Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 22

Chapter 22

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,223 words 0 views Progress saved
Download Book

idan da zata zauna zaman lissafi zata iya lissafa wucewar kusan rabin shakara rabon da taga ya shiga cikin wannan mood ɗin, mai sauya shi ya fita daga Turakinsa ya koma wata halittar ta daban. zata faɗa ko aina ne he is very simple Man, abu biyu ne kawai a duniya masu rikiɗar da shi, su saka ya fusata har ya aikata wani mummunan abun ba'a cikin hayyacinsa ba. sai dai mamakin da ta ke ta ya Fillo ta fama masa ciwon da ke zuciyarsa, ko kuma garin ya ta taɓa abunda zai iya aikata kisan kai akansa?. tana kallon Fillo tace,"me kika yi masa?". tana girgiza kanta tace,"ni ban masa komai ba. abinci yace sai na cinye kuma ni na ƙoshi". "an kira shi a waya ne?". "ni ban sa ni ba". Zaytuna tayi shiru, dole cikin biyun abunda ke haddasa masa ƙunci zuci ya faru. tasan ko menene baida alaƙa da mahaifiyarsu tunda Fillo bata san komai ba akai, amma duk yanda akai bisa kuskure ta taɓa Maama, shi kuma ɓangaren da baya ɗauka kenan. idon Fillo na kan Turaki, tsab zata iya lissafa adadin jijiyoyin da suka fito raɗau ajikinsa, tun daga kansa har hannayensa da wuyansa. fahimtar da tayi masa mutum ne shi da ba'a sanya mahaifiyarsa a cikin kowanne lamari saboda muhimmancinta. kuma ita sai a yanzu take ganin rashin kyautarwarta, bai kamata dan yace taci ƙazantarta ba ta buɗi baki tace ai Hajiyarsa ce ta dafa, kenan jagwalgwalon ba nata bane na uwarsa ne, matsayinsa na wanda tasan ya bata shekaru da yawa bai kamaci irin wannan maganar daga gareta ba. ko babu wannan ma yaci ace ta darajarta shi duk da jin kai da ta fahimci yana da shi, tunda ita da Kakarta a ƙarƙashinsu suke rayuwa sama da shekaru biyar, ba'a taɓa haɗasu da mara kyau sunci ba matsayin su na ƴan aiki, haka kuma ba'a basu makwanci mara kyau ba. idan ba zata manta ba me gidan da kansa na shiga ɓangarensu ya gaida tsofaffi, Hajiya Madina ce ma bata taɓa gani amma ta taɓa ji ance ta shiga sau ɗaya. kawai sai tayi ƙasa da idonta tana jan yatsun hannunta, maganar Kaka na dawowa cikin kunnenta na wani lokaci can baya da ta taɓa faɗa mata. "Halima dan Allah ki rage jin kai domin ke ba ɗiyar kowa bace, ki rage zafin zuciya, ki zama me haƙuri, ki zama mai sadda kai ga wanda duk kika san ya shiga ɓacin rai ta sanadiyarki, karki ce ba za ki bada haƙuri ba domin tsugunawa wada ba gajiyawa bane, ka zama me haƙuri ma da iya bada haƙuri wani babban arziƙi ne gare ka...bada haƙuri babu abinda zai rageki da shi sai dai ma ya ƙareki da abubuwa da dama...zai iya sawa aga mutumcinki, zai iya zama silar ɗaga darajarki". Fillo ta rufe ido ta haɗiye wani busashshen yawu, a hankali ta shiga sauke gwiwoyinta har ta kai su ƙasan tiles ɗin. muryarta ta fito da amon rashin jin daɗi tace,"dan Allah kayi haƙuri". hannunsa na cikin na Zaytuna ya damƙe da kyau, ya waigo yana mata wani irin kallo kamin yace,"cinye abincin nan shine zai wanke ki". itama sai ta ɗago ido ta kalle shi,"to idan na cinye zaka haƙura?". "kurma ce ke da ba kiji me nace ba". faɗin hakan yasa ta miƙe ta zauna kan kujerar, har yanzu hannunta bai bar rawa ba ta ɗauki spoon ta fara tura abincin bisa dole. kuma har lokacin su na tsaye shida Zaytuna idanunsu duk akanta, daga yanda ta