Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 146

Chapter 146

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,224 words 0 views Progress saved
Download Book

kirasa kayi masa bayani da kanka nace, idan kuma ka bari na ɗau mataki da kaina zaka sha mugun mamakina, sai kayi zaton bani na haifeka ba Muhammad". Turaki ya kallesa hankalinsa a mugun tashe, ya marairaice yana haɗa hannayensa yace,"don girman Allah Baffa ba sai an faɗawa Hakimi ba dan Allah Baffa, i beg you kayi min hukuncin duk da zaka yi min amma karka faɗa masa". sai kuma ya juya wurin da Maama take yace,"dan Allah dan Annabi Maama kuyi haƙuri, idan nayi muku bayani Allah zaku fahimce ni, nima ban san nayi kuskure ba sai daga baya, kuma na rasa ta yanda zan maku bayani ne shisa aka ɗauka tsawon wannan lokacin". Maama ta kawar da kanta gefe ɗaya bata ko kallesa ba, ita aurar Fillo fa ba shi yay mata ciwo ba, ofcourse yayi ba daidai ba, but da auren ya ƙare akan Fillo abin yayi mata daɗi, takaicinta ɗaya da aurensa zai ƙare a unprepared marriage, shikenan mafarkinta akan aurensa duk sai ya tashi a banza?, bacin irin ƙwallafa rai da cin burin da tayi da aurensa mussaman da ta gama saka Fillo acikin lissafin ƙarin auren nasa?, wancan an yisa ba shiri wannan ma kuma sai azo mata da wani zance na daban da hankali ya kasa ɗauka. "Maama please". ya ƙara kiran sunanta dan ya san ita ɗaya yake da ita a wurin nan, roƙon Mum won't favour him shisa ma yake tsoron kallonta. tausayinsa ya kama Maama sosai amma sai ta kawar ta dake ta kalli Baffa tace,"ka yiwa tufkar hanci kawai, ka kira Hakimin da kanka ka faɗa masa komai, mu ba iyayen banza ba ne da zai ja mana magana a bakin duniya, inma sallamarsa zaka yi ka sallame shi ya tattara komatsansa ya wuce ya bar mana gida, dan ni ba zan ci gaba da zama da ɗan wiwi ba, rashin sanin darajar iyaye har ina haka?, ai cin mutumci da rashin sanin darajar tamu yayi yawa". ya miƙe daga gaban Baffa ya nufi Mum, tana kallon ya taho ta dakatar da shi,"karka sake kazo inda nake, banda hurumi da kai. su ma ɗin da suka gaza ɗaukar mataki akanka har yanzu lokacinka suke da, ni kuwa ka iso gabana banga abinda zai hanani shaƙeka ba". sai kuma ta mayar da kallonta kan Baffa cikin ƙunar rai tace,"kai har yarda kake da shi akan ya auri yarinya?, ta ina zai soma ɗaurama kansa aure babu iyaye, shege ne shi?, ko kuma shi uban yarinyar ba ƙwaƙwalwa akansa?, ai kawai ka zartar masa da hukuncin haikewa ƴar mutane da ya nemi yayi, ka bugasa a jarida ka yaɗawa duniya, ba wai ka tsaya sauraron zantukan kare kai daga bakinsa ba, mu zai rainama wayo saboda a rabu da shi shine zai ce ya aureta, ko ya taɓa ganin anyi haka a film da zai ce zai kwatanta?, to ka zartar masa da hukuncin da ake ma ƴan iska kawai, ka mance ɗanka ne kayi alƙalanci dai-dai da yanda kuke ma masu ɓata ƴaƴan mutane, batun ya aureta ma bai taso ba ƙarya yake yi kare kansa zai yi". hankalin Turaki ya ƙara tashi matuƙa, ya zube yana dafe kansa sosai yace,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wallahi tallahi na aureta, na rantse da Allah na aureta, idan ban mallaketa ba babu abinda zai sa ki samemu a yanda kika ganmu Mum, mahaifinta ma shaida ne shi ya karɓi sadakinta...kuma wallahi ni banyi auren nan domin rashin sanin darajanku ba ko kuma ci muku mutumci ba, wallahi na amince an ɗaura auren ne saboda tausayinta, saboda ban da yanda zan yi a lokacin". ya ɗaga kai ya kalli Baffa yace,"Baffa tayi min taimakon da ba kowa zai iya yi min ba shisa na aureta saboda ina ganin hakan shi ne mafi cancantar sakayyar da zanyi mata". "Taimako?". Baffa ya tambayesa. ya ɗaga kansa,"ehh Baffa, kuma ka tambayeta kaji". Baffa ya kalli inda Fillo take kamar yanda Hajiya Madina ta buɗe ido tana kallonta, kar dai ta faɗa masa duk shirin da su Samha suke yi akansa, kuma tunaninta bai kai ga nisa ba taji Fillo na cewa Baffa,"ni bai aureni ba Baffa, bai ma san a inda Abbana yake ba, kuma banyi masa taimakon komai ba". Turaki ya saki baki yana kallonta da mamaki, sai kuma yace,"ehh Baffa bata san na aureta ba amma ƙarya take yi wallahi tace bata taimakan ba, taimakon da tayi min ko wanda muka fito ciki ɗaya ba lallai ya iya yi min ba, ku a bata ƙur'ani ta rantse da shi bata saka kanta a haɗari ba saboda ceto ni daga hallaka ni da aka nemi yi, wallahi Baffa asirin da akayi min ta dinga bi tana ɗaukewa". Mum ta riga Maama da Baffa furta kalmar asiri, Fillo ta ɗago kanta a rikice tana kallon Baffa tana girgiza masa kai,"Baffa ba haka bane, ni ban san abin da yake faɗa ba". kwarjin da ke tare da Baffa yasa bata san sanda ta fashe da kuka ba tace,"wallahi Allah bani nayi masa ba, waɗanda ma suka binne asirin ban sansu ba, jinsu nayi kawai suna faɗa, ni kuma nasan bai yi musu komai ba shisa na dinga lalata musu aiki". Baffa ya kalli Hajiya Madina yace,"kira min Kakar yarinyar nan". abin da take shirin yi kenan dama, dan ta fara tunanin anya ba aljanu a jikin Fillo, ta ɗauka waya ta kira Kaka wadda taji ta ruɗe jin tace suzo yanzu cikin gaggawa. Mum ta dinƙa kallon Fillo cike da nazari, muryarta kaɗai ta isa ta shaida maka abinda ta faɗa gaskiya ne balle kuma ka kalli fuskarta da gaskiyar ta fito ɓaro ɓaro, to waye zai ma Babanta asiri?, akan wanne dalili?, lokaci ɗaya kuma cikin kanta da zuciyarta suka haska mata sunan Fulani Azima, take ta furta innalillahi wa'inna ilaihi raji'un wanda yaja idon kowa kanta. kawai sai ta fashe da kuka tana jin wani zafi da tashin hankali, me sukai ma Azima haka a rayuwa?, cutarwar da tayi mata bai isheta ba sai da ta biyo ta kan ɗanta?. kukan nata kuma shi yasa Fillo hargitsewa ta fashe da kuka sosai tana girgiza kanta tana cewa,"wallahi Allah Mum bani nayi masa ba na rantse da Allah". Baffa yace da ita,"in har ba ke bace me yasa baki sanar ba?". tace,"Baffa ai nasan idan na faɗa ba lallai a yarda dani ba, kuma wataƙila ma ace ni nayi masa kuma wallahi bani bace". Hajiya Madina ta sauke numfashi, calmly tace da ita,"nutsu Fillo ki juyo ki fuskance ni". tana fizgar numfashi ta juyo ta fuskanceta kanta a ƙasa tana cewa,"wallahi Maama bani bace, wasu ne su uku, kuma ban sansu ba". Hajiya Madina tace,"kuma kin tabbatar asirin ne?". tai saurin ɗaga kanta,"ehh Maama haka suka ce, Allah ne shaidata". "amma me yasa baki taɓa faɗa min ba?". tace,"Maama ban san ta yanda za'a yarda da ni ba, kuma da naga duk na kwashe waɗanda naji sun faɗa shisa ban faɗa miki ba, kuma bana so ku shiga damuwa ma". Mum ta fashe da kuka sosai tace,"idan na yafe na wa ba zan yafe na Babana ba, sai mun tsaya a gaban ubangiji da ko waye yake da hannu akan lamarin nan, me yarona yayi mata tsakani

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243