Chapter 2
Chapter 2
wanda bata so ko da ƙuda ɗaya ya taɓa mata shi, kan kace kwabo hawaye sun fara reto akan kuncinta, cikin ƙanƙanen lokaci kuma ta fashe da kuka, kukan da ya haddasa wani duka a ƙirjin Yusuf. "Sweety". sai a yanzu laɓɓansa suka buɗe da kiran sunanta, ta ɗago kanta da ta duƙar tana kuka ta zuba idonta cikin nasa. sai kawai ya sakar ma ta wani kyakykyawan murmushi, irin murmushin nan da zai tsayar da kukan nata. amma me? kamar yanda ya riga ya sani ba zata yi shirun ba, hasalima kamar ya ƙara tunzurata ne, dan kawai ɗora hannu tayi akan fuskar ta ƙara fashewa da kuka, kuka sosai kamar ƙaramin yaro me neman shan nono, sautin muryarta na fita cikin kuka na shagwaɓa da damuwa take ƙara cewa. "ni ba irin wannan ba, bana son wannan ka jefar da shi. indai murmushin ƙarfin hali ne a tare da kai your Excellency bana ƙaunarsa, kuma ba shi zai sa na sami sassaucin raɗaɗin damuwar da na riska a tare da kai ba". tuƙin yake amma gaba ɗaya attension ɗinsa ya koma gareta, kyawawan idanuwanta na kan wuyansa tana bin wani dunƙulallan abu da ke wucewa ta maƙogoronsa, muryarta ta ƙara narkewa tana cewa. "please tell me what is the problem?, Did you do something that you did not succeed on it?". ta riga ta san waye mijinta, yawancin damuwarsa na ta'allaƙa ne akan rashin cimma nasararsa akan abu musamman ma ta ɓangaren aikinsa, amma da mamakinta sai taji yace,"keep calm Sweety". voice ɗinsa ya fito very cool. sai ta gwaɓe kamar ƙaramar yarinya tana cewa da shi. "to ni dai ka dawo gida idan Allah ya kaimu gobe. ka bar komai da kake yi ka dawo, otherwise i will keep on crying". "Sweety isn't a big deal faa, please don't bother your self kinji". "ni ban yarda da kai ba". sai kawai ya tsarate da wani kallo da ya sa ta saki wani murmushi da ya fito da annurin fuskarta, sannan kamar sai a yanzu ne ma ya lura da irin shigar da ke jikinta wanda yasan ta kira ne dan ta nuna masa, dan haka ya kanne mata ido guda ita kuma sai ta cije gefen leɓenta kaɗan. gaba ɗayansu sai murmushinsu mai ƙarfin sauti ya fito a tare. wucewar daƙiƙa 2 su na aikawa junansu saƙo ta irin kallon da suke ma juna kamin Nuratu ta ɗan cukule fuska tace da shi. "this time around idan ka dawo sai nayi shari'a da Kalid". yanda tayi maganar da gaskiyarta yasa shi yin murmushin da ya bayyanar da haƙoransa, Kalid da ke gefe yana charting ya saki dariya yana faɗin. "yi haƙuri Madam tuba nake". "i will not accept your apology tunda kai dai har yanzu ka kasa koyon yanda zaka kula da amanar da aka baka". "wani abu ya faru ranki ya daɗe?". ya tambayeta cike da zolaya da kuma son ƙara kunnata. "au kana ma tambayana ne me ya faru ko?, Allah dai ya dawo daku lafiya zaka min bayani daki-daki. lawyer nake, kasan abunda zan aikata da wanda ba zan aikata ba". *No 3. Shongo Housing Estate, Gombe State.* *17:00 pm.