Chapter 110
Chapter 110
duk ta inda aka so, wannan ba daidai bane wallahi, kuma Allah ko kotu muka je sai an ƙwatarwa ɗana hakkinsa". Baffa ya ɗago ido ya kalleta da kyau yace,"you are free to go there Madina, ki shigar da ƙara gaba da kotu kinji. abu ɗaya kawai nake so in sanar miki shine babu mahaluƙin da ya isa ya hana wannan auren. duk fitinar da zaki tayar wallahi sai dai ta ƙare miki ke ɗaya, wannan batu na aure magana ce ta mahaifiyata, saboda haka babu uban da ya isa ya hana, ɗa nawa ne ba na wani ba, kuma tun a jiya na faɗa miki muddin kika nemi ki ɗaga min hankalin ki tada fitina akan wannan batun, to tabbas zai yanke tsatstsauran hukunci akanki". Hajiya Madina ta ƙara fashewa da kuka sosai. Turaki dai na zaune kamar gunki sai kallon Baffa yake kamar yana kallon sabon mutum. sai da Hajiya Madina taci kukanta sosai tukunna ta ɗago tace,"muddin ina raye, muddin da lafiyata babu wanda ya isa yaywa ɗana auren dole, sai kace wata mace. abunda ko ada can ba'a yi ba, idan ma auren dolen ake so ayi masa a fara faɗa masa mana, ba wai aje a ɗauko ɗiyar matar da ba ƙaunarsa ta ke ba a haɗasa da ita". sai tai ta ɗauke idonta daga kan Baffa ta maida kan Turaki, tasa hannu ta ɗago fuskarsa daga saman cinyarta da ya kwantar, ta kalla cikin idonsa tana ganin yacca ƙwayar ta sauya kamar bata shi ba, taji wani bala'in tausayinsa ya kama shi, yana da mugun haƙuri kuma yana da tsananin biyayya ga iyaye ko da ace zai cutu, tana kallonsa tace,"kana da ni Hammah, ni mahaifiyarka ce da ba zan iya zuba ido naga ana cutarka ba, saboda haka ka faɗa min zaka iya auren Ilham ko ba zaka iya ba?, ka shiryawa wannan auren ko baka shirya masa ba?". Turaki ya haɗe murfin idonsa ya rufe yana jin wani abu na taso masa daga ƙasan zuciyarsa, dama har yanzu shi under 20years ne shi bai sani ba?, dan a ganinsa yaron ma da yake 20years ba za'ace zaa masa irin wannan auren ba, me yasa Baffa?, me yasa zai biyewa rikicin tsufan Boɗejo?, ofcourse baya san wannan auren, kuma ko da ace zai iya so ɗin kukan Maama kaɗai na iya sa shi ya ƙetare umarnin Baffa da bai taɓa ƙetarewa ba tunda aka haife shi, to amma sai dai Baffan ya karya shi da furucisa guda ɗaya, ya sagar da shi daga duk abinda yay niyyar yi. dan shi tanadin da yake Baffa na gama zancensa daga nan sai ya miƙe yaje ya sami Ilham ɗin yay mata cin zarafin da ko da gawarsa ba zata yarda a ɗaura mata aure ba, to sai dai a yanzu Baffa ya gama da shi tunda har yake batun zai ɗauki tsatstsauran mataki kan Maama, bijirewar tasa ba zata haifar da komai ba sai ɗa mara ido. dan haka zai amince ya auri yarinyar, amma ya tabbata da kanta zata bar gidan, dan ba zata taɓa samun fuskar zama da shi ba, ya sa ni ita ta amince tana sonsa tunda har aka yarda da auren, but she will regret. yanzu baida lokacin yi mata komai saboda ba abinda ke gabansa ba kenan, neman Fillo ne a gabansa yanzu. yasa hannu ya dafe kansa yana jin zafin dake kansa na ratsawa a jikinsa. ya buɗe ido ya kalli Hajiya Madina da har yanzu hannunta ke kan goshinsa tana kallonsa kamar ba zata ƙifta ba. ta ƙara ce masa,"karka cuci kanka, sai in har ka yarda za'ai auren nan, idan baka yarda ba yanzu ka miƙe in kai ƙara gaban Babban