ke ci yasan cin dole kawai takeyi, sai dai shi babu ruwansa ko zata amayar sai ta cinye. sai da tacinye tass tukunna ta ɗago da kanta ta kalle shi idonta na zubar da hawaye, yay saurin rumtse idonsa yana kauda kai gefe, idan da abinda ba ya son gani a rayuwarsa shine hawayen mace. yana jin zata miƙe ba tare da ya kalleta ba yace,"wa zai shanye miki tea ɗin?". jin hakan yasa tasa hannu ta ƙara goge wani hawayen, sannan ta kalli Zaytuna tace,"Anty na ƙoshi idan na kuma cin wani abu amai zanyi". Zaytuna tace da shi,"Hammah ai mata afuwa". ya wurgawa Zaytuna wani kallo sannan yace da Fillo,"kin zuba kinsha ko sai na barki da Allah akan zagar min Uwata da kika yi". tayi saurin girgiza masa kai. yace,"to zuba rabin kofi ki shanye". tana zuba tea ɗin tana hawaye haka ma har ta shanye bata bar kuka ba. sai a sannan yay ƙasa da murya yace,"aikin da aka kawoki shi kawai za ki dinga yi, duk ranar da kika ƙara gigin saka hannu a abinda zanci sai kin cinye shi ta hanci". yana faɗar hakan ya bar wurin, yana fiddo waya daga aljihunsa yay picking call ɗin Bello Ƙaraye. a bakin ƙofar parlo ya tsaya yana cewa,"bana part ɗina ina part ɗin Maama". da faɗin hakan ya katse wayar ya maida aljihu sannan ya nufi kujera ya zauna. Zaytuna ta wuce upstairs bayan tace da Fillo idan baƙo ya shigo ta kai masa ruwa da lemu. ta amsa da tou, sannan ta miƙe ta kwashe kwanukan abincin da aka tursasa mata ci ta kai su kitchen, ta dawo ta gyara wurin ta goge ya zama fess sai ƙyalli glass ɗin yake. a kitchen ma kusan duk wani abu da ake cin abinci a cikinsa sai da ta fito da shi ta wanke, wannan koyarwa Kaka ce gareta, kwanukansu kullum sai sun wanke su ba iyaka wanda suka ci abinci ba kaɗai. a hankali ta ke yin komai gudun kar ta fasa wani abun tunda komai tangaran ne. bayan ta gama gyara kitchen ɗin ta fito ta hau upstairs ta tambayi Zaytuna aina zata ɗauki lemun. Zaytuna tace,"ki buɗe friedge za ki gansu aciki, amma karki manta ki haɗa da cup". ta amsa da,"to Anty". sannann ta sakko ta koma kitchen ɗin, sai da ƙyar ta iya buɗe friedge ɗin saboda bata san yanda ake buɗe shi ba. drinks ne kala-kala aciki da ruwa na jarka, ta san dai ruwan amma lemun idan aka cire fanta bata taɓa ganin duk sauran ba musamman five alive na kwali. kawai sai ta ɗauka ƙaramin tray ta saka kowanne guda ɗaya tare da faro guda biyu. lokacin da ta iso wurinsu Turaki ya sauke hannun rigarsa na dama yana nunawa Bello yanda ciwon wurin yayi, babu wanda yasan da zuwanta wurin balle tsayuwar da tayi tana bin ciwon nasa da kallo ganin yacca yay rami, ita bata taɓa ganin ma irin ciwon da yay haka ba. cikin kaɗuwar ganin ciwon ta sauke idonta ƙasa kawai tayi tsaye a wurin, tafi ƙarfin minti uku kamin Bello ya ankare da ita yace,"bismillah mana". ya faɗa yana kallonta. ta ƙaraso ta aje tray ɗin saman table ɗin da ke tsakiya, sannan ta tsuguna ta gaida Bello cike da ladabi shima kuma ya amsa mata da fara'a. tana durƙushe Zaytuna ta iso itama hannunta ɗauke da bowls guda biyu, duka snacks ne aciki.l ta aje kusa da tray ɗin. idonta na kallon Bello tace,"Hammah Bello ina kwana". shima nasa na kanta yace,"lafiya lau Zaytun, ya kike ya hutu kuma?". ta amsa mishi da,"lafiya lau wallahi, ya office?". ya amsa da,"office babu daɗi, aminina ya gudu ya

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243