Chapter 172
Chapter 172
ma bai san da shigowarta cikin motar ba, Fuskar nan kamar an aiko masa da mutuwa, ya fito sak a asalin Turakin da ta fara sani a rayuwarta, sai dai duk da wannan ɗaure fuskar da ya yi hakan bai hana fito da azababben kyan da ya yi ba acikin arniyar suite ɗin da yasa, black da ratsin pink colour irin na jikinta. tuna cewar ita fa ba matarsa ba ce yasa tayi saurin ɗauke idonta akansa, tana me tuna haramcin hakan, idanuwanta suka ciko da ruwan hawaye suna ƙoƙarin zuba, sai dai ba ta basu damar hakan ba dan sam bata so yaga weakness ɗinta a yau balle ya alƙanta hakan da zafin sakin da yay ma ta. ta kafe ƙunshin hannunta da kallo tana jin ƙaguwar su tafi aje ayi ayi a gama taron ta daina ganinsa a kusa da ita. da ga Bello dake driving har su kowa zuciyarsa a cunkushe take, Maijidda ce kawai da bata san damuwar komai ba take jin zuciyarta wasai sai kallon titi takeyi, Bello kuwa bini-bini sai ya daki stearing yana jan dogon tsaki. can da tafiya tayi nisa Fillo taji kallon dake jikinta ya yi yawa ta ɗago ido, karaf ƙwayar idonsu ta tsarƙe ata juna, tasha murr fiye da yanda ya haɗe tasa fuskar, kwatakwata ba ta san lokacin da bakinta ya suɓuce da faɗin,"kana da buƙatar ƙara sanin addini da kyau, domin na lura sam baka san yanda shari'ar musulunci ke tafiya ba". tayi maganar a ƙasa yanda su Bello da ke gaba ba zasu ji ba. Turaki ya dinƙa kallonta da mamaki tsantsa, kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce da ita,"kin fini buƙatar komawa makaranta ke da kika kasa ba da takardar sallamar da aka ba ki". ya faɗa daidai da isowar motarsu event center, suka yi parking a bakin ƙofar shiga gurin sannan suka yi zaman su a mota, Bello bai ko waiga ya kalli Turaki ba balle yay masa magana, ya fita ya tsaya jikin motar sai jera uban tsaki yake yi. sai da duk mutane suka gama shiga cikin hall sannan aka zo aka fito da Turaki da Fullo, Bello ya yi gefe abinsa kamar bai da wata alaƙa da Turaki, aka zagayo da Fillo side ɗin da Turaki yake nan da nan sai ruwan camera akansu, ƙememe suka ƙi riƙe hannun juna duk da ɓata ran da Anty Rahinatu(ƙanwar Mum) ta nuna musu, suka jera kamar ƴan ƙauyen ƙayayau. su Amatullah da suka zama ƙawayen Fillo su ne suka fara shiga a layi na hannun dama da ga nan sai iyayen gayyar a tsakiya, sannan abokan ango da Turaki bai sa a inda Bello ya kawoso su ba suka ja nasu layin a gefen hagu, abin dai gwanin burgewa, ba zaka taɓa kallon fuskar Turaki da Fillo ba kayi zaton ransu a ɓace yake, ko damuwa, hakan yasa duk hoton da aka ɗauke su sai sunyi kyau, ita dai tayi ƴar ƙarama a kusa da shi dan ita kanta sai nauyi take ji. su na ɗora ƙafafunsu akan step na shiga hall ɗin MC ya fara sanar da shigowarsu, kowa ya miƙe tsaye kamar an ce wasu masu mulkin nigeria ne za su shigo. ƙafafun Turaki da na Fillo suka shiga hall ɗin a tare, abokai kuma na take musu baya, cameras suka shiga ɗaukan su ta kowanne angle, me video coverage na ɗauka tun da ga kan takalmansu har zuwa kan fuskarsu. taro dai ya tafi a bisa tsari kamar yanda iyayen ango suka so ya kasance, yanda Bello ya zo ya yi baiograph haka AmaturRahman tazo tayi biograph na Fillo, anci an sha an bar abinci, biki dai kamar da ma an jima ana shirya masa dan sosai sisters ɗin Fillo suka dinƙa rawa, tashin kiɗa a wajenan kace bayyanar dujal, su dai waɗanda ake abin dominsu suna tsaye ƙyam kamar gumaka, gwara Fillon ma na ɗan murmusawa mussaman da ta ga cousin sisters ɗin suna ta shan rawa abin su, ruwan kuɗin liƙi kamar ba'a talauci a nigeria. Dada da Hajiya Madina kuwa watsa kuɗi kawai suke yi kamar babu talakan da ke buƙatarsu a duniya, har hannayensu sai da suka fara ciwo, rawa kuwa ba ka ce da jikinsu su ke yi ba, Dada sanda ta suɓuce zata faɗi akai saurin tarota, amma a haka taci gaba, ita kanta Maama har sai da Khalil yaji haushi yazo ya janyeta, tazo tana rawa ta manta gaban ƴaƴa take da abokan ƴaƴa. sai a ƙarshen taro Fillo ta yanka cake ɗin da Turaki ko kallonsa bai yi ba, kuma babu wanda ya lura da hakan banda Bello da ke kallonsa yana jin kamar ya rufe shi da duka, Hajiya Sajida Yayar Hajiya Ramla ita ta rufe taro da adu'a sannan aka tashi. lokacin da aka tashi ƙarfe goma sha biyu, direct daga nan aka wuce da Fillo gidan mijinta. su na zuwa Dadda tasa tayi wanka sharp sharp aka ƙara shiryata cikin wani ɗinkin atamfa na riga da zani, aka ɗora ma ta sabuwar alkyabba ba irin wacca aka zo da ita ba fara ƙal me arnen kyau, a gurguje suka ƙara yi mata nasiha daga bisani kuma suka yi ma ta sallama suka tafi, tare da shaida ma ta zasu zo gobe kafin su wuce in dai Dada bata hana su zuwa ba. Adda Asma ta kalli su Raudha da suka wani maƙale mata ta ce,"sai ku tashi mu tafi ko". kusan duk a tare suka miƙe su na rataya jakunkunansu, Fullo ta kamo hannun Maijidda, ta ɗage hular alkyabbar da aka rufeta da ita, ta kallesu duk su biyar ɗin, Amatullah, Amaturrahman, Raudha, Maijidda, Khairat, da kumburarrun idanunta cikin sanyin murya ta ce,"yanzu tafiya za ku yi ku barni ni kaɗai?, ku zauna tare da ni don Allah". Khairat ta ce,"mu barki ke ɗaya ko mu barki ke da angonki?, gulmammiya rabonki da azababben kukanki tun jiya da kika ji za'a kawo ki gidan miji yau". Raudha ta ce,"bar ƴar ƙaniya za ta wani marairaice mana ba". Maijidda ta ce,"rabu da su zanke zuwa ina ganinki kinji Hussainata". Dadda ta sake ƙwala musu kira dan haka suka fice da sauri su na ƙara yi ma ta sallama da yi ma ta tsiya. tana jiyo takun su a sanda suka sauka daga bene, ta jiyo ƙarar rufe ƙofar parlon ƙasa, sai kuma ta dinƙa jiyo hayaniyarsu a compound suna shiga mota an buɗe musu gate sun fita. ƙarar zuge gate ya haɗe da bayyanar wani bala'in tsoro a ƙirjinta, tayi saurin tashi ta isa window ta leƙa, karaf idonta ya sauka akan Turaki da yake fitowa daga mota, tana kallo ya ɗau wata hanyar ta daban ba nata part ɗin ba, sai kawai taji saukar sabbin hawaye a saman kuncinta masu zafi kamar zasu ƙona fatarta, ta ƙara komawa ɗaya windown ta hangesa ya buɗe part ɗin da yake na Ilham ya shige, tana kallo ya zuge glass door na entrance din parlon, sai taji kamar ya haɗa da zuciyarta wajen rufewa ya datse. a hankali ta sulale a wajen tana rushewa da kukan da zata ce bata taɓa yin irinsa ba, yanzu ita ɗaya zata kwana a wannan ƙaton wajen?, tabi tangamemen bedroom ɗin da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243