* gidaje guda 5 ne a duk girman estate ɗin, kuma a kallo ɗaya zaka yiwa gida me lamba na uku ka gane ba ɗaya yake da sauran gidajen ba, tun daga girmansa zuwa tsaruwar ginin da yanda aka fitar da fasalinsa. anyi tsarin ginin gidan da ado da kwalliya irin na gidan sarauta, idan har ba sani kayi ba zaka tsammaci wata babbar masarauta ce. duk jikin bango da zaka kalla birjik yake da ado na ƙawa cikin nau'i iri-iri don burge idon me kallo. daga cikin gidan, second part da ke kallonka a yayinda shigowa cikin haraban gidan, a cikin tamfatsetsen parlon na alfarma wanda yake shaƙe da kayan alatu na more rayuwa, me ɗauke da royal italian cushion. sautin waƙa ne ke tashi acikin wata mp3 da ke manne ajikin wani glass kamar drower. _Happy birthday to you, happy birthday to you, happy birthday happy birthday, happy birthday to you._ waƙar na fitowa ne a cikin sautin kiɗa, yayin da ƴan mata da yaran da ke kewaye da shi ke tafi da hannayensu cikin murna da annashuwa, suma su na bin sautin waƙar fararan haƙoransu duk a waje. yana tsaye ne a gaban ƙaton cake ɗin da akai masa kwalliya da tsari me kyau an saka +1 ajiki, ga candle guda ɗaya a kunne a saman cake ɗin. irin yanda fuskarsa ke washewa da murmushi ba zaka taɓa ganewa hakan ba a kallo 1 zuwa biyu da zaka yi masa. lokacin da sisters ɗin nasa suka gama bin waƙar sai ya sunkuyo da kansa yayi blowing wutan candle ɗin sannan ya ɗago yayin da idanuwansa ke a lumshe yana yiwa kansa adu'a acikin ransa, for few seconds ya buɗe yana sauke ganinsa akan ɗaya daga cikin sisters ɗinsa wadda duk ta fi sauran matan haske da kuma dogon hanci. kyakykyawan murmushi suka sakarma junansu lokaci ɗaya. da ido yay mata alama ba tare da yay magana da baki ba, hakan yasa ta matso kusa ta riƙe hannunsa ya yanka cake ɗin, laɓɓansa na talewa da murmushi mai faɗi. ya yanko cake ɗin yana juyowa ga hannun damansa inda wata farar dattijuwa kyakykyawa ke tsaye sai murmushi ta ke, haƙoranta sunƙi rufuwa saboda irin farin cikin da take ciki, jikinta sanye da tsadadden less brown and black colour, tasha ɗauri kace budurwa me ji da tashen ƴan matanci. bakinta ya nufa da cake ɗin da ya yanko ya saka mata, ta karɓa tana faɗin. "Happy birthday Son. wish you long life and prosperity". "Use miyyete Maama, midon nana beldum joddaki emada eder duniyaru am". (Amin na gode Maama, ina alfahari da kasancewarki cikin rayuwata). ya faɗa yana yanko wani cake ɗin, sai da ya kalla duka sisters ɗin nasa su huɗu sannan ya sauke kallon ƙarshen nasa akan Zaituna, kallon da yay mata ne kawai ya fahimtar da ita mai yake nufi, dan haka ta matso kusa da Maama, ta buɗe baki itama ya saka mata cake ɗin a baki, ta karɓa tana faɗin. "Mi seyake be yaltugo nyandere danyeki ma Hamma am. Allah ɓeddane njamu be jutal balde barkante jo". (Barka da zagayowar ranar haihuwarka Yayana. Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana masu albarka.) fuskarsa ta ƙara washewa da annuri, ƙwayar idonsa na haskawa da wani ƙyalli na farin ciki da son ahalinsa. sai ya dangwalo icing cake ɗin ya lakuta mata a hancinta da gefen kumatunta kamar ita ce birthday girl ɗin, yana faɗin. "Special thanks to you Sweetest". daga nan kuma ya dinga yankar cake ɗin yana sakawa sauran sisters ɗin nasa a baki, suma duk su na binsa da wishing. haka ya gama basu sannan suma kowacce ta yanko ta nufo bakinsa da shi, sai dai bai karɓi na kowa ba sai da ya fara amsar na Maama da Zaitoon tukunna. su na haka Kalil ya shigo aka ɗora da shi, gaba ɗaya shi sai ya koma ma kamar shi ne me birthday ɗin, dan gaban cake ɗin ya zauna yana ta ci. kuma zuwansa wurin sai ya sauya ƙaramin birthday partyn da Maama ta haɗa zuwa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243