Chapter 47
Chapter 47
yana raye?, to mene amfanin ɓoyewar?. sai kawai ta gyaɗa kai cikin ranta tana faɗin wataƙila kuma ba'a so a ɗora alhakin mutuwar tata ne akan Turaki shiyasa, tasan zasu iya komai tunda suna da uwar kuɗinsu. Fillo da take jinsu a lokacin ta kira sunan Kaka, wani farin ciki ya baibayesu suka yo kanta. Maijidda tayi mata wata runguma har sai da ƙashin bayan Fillo ya amsa. kuma a sannane Amir yazo, tunda ya shigo ya kafeta da ido, kallonsa take shima kallonta yake, zuciyoyinsu na saƙa abubuwa iri ɗaya dangane da junansu. kalmar da Amir ya fara faɗa mata shine,"za ki iya yin sallah?". kai kawai ta ɗaga masa, Yami ta kamata ta sakko a gadon ta kaita banɗaki. lokacin data fito Amir kawai ta gani har sannan yana tsaye idanuwansa duk sun faɗa ciki, kana kallonsa zai baka matuƙar tausayi. shi ya shimfiɗa mata sallaya, ya tayata saka hijabin, yace mata idan zata iya ramawa duk ta rama, idan ba zata iya ba tayi wasu ta bar wasu sai jimawa. tambayar da tayi masa shine,"kwana nawa yau?". "huɗu". amsar daya bata kenan. kuma tunda ta tayar da sallar bata tsaya ba sai data rama duka sallolin dake kanta, har lokacin Amir bai zauna ba yana tsaye. tana idarwa kuma sannu kawai yay mata, zai fice a ɗakin tabi bayansa da kallo tace,"ina zaka?". "tafiya zanyi". amsar daya bata kenan ya fice daga ɗakin bai jira cewarta ba, jikinta yayi matuƙar sanyi, su Kaka suka dawo ciki ta tambayi Maijidda suka ce ta tafi raka Amir. Yami ta zuba mata abinci ta ajiye a gabanta, har lokacin tana kan sallaryar ta miƙe ƙafafunta, da ƙyar tayi sallar, ƙarfin dauriya irin nata kawai. "na ƙoshi Yami". kalmar da ta faɗa kenan, kuma kafin Yami tace wani abu an turo ƙofar ɗakin an shigo, Dr Yusuf ne, suka amsa sallamarsa sannan ya umarci Fillo da ta koma kan gadon za'a ƙara saka mata drip. gadon ta koma ta kwanta, yay mata wasu tambayoyi dangane da yanda take ji tana basa amsa, acikin drip ɗin ya zuba duk alluran da za'ai mata. yana gama saka mata kuma yace da Kaka,"idan ya ƙare a bata abinci taci". da haka ya fita. sai yanzu su Kaka suka sami natsuwa, Yami ta zuba musu abinci suka shiga ciki, lokaci zuwa lokaci Maijidda na lura da ruwan daya kusa ƙarewa. bayan wani lokaci hankalinsu ya karkata ga turo ƙofar ɗakin da akayi, ganin wanda ya shigo da sauri Kaka ta miƙe tana yi masa sannu da zuwa tare da amsar ledojin dake hannunsa. Khalil ya shigo yana ta kallon Fillo, mamakin da kowa yake akanta shine taya akai ta fita acikin wannan daren?, kuma me taje yi a wannan dajin?. shi dai abinda zuciyarsa ke raya masa shine Turaki ne ya ɗauketa zai je ya cutar da ita, Turaki ne yay komai, har yau haka zuciyarsa ke faɗa masa. *Plss Comment, Vote, and Share.* [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* _🤔zato dai zunubi ko da ya kasance gaskiya, ku daina ɗaukar hakki babu kyau ni gaskiya nake faɗa muku, ahh tou🤣, yo kowa ya tashi sai ya wani kama cewa Hajiya Madina kaza-kaza, banda ma dai neman magana yaushe kuka taɓa ganin ta cutar da wani daban balle Turaki da ya gama nannaɗe zuciyarta😒...to a daina gaskiya ban so, duk wanda naji ya ƙara taɓata zan hau bori😭😭..._ *18* After long minutes sai ga Zaytuna itama ta shigo room ɗin, har lokacin Khalil yana nan bai tafi ba, yana zaune akan kujerar da Kaka ta ajiye masa. yana kallon Zaytuna da mamaki yace,"from where?". bayan duk ta gaida su Kaka tare da tambayarsu ya me jiki tace da shi,"bamu jima da shigowa garin ba, so muna sauka a airpot mu kai waya da Hamma yake ce min yana nan". Khalil ya ƙara tambayarta,"ya Granny ɗin?". tace,"tana lafiya, duk tana gaishe ku...da ta saka rigimarma sai mun zo tare tana so taga Hammah". yace,"Allah sarki Granny, insha'Allahu zan matsa masa akan muje, sai mu dawo a ranar tunda dai am sure ba zai kwana ba". Zaytuna ta cirewa Fillo drip nata da ya ƙare yanzu, itama tana tambayarta yanda take jin jikin tana faɗa mata komai da sauƙi ƙafarce dai har yanzu. after five minutes Zaytuna ta yiwa su Kaka sallama saboda kiran da Baffa yake yi mata, tare suka fita da Khalil wanda yake ta mamakin yacca akai har yanzu Turaki bai shigo ba. bayan fitarsu Maijidda ta dafa shoulders ɗin Fillo tace,"mene damuwar?". tace,"me kika gani?". Maijidda tace,"na san dai ba ki da lafiya amma yanayin fuskarki ya nuna akwai damuwa a ƙasan ranki". Fillo ta haɗiye yawu tukunna ta ɗago ta kalla Maijidda sannan tace,"me yake damun Amir?". Maijidda ta tashi daga kujerar da take zaune ta dawo gefen gadon kusa da ita ta zauna, ta kamo hannunta ta riƙe acikin nata tace,"me kika gani?". Fillo ta dake ta hana kuka ƙoƙarin fitowa tace,"sannu fa kawai yace min, ina amsawa yasa kai ya fice". "kinyi masa wani laifi ne?". ta girgiza kanta,"a'a ni banyi masa komai ba. kuma ko da ace ma nayi masa ba zai min haka ba tunma da ya ganni banda lafiya". Maijidda tace,"to kwantar da hankali ba abin da kika masa, kawai yana cikin damuwa ne akan lamarinki. yace ya kasa fahimtar me ke faruwa, yana ganin kamar mutanen ɓoye naso su shafeki ne tun a wancan ciwon da kika yi, amma wannan karon sai yaga kamar ma sun riga sun shigeki...baki gani ba wallahi yanda yake ta sadaƙa yana sauke miki alƙur'ani, anan fa yake kwana kullum ba ya tafiya, abinci sai Innarsa tayi da gaske". Fillo tai ɗan jim kafin tace,"to ai ni banda wasu aljanu, hasashensa ne dai kawai". Maijidda tace,"to aikuwa abin da kowa ke faɗa kenan". Fillo ta kalli su Kaka da suke can gefe su na maganarsu, hankalinsu ba ya kansu gaba ɗaya. murya can ƙasa tace,"Maijidda ina asirin da nace miki zan ɗauke a ɗakin Turaki?". idanun Maijidda a waje take kallon Fillo da al'ajabi, ai dama tunda hakan ta faru ta fara tunanin da wuya idan ba karambaninta ne ya bata damar ɗauke asirin da ta gaya mata zata ɗauke ba. ita kam ta fara tsorata da lamarin ƙawarta, ta bakin Amir aljanu sun shigeta domin mutum dai ba zai yi abin da takeyi ba. Fillo taja hannun Maijidda da taji tayi shiru,"kina da matsala wallahi, shi yasa wani lokacin da faɗa miki abu gwara shiru". bata bawa Maijidda damar magana ba taci gaba,"na ɗauke asirin harma ya ƙone". "shima ke kika ƙona shi?". ta girgiza kanta,"aa wallahi ikon Allah kawai, ba ki gani ba kamar tashin bom haka yayi tushhh, kinji yanda yake ɗoyi kuwa Allah kika shaƙa kayan cikinki sai sun kusa zubowa...kuma kin san me?". ta faɗa tana muskutawa ta gyara zamanta akan gadon inda ta juyo ta fuskanci Maijiddan. "ina ga wannan asirin ne yake hana Turaki Sallah, ai dama na faɗa miki naji Maama na kokawa da hakan. kinga nima fa tun sanda na ɗauko shi naji bana sha'awar yin sallah kwata-kwata...bari dai mu bar asibiti zan baki labarin komai". ita dai Maijidda tsuru tayi tana zubawa sarautar Allah ido, ta ɗanja baya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243