Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 218

Chapter 218

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
Download Book

garin kunun, don Allah a ƙara yi min, naji daɗinsa sosai wallahi, sometimes idan na kalli kaina sai inga kamar ba ni ba, ji fa kumatun da na tara". ta faɗa tana ƴar dariya me kama da ta ƙarfin hali. "wai ke zatonki kunu ne kaɗai ya saka ki wannan ƙibar, to har da Babyn mu". "hmm ni fa banda wani ciki. haka jiya Ammi ma da naje sai adu'a take wai Allah ya raba lafiya, ni dai nayi murmushi kawai. kafin mu taho test nawa aka yi duk ba ciki ba ne, ni kam ma ba yanzu zan haihu ba sai kamar nan da 2years lokacin na ƙara girma". "yanda za'aji daɗin cewa ke juya ce kenan, ki ma daina wannan kuskuren tunanin, yanda kike da kishiyar nan in har ta rigaki haihuwa sai kin fuskanci ƙalubale, gwarama ki roƙi Allah ya ba ki, in ya so kya huta daga baya". har bakin mota Nuratu ta rakata, ita kuma sai godiya take yi mata. "ki daure dai ta bakin Abban Farha ki ƙara zuwa asibiti su duba, don bani da tantama kin ɗauki ciki". Fillo tayi murmushi me ciwo,"idan cikin ne zai bayyana kansa Anty Nuratu. kin san fa nace masa muje asibitin wallahi ko tanka min bai yi ba, da na ƙara magana ma ce yay bai shirya tara ƴaƴa yanzu ba". tausayinta ya kama Nuratu, ta kawar da zancen dan ta lura kamar akwai damuwar da take ciki, kamar dai yanzu tana zaman haƙuri ne da Turaki kawai. "kin ji bikin Raudha an mayar da shi Adamawa ko?". "haka Ummi ta faɗa min jiya da muka yi waya". "ni ban so hakan ba wallahi, kawai dan ba yanda aka iya da Maudo ne. yaushe za ki tafi to?". Fillo tayi murmushi me ciwo tace,"ai babu ni a batun zuwa kam dan yace ba zanje ba, kuma wallahi ba zan ƙara yi masa maganar ba, na lura tun da zai mayar da auren nan ya ɗauko wata bura'uba ya ɗorawa kansa, kuma sai dai komai ya ƙare akansa shi ɗaya ni ba saurarsa zan yi ba, ban iya haɗa hanya da damuwa". Nuratu tace,"Allah dai ya kyauta, yanzu kam sai kin ta haƙuri, yan da za ki sami mijinki a ke ta ɗaya ba haka za ki same shi ba a ku biyu ba. shawarata kiyi ta adu'a Allah ya kauda fitina tsakanin duk ku ukun, abin da bai da kyau Allah ya mayar maku da shi me kyau. sannan don Allah ba ruwanki da wata fitina, imma daga ɓangarenki ko nata, ki kama mutuncinki ki riƙe, kar ki sake wani hargagi ko cin mutuncin ko fashe fashe da duk danginsu a same su daga gareki, wannan duk kishin marasa ilimi ne. kuma jiya na faɗa miki yau zan ƙara maimaita miki, babu ruwanki da shisshigewa ko tusa kai a wurinta wai ko dan ku zauna lafiya a'a sam, idan har taga kin ja ajinki da mutuncinki za ki ga tana jin shakkarki, idan ma tana tare da tsiya ne to zata sha jinin jikinta. sai kuma shawarar da zan ƙara ba ki, kafin ya amince kici gaba da karatu to ki fara business, kin san ance darajarka jakarka ko aljihunka, to ki kama kasuwanci kamu me kyau, ta yanda hankalinki zai karkata ɗungurungum akansa, ta yanda za ki zama baki da lissafin wata kishiya da takaicin miji sai na kuɗinki, wallah kasuwanci wani babban abu ne na siyawa kai mutunci wasu matan ne kawai basa ganewa, kuma kar ki yarda ki kama kasuwanci da kuɗinsa, ki kira Dada ki faɗa mata kina buƙatar kuɗi ko kuma kice a buɗe miki shago. Sannan ko da wasa kar ki sake mijinku ya fara samun tashin hankali ta ɓangaren ki, in ba haka duk san da wani laifi ya afku ko da ba ke bace zai ce ai kece uwar rigima, abu guda biyu ne zuwa uku naki, sanin darajar kai da sanin yadda za ki sarrafa ragamar miji, ki zama kece limamiyar ba wannan limamiyar da ke jan ragamar limancin layu biyu ba. Kissa da kisisina kamar ki lashi takashinsa amma shi ma ina jan kunnenki, mutunciki kar ki sake kiyi wasarairai da shi, domin shi ne limamin rayuwa". Fillo tasa tissue ta goge hawayenta, kuka ya kubce mata ta ce,"ni kaina na san sai nayi haƙuri yanzu Anty, Turaki ya sauya min fiye da tunani. wallahi Anty da yazo min da batun zai mayar da auren nan sam ban nuna masa ina ƙin dawowarta ba balle kuma na ɗaga masa hankali. amma jiya kafin su tafi ɗaurin aure kar ki ga yan da ya taso min da faɗa, har da zagi fa Anty, kuma wallahi ba wani abu nayi masa ba, cewa kawai nayi zan koma can gidansu sai an gama biki na dawo, wai buɗar bakinsa ce yay tunda ina baƙin ciki da zuwan wata ai dole nace zan bar gida, to babu in da zanje in zauna in kula da ƴan uwanta da suke zaryar shiga da fitar yi mata jere, idan suka buƙaci wani abu wa nake nufin zai ba su, ko shi zai baro wajen aikinsa ne ya kawo musu. to kar inyi kuskuren wulaƙanta masa Mata, don ƴar'uwarsa ce, kuma samun zaman lafiya tsakanina da shi na mutunta ƴan'uwansa, Anty kamar fa zai duke ni, duk yadda na so da kar a fahimci ina cikin damuwa sai da Maama ta fahimta, da na dawo da daddare sai ce min yayi wai naje na kai ƙararsa ina so in shiga tsakaninsa da iyayensa, to wallahi zai yi min abin da ban taɓa zato ba, zamana da shi babu dole..." kuka ya ƙara kubcewa Fillo sosai,"kuma wallahi tallahi Anty ban kai ƙararsa ba, na san dai nayi iyaka ƙoƙarin da za'a fahimci bana cikin damuwa amma na gaza, shi ne har Maama ta gane ta tsare ni da tambayoyi, kuma ita ma ban ce mata ga dalili ba haka nace mata bana jin daɗi ne, kuma da ta san da ma ban da lafiya bata ƙara tayar da zance ba, amma shi ne har yake ikirarin wai sai ya rabu da ni in har na nuna bana son ƴar'uwarsa ko kuma na ƙara kai ƙararsa wurin Maama. tsakani da Allah Anty ko anan idan tazo ya nuna mata ta fini matsayi ba sai yaja min wulaƙanci daga wurinta ba, yanzu nan ƙunshi nace za'a yi min sai ce yay ba da yawunsa ba". Nuratu taji tausayinta sosai, ta dinƙa bata haƙuri da lallashinta, tare da yi mata nasihohi da kuma wasu shawarwarin da zata ji daɗinsu muddin tayi amfani da su. kafin nan suka yi sallama taja motarta. [9/7, 02:17] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *58* dawowar Fillo gida ta tarar ana ta kai komo wajen shiga da kayayyaki ɓangaren Ilham, tun jiya ake wannan zaryar, ƴan'uwan mahaifiyarta ne kusan duk ɗin su, sai Boɗejo da Inna Falmata. sai dai bata san ba ko yau har da su tunda dai bikin ba ɗaya ba ne, duk da dai taga Boɗejo na nuna kamar bata da hurumi da auren su Zaytuna da Khaleel da Samha, kamar su ma ba jikokinta ba ne. ɗauke kai tayi daga barin kallon part ɗin Ilham ɗin, tayi wucewarta part ɗinta bayan ta

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243