Chapter 199
Chapter 199
dawo gida na duba takardar gonar a cikin takardun Baffa, ina ta sauri but kin san lamari irin haka dole yana ɗaukan lokaci". ya faɗa yana sa hannunsa a bayanta yana zagaye ɗan ƙaramin ƙugunta da shi, sannan a hankali ya ƙara raɗa ma ta,"am sorry, kin haƙura?". har sai da ya tabbatar zuciyarta ta nutsu sannan ya a hankali laɓɓansa su ka sauka akan cheeks ɗinta. sannan ya shiga tambayarta me yasa bata shirya ba, Mum na ta yi masa waya tun ɗa zu, idan ba su je yau ba za'a sami matsala. ta ce,"ni ban san kayan da zan saka ba ai". a lokacin taji sautin murmushinsa kafin ya saketa, closet yaje ya zuge ya buɗe ɓangaren da abayas suke jere a jikin hanger, ya ɗauko wata orange colour da tasha uban adon stones a jiki. "na ɗi son abaya akan atamfa ko less". ya faɗa yana ajiyewa akan gadon sannan ya kamo hannunta ya kaita gaban dressing mirro ya zaunar da ita kan stool, da kansa ya ɗauka body lotion ya shafa ma ta, ita dai kallonsa kawai take ta cikin madubin, kamar ba asalin Turakin da ta sani ba, ya ɗauka powder ya rambaɗa ma ta, taita dariya, ganin zai mayar da ita dodanniya tai saurin karɓar form ɗin ta gyara powdern. ba ta yarda ya saka mata brezier ba kamar yanda taga yana ƙoƙarin yi, ta karɓa ta shiga toiler ta saka da kanta, tana fitowa ta tarar baya nan, sai ta ɗauki rigar ta saka, abayar ta ƙara haska fatar jikinta da tayi fresh, tayi rolling mayafinta, sai ta zama kamar balarabiya, kamar ba wannan Fillon da ke yawo cikin tsumman kaya ba shekarun baya da suka wuce, wannan wata Fillo ce ta daban, wacce ake rainonta cikin so da kulawa, wacca ake nuna ma ta babu wata tamkarta, wacca ta shigo cikin sahun masu ji da ado da ƙwalisa. ta ɗauko ƙaramar jaka kalar kayan, duk sai taji ta ƙosa Turaki ya dawo ya ganta, tana tsaye tana ta kallon kanta a madubi, tana tunanin duk ranar da akace ta ƙara kumari kuma ya zata dawo kenan saboda tsabar kyau?, sai ta tuna irin wankan da Raudha ke yi a saudiya idan zasu fita, tafiya tayi ta ɗauko wani box ta buɗe ta ɗauko glass ta saka. tana shirin fita yay daidai ta buɗewar Turaki ya sanyo kai, turus yay ya tsaya yana kallonta tun daga sama har ƙasa, laɓɓanta suka tsuke fuskarta na bayyanta murmushin jin daɗi. tana jiran kalman yabawa su fito daga bakinsa sai taji yace,"ina za ki a hakan?". ya faɗa annurin fuskarsa na ɗaukewa, bai bari tayi magana ba ya wuceta ya shiga ciki, binsa tayi da kallo taga ya ɗauko hijabi, babu shiri ta juya zata fita yay saurin damƙo hannunta. "babu abin da za ki fita a haka, da igiyoyin nawa uku reras akanki za ki fita a haka saboda an faɗa miki bana kishinki?". "to mene a wannan shigar?". "abubuwa da yawa kuwa da zasu ja hankalin wani ɗan banzan a kanki, ko ba kiga yanda kika yi kyau ba ne?". ta juya idanu tare da yin fari tana cewa,"ai baka ce nayi kyan ba". ya ce,"idan nace zan tsaya faɗa miki yacca kika yi kyau ba zamu samu damar fitar nan ba, dan duk lokacin za su tafi ne ba tare da na gama fayyace miki irin kyan da kika yi ba. oya ta ina zan zan cire wannan pin ɗin?". ta marairaice da cewa,"please ka bar ni a haka, wa ye ma zai ganni to bayan a mota zamu je?". sai kuma ta ɓata rai tana cewa,"wai ma ba gidan su me wancan part ɗin za mu ba?". ya kalleta yaga yanda ta wani ci kunu tamkar ba ita ba, yace,"can zamu sai aka yi ƙaƙa?, sai aka ce a gidan su babu maza ko babu masu idanu?". ta ɗan murguɗa baki,"sai ba zan dankama hijab naje gidansu ba tayi tunanin ni ƴar ƙauye ce wadda bata waye ba, ka sa aita gulmana idan mun baro gidan". "su waye za su yi gulman naki?". "ko ba tayi ita da muƙarrabanta ba za tayi ita da zuciyarta, don Allah ka barni in je a haka kar ta raina ni". dariya ta ba shi, but sai ya gimtse yana ɓata nasa ran shi ma, ta durƙusa tayi pleading hannayenta tana yi masa magiyar ita ya barta ta tafi a haka, a ƙarshe dole ya haƙura ya barta, sai dai bai yarda tasa glass ɗin ba ya zare shi yay jifa da shi, ya kama hannunta su ka koma ɗakinsa ya ɗauko facemask ya saka ma ta. "kuma saura idan munje in ga kin wage baki kina dariya ko murmushi...". tun bai ƙarasa faɗar abin da zai ce ba tace,"yanda zata ji daɗin cewa zaman ƙunci nake yi da kai ba, ni dai kawai babu ruwanka da ni ka bini da ido kawai". ya buɗe baki da mamaki fal yana cewa,"when?, where?, how?, duk a yaushe kika yi baki har kike magana haka?". ta turo baki gaba, ta ƙwace hannunta ta ɗauko baƙin glass ɗinsa ta saka masa,"yana yi maka kyau sosai idan ka saka, amma ni ɗaya zaka ke sakawa, promise". ya karyar da wuya,"i promise you". hannunsa ta riƙe suka fita, tunda suka hau saman titi kuma duk sai ta koma masa kamar ba wannan ƴar Babyn ba sarkin daru da rigima, wacce ta ke hawar masa bori ya zauna zaman lallashi, wannan wa ta Fulani ta daban ya ɗauko, me faɗa kamar yaƙi, da kuma ba da instructions. ta dage tana faɗa masa in sunje gidan bata yarda ya kalli kowa ba, bata yarda yay magana sama da sau biyar ba, bata yarda ya amsa gaisuwar kowa ba, bata yarda ya cire glass aga hasken idonsa ba. shi ma ya tamke murya yace,"duk da wa kike?". "da Muhammad Turaki". ya saki hannunta ya ɗalli bakinta, ta ɗauke idonta da ga barin kallon titi ta juyo ta kalle shi. "to ba sunanka ba ne?". "a bakin mutane ba, amma ban da naki". "to ni haka zan faɗa". yay murmushi,"wai to duk wannan cin maganin na mene?, ba fa a haka muka fito ba, ko nayi laifi bisa kuskure ne?". tayi narai narai da idanu ta ce,"ni kawai bana son zuwa gidan". "me yasa?". "bana so muje wannan matar ta ganka, na san dole zata kalle ka, na san dole sai taji wani abu akanka". tai maganar kamar zata yi kuka. yay shiru bai ce komai ba, sai da suka yi nisa a tafi sannan ta ƙara cewa,"kuma na san kaima zaka kalleta ko?". nan ma dai bai ce ma ta komai ba, hakan yasa kawai ta kifa kanta a saman gwiwarta tana jin wani bala'in zafi a zuciyarta, idan ta san haka ne da tun farko tace bata da lafiya ba zata iya zuwa ba. *_bari nayi amfani da wannan dama wajen miƙa godiyata da nuna jin daɗi gare ku masoyana, tank you so much lovlies for keeping up with this story, ga shi dai muna ta tafiya amma ko kaɗan baku ƙosa da ni ba, duk da inata ƙoƙarin ganin na yanke labarin an gama shi kwatakwata. Anyway don Allah kuci gaba da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243