Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 215

Chapter 215

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,213 words 0 views Progress saved
Download Book

ki haƙura ki haƙura". daga cikin wayar ɓangaren Rashida ta ce,"haka kace?, to zaka san kayi da ƴar halak, wallahi sai in ce ma ba za'a kawo ni gidan naka ba". ita ma tayi maganar a fusace kamar yanda shi ma yayi. "hakan zai sa ki burge ni". ya faɗa yana kashe wayar ya jefa cikin aljihu, ransa a ɓace ya nufi mota ya shiga. daga cikin gidan, idan ka shigo compound, zaka kutsa ne ta cikin tarin jama'ar da ke ta hayaniya su na kaiwa da komowa wajen aikace-aikace, wasu na wucewa da manyan kuloli na abinci, yayin da wasu ke tsaye akan babban kaskon da ake suyar nama a cikinsa. idan ka lura da part huɗun da ke jere, za ka fahimci a ɓangare na uku daga ɓangaren dama, wanda shi ne ɓangaren Hajiya Ramla, anan ne taron mutanen yafi yawa, don ga takalman jama'a nan birjik daga wajen ƙofar parlon. a yayin da ka shiga cikin parlon, zaka tarar da manyan mata masu ji da kansu, waɗanda suka sha ilimin boko, boko ta ratsa su ta ko'ina, waɗanda mafiya yawan su ma'aikata ne a ƙarƙashin federal government. wasu na zaune akan kujera yayin da wasu ke zaune a ƙasan carpet ɗin da aka malale duka parlon da shi, kowa na hira da abokin zamansa, hayaniyar dai tayi yawa wacca ta kai ga har ba'a iya jiyo sautin muryar wata dattijuwa da ta shigo ciki tana kiran sunan Hajiya Ramla. a lokacin ne kuma Hajiya Ramla ke sakkowa daga saman bene tare da ɗaya daga cikin amaren da ake aurarwa wato Samha. magana suke yi yayin sakkowar ta su inda Samha ke ta ƙorafin hayaniyar. "na nemi Nihal na rasa, ki lalubo min ita acikin taron jama'ar nan don Allah, ta zo driver ya kaita su karɓo mana ɗinkin mu. kina kallo ma Fillo bata sami saka ankon ɗaurin auren nan ba, haka Babana ya zo ya sakani a gaba yana ta kumbure-kumbure, ni ban san ya akai ku ka kaiwa ɗan shiriritar tela ba". Samha ta amshe da cewa,"ai wallahi jiya na so da ni aka je da sai nayi masa rashin mutunci. ni yanzu Nihal ma aina zan ganta, da ƙyar ma idan bata ƙwace tayi gidan Hammah ba fa". a lokacin ne dattijiuwar da ta shigo tana laluben Hajiya Ramla ta ƙaraso wajen. Hajiya Ramla tace da ita,"sannun ku da aiki Maga". "yauwa Hajiya, wai da ma masu yankan nama ne suka ce Baffa ya kira waya yace a ƙara yanka raƙumi da raguna guda uku, sai akai raƙumin gidan Hakimi". "sun yanka ne?". "a'a da ma nace bari na zo na fara shaida miki". "to kinga garzaya ki faɗawa Madina, ki dubata a ɓangarenta ko ɓangaren yaran nan". "to shikenan, batun funkason can fa ya za'ai da shi?". "ai da kun gama ku kai gidan Babana, ɓangaren Fillo za ku kai, nata ne aka yi mata saboda baƙin da ke can". "to shikenan". Maga ta juya ta fita a parlon, yayin da Hajiya Ramla ta ƙarasa wurin mutanen da ke zazzaune a parlon, waɗanda mafi yawan su abokan aikinta ne. "sannunku fa". ta faɗa a sanda take zama akan ɗaya daga cikin kujerun, kusa da wata aminiyarta Hajiya Shamsiyya. "yo ke uwar amarya haka ake sai ki shige ɗaka ki barmu zazzaune anan". murmushi ya ƙwace a fuskar Hajiya Ramla tace,"haƙuri zaku yi, ƴar taku ce ta sakani gaba tana kuka". ta faɗa a lokacin da take bawa wata tsohuwa umarnin inda zata ajiye kulolin soyayyan naman da ta shigo da su. sannan ta ƙwalla kiran Ɗausiyya da sabuwar ƴar aikin da suka yi bayan auran Fillo, me su na Maraƙisiyya, cikin sauri sai ga su sun zo sun durƙusa a gabanta. "ku ɗauko farantai ku fara rabon naman nan, kowanne plate ku zