da aka kai su sudan, sun kira ɗazu sun ce na faɗa miki result ɗinsu yayi kyau, gobe za su sauka a ƙasar nan, sun ce na faɗa miki suna sauka wurin ki za su fara zuwa, suna ta cewa ayi miki godiya su da iyayen su. gwandar a markaɗa ko yanka miki za'a yi?". gaba ɗaya a wani ruɗe yake maganar, kamar dai wanda ya susuce, ya juyo ya kalli Fullo da Nihal waɗanda ke tsaye a bayansa. "Nihal ɗauko wuƙa ki yanka mata gwandar". sai kuma yace da Fillo,"Halima taci faten?". a karo na farko da ya taɓa ambatar ainihin sunan Fillo. "a'a naga tana bacci shiyasa ban tasheta ba". "sauri ki zubo mata Halima, yanzu zan tasheta". kusan a tare Fullo da Nihal suka juya jiki duk a sanyaye, hannayen Fillo na karkarwa ta buɗe flask ɗinta zuba faten tsakin da yawa, kafin ta yunƙura ta miƙe daga duƙen da take Turaki yazo ya karɓa, karɓar tasa tayi daidai da shigowar Nihal daga ɗauko wuƙar, ta ɓara ƙwallon gwadar ta yi masa wata iriyar rabawa, cikin sauri ta isa ta ajiye plate ɗin akan table ɗin da Turaki ya ɗauko ya ajiye a gaban gadon. har yanzu baya jin mazaunansa za su iya zama akan wani abu, don haka ko a yanzu ma gwiwoyinsa ƙara zubewa suka a gabanta, kafin yasa hannu ya juyo da kwanciyartata saitinsa, ya kalli fuskarta, ya kalli murfin idonta da yake a rufe, sannan ya kai ɗaya hannunsa ya kamo tsintsiyar hannunta guda ɗaya ya riƙe, tare da kai ɗaya hannun nasa ƙasan hancinta. jijiya bata motsi!, haka ma numfashin baya fita!, sai ya ƙara maida hannunsa wuyanta, nan ma beat ɗin dake wurin ba ya harbawa. ya san akwai suma kuma ya san akwai mutuwa, kamar yanda ya san banbancin kowanne, sai dai ba ya jin zai iya ɗaukar abin da yake ganin gaskiya ya ɗora Maama a wannan matakin, ba zai iya ba, ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243