Alƙali, dan yau daga uban har ƴaƴan sai na maka su a kotu dan ba zan ci gaba da zuba ido ina kallo ana zaluntar min kai ba wallahi, ko zaka yi aure ba'a cikin shiri ba na yarda amma sai in wadda kake so". bata ma san sanda tai furucin daga uban har ƴaƴan ba. Turaki ya kalla mahaifinsa yace,"Baffa ni fa ba yaro ba ne". Baffa yay saurin ɗaga masa hannu yace,"sanin hakan yasa muka haɗa aurenka da ƴar'uwarka, ka shirya gobe after salatul juma'a za'a ɗaura aurenka. haka muka zauna muka yanke ni da mahaifiyata da ƴan'uwana, and that is our final decision, idan har kuma ka bijire min to tabbas zan sallamaka a cikin ƴaƴana sannan in sallami itama Babar taka dake ɗaure maka gindi". Hajiya Madina tayi hanzarin miƙewa daga kan kujera tace,"in har zan cika alƙawarin dana ɗauka na riƙe yaron nan bisa amana, to Alƙali Dikko dan ka sakeni ba zanji wani ɗar acikin raina ba. so barazanar sakinka ba ita zata sa in sauka akan bakana ba, aure in kaga anyi tabbas to da amincewar yarona". tana gama faɗar haka tace da Turaki,"Hammah ta shi muje, inga wanda ya isa yayi maka auren dole, ko da kai yaro ne ba'a isa ba balle kuma da hankalinka". cikin ɗaga murya Baffa yace,"Madina wai me yasa baki da mutumci ne, auren nan na faɗa miki mahaifiyata ce ta shirya shi, shine har kike so in ta ke umarninta?". Maama ta taɓe baki tace,"cikin ku huɗu da Allah ya bata kaf ɗinku wa aka yiwa auren dole?, kuma jikoki nawa gareta?, sauran ƴaƴan nata rasa ƴaƴa suka yi da ba zata yiwa ƴaƴansu ba sai nawa ɗan da aka sawa ido dan an gansa yafi kowa haƙuri, yafi kowa biyayya. to daɗin abinda ƙasa bata cika bakina ba balle a cuce shi...Me Babban suna ta shi ka ji, aure sai in bana numfashi, kaf ƴaƴana ba wanda aka isa aiwa auren dole". Turaki ya riƙe kansa da ke neman barazanar fashewa ya riƙo hannun Maama yace,"zan aureta Maama, zanyi auren na amince. adu'a kawai zaki yi min". ƙyam idonta ya tsaya akansa tana hango tsananin ƙarfin halin dake tare da shi wajen ganin ya furta hakan. ta maida kallonta kan Baffa tana kallonsa, ko a jikinsa, bai damu da halin da ɗansa zai shiga ba ma?. ta ɗauke kanta tace,"babu komai akwai Allah, idan ma saboda wata manufa aka haɗa auren nan Allah ya saka maka ya kareka daga sharrin mugun mutum...and ko banza ƴarsu ce zata wahala wallahi tunda babu sonta a zuciyar mijinta. kuma sai in dai bai ga wadda yake so ba, abu da Allah ya halasta masa auren mace huɗu, yana ganin wadda yake so zan ɗaura masa aure da ita wallahi kuma banga wanda ya isa ya hana faruwar hakan ba, in masa auren gatan da ko ƴaƴan masu mulkin ma ba'a yi musu". taja hannunsa,"tashi muje Allah yayi maka albarka ya baka ladan biyayya, idan ba me tarbiya ba waye ma zai yarda da wannan kalar cutarwar". ta mayar da kallonta kan Baffa tana cewa,"Allah ya bawa mutum ƴaƴa amma baida burin da ya wuci ya ƙuntata musu, duk wai ace mutum shi yana bin maganar manyansa, Allah na tuba yayye ba iyaye ba har sunsa na baƙantawa ɗan cikina, ita kanta yarinyar nasan ba kai tsaye akai komai ba sai da ubanta yaji ta bakinta, amma kai wai me biyayyar yayye ka yanke hukunci kanka tsaye, sai anyi magana ka dafe ƙirji kana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243