Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 217

Chapter 217

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,212 words 0 views Progress saved
Download Book

ruwan ɗumi kuma da shi za ki kwaɓin gaba ɗaya. yauwa to miƙo min gishirin can, if you like you can add sugar". bayanin da Nuratu ke yiwa Fillo kenan a kitchen ɗinta, a yayin da take koya mata yanda ake alkubus, tun san da suka dawo suka zo gidan taci taji daɗinsa tace zata koyi irin nata. Fillo ta ɗauko roban sugar da gishirin kamar yanda Nuratun tace, ta ajiye tana ci gaba da kallon yanda take yin kwaɓin da kuma sauraron bayanin da take yi mata. wucewar wasu mintuna Nuratu ta kalli Fillo jin tayi shiru, ta girgiza kanta kawai tare da jin tausayinta, kafin tace mata,"kin san mene?, wallahi tallahi cutar kanki za kiyi muddin za ki ɗauki damuwa kisa a ranki har haka, ke wa ya faɗa miki yanzu ana nuna damuwa da kishiya?, kina ƴar ƙaramarki haka?, amma...". ranta a ɓace ta ɗauki tukunyar da ta rufe ta bar kitchen ɗin. Fillo ta bi bayanta da kallo kafin ita ma ta bar kitchen ɗin, parlo ta wuce ta zauna, ta ɗauko Farha da ke cikin keken wasanta, tana cikin yi mata wasa Yusuf ya shigo, bayan sun gaisa ya ke ce mata. "jiya sai nake jin zancen an mayar da auren abokiyar zaman ki". wata ƙwallar ciwo ta tararwa Fillo a ido kafin tace,"ehh Yaya". "to Allah ya baku zaman lafiya, ayi ta haƙuri kin ji ko". "insha'Allahu Yaya, na gode". sai ya ƙara cewa,"amma ba ki da wata matsala ko?". "babu Yaya". "to masha'Allahu, kar fa kice za ki sakawa ranki damuwa kinji ko, kinga ba isassar lafiya gare ki ba. ya zancen karatun ki kuma?". tasa hannu ta goge hawayen da yay nasarar gangaro ma ta kafin tace,"lokacin da muna Ausburg har ya nema min addimission acan, to kuma da muka dawo sai yake cewa wai na haƙura kawai, to ban san me dai yake nufi ba, gaba ɗaya zan haƙura da karatun ko kuma wancan admission ɗin zan haƙura da shi". Yusuf ya sauke numfashi yay ɗan jim kafin yace,"ki ba shi lokaci tukunna, zuwa gaba sai kiji koma menene dai, amma karatun naki yana da muhimmanci sosai". ya miƙe daga kan kujerar da yake zai wuce ɗaki Farha tasa kuka, ya dawo ya karɓeta ya tafi da ita. wayar Fillo dake kan cinyarta tayi ƙara, ta ɗauka ta kara a kunne tare da amsa sallamar Maijidda. "ke na zo kuma na tarar ba kya nan". "ehh wallahi naje gidan Yaya Yusuf ne". "lallai ma ke ɗin nan, kuma kika ce na zo na raka ki ƙunshi, kin san za ki fita za kisa na zo, ko don kawai dai kin raina min hankali, wannan ai rashin mutunci ne". "Allah ya ba ki haƙuri maida wuƙar, ba jimawa zan yi ba yanzu ma fa nake shirin tahowa. sanin halin ɓata lokacinki yasa nace bari kawai in je in dawo, don Allah ki zauna yanzu gani nan a hanya". "sai kin dawo, idan da mota kika fita ki yiwa Allah ki samo min mangoro a hanya". "to uwar biyu". Maijidda tayi dariya sosai tare da cewa,"rufa min asiri maza su kaini ba mata ba, uban wa na aura da har zan zama uwar biyu, ke ɗin dai". su kai Sallama Fillo na miƙewa ta nufi ɗakin Nuratu, samunta tayi tana haɗa wasu magunguna a leda da dukkan alama maganin mata ne. Fillo ta zauna bakin gadon tana cewa,"Anty tafiya fa zan yi...". kuma bata ƙarasa ba ƙarar wayarta ya katseta, ganin sunan Maama yasa tayi saurin ɗagawa. daga ɓangaren Hajiya Madina tace da ita,"Daughter lafiya ba ki shigo ba?". "Maama naje gidan Yaya Yusuf ne". "zuwa yaushe za ki dawo?, ko acan za'a yi miki ƙunshin?". "a'a wallahi Maama, wadda muka yi zata zo ɗin da safe ta kirani an yi musu rasuwa, wai da zata turo sister ɗinta but tana faɗa min bata ƙwarai sosai kamarta ba, shi ne nace ta bar shi kawai". "ok to ki taho yanzu, nasa a kira wacca ta yiwa amare tazo tayi miki, bana so ki ƙara zama haka babu lallai, da ɗaurin aure an ga ba kiyi ba mutane sai su fara zaton ko baƙin cikin damuwar kishiyarki yasa". "to Maama yanzu zan taho". "to shikenan sai kin dawo, yauwa kar ki manta ki taho min da ajiyar nan da na ba ki, ga dai Nihal nan zata ja da duk alamu ɗinkinki na gobe ma babu". Fillo tayi ƴar dariya. Maama ta ƙara cewa,"ga baƙi nan an ƙara yi, su na ta tambayar uwar gidan Turaki, idan kin zo duk zan miki bayaninsu, ƴan uwana ne na Kano, babu wanda ya taɓa zuwar min sai yanzu da bikin ƴaƴansu ya tashi". bayan sun yi sallama Nuratu tace,"to ke ko anan ma ba sai ki godewa Allah ba, iyayen miji na sonki miji na sonki, danginsa su na sonki to kuma dan me na damuwar don ya mayar da matarsa?, auren nan fa biyayya ce kawai zai yi ba wai don baya sonki ba, ko a haka matsayinki da nata ai ba ɗaya ba, matar so kike, ita kuma matar shige". "Anty Nuratu wallahi ni abin da nake tsoro raini da wulaƙanci". ta faɗa cikin rauni da muryan ban tausayi. Nuratu tayi guntun murmushi me sauti. "me zai sa ta raina ki?, a wanne dalili Fillo?, wurinki fa daban wurinta daban, ko za ku shekara dubu a gidan nan sai kun so za ku haɗu da juna. kinga look, ni fa ko a yanda na ɗauka ma sai ka yi abin da za'a rainaka ɗin tukunna ake samun damar rainaka, as far as kin kiyaye waɗan nan abubuwan wallah ko da me kishiya ke ji bata isa ta raina ki ba. na farko karki kuskuren saka mata Ido a lamarinta, kar ki ke kai ƙaranta, saurin faɗa da ita shi ne babban abin da ke janyo raini, da kuma ɗaukar zuga, in har kishiya ta fuskanci kina ɗaukar zugar mutane to billahi ta gama rainaki, haka zalika kar ki yi gigin dinga shiga kowanne lamarinta ko da ita da kanta ke cusa ki aciki, baya baya dai...". Fillo ta tari numfashinta,"Anty Nuratu to ni ina ma nake da lokacin waɗannan abubuwan akanta. ina miki batu ne na tana ganin ita ƴar sarki ce, ta fini ilimi, ta kuma fini wayewa, kuma tana da aikin yi, sannan zata dinƙa min kallon cewar ni ba kowa bace face ƴar aikin da aka tausayawa aka auro, Anty Nuratu dole ta raina ni". "to ai ƴar aikin ta fita tun da har tausayin ma yasa aka iya auro ki, ita da ba'aji tausayin nata an aurota ɗin ba fa sai cusata da aka yi?, mtsww kin ga don Allah ni kar ki bayar da ni, ko wayewar ma ai bata fiki ba, wayewar shiga jami'a kawai ta fiki, amma ban da ta gidan miji, ko kin manta tsawon watanni da kika shafe a ƙasashe da dama kina durzar amarci ke da mijinki, ita ta sami wannan damar ne?, bata samu ba kuma ba zata samu ba". sai kuma ta miƙa mata ledar da ta gama zuba kaya aciki,"ga waɗan nan ɗin, ai duk nayi miki bayanin yanda za kiyi amfani da su". "to na gode sosai, Anty Nuratu sai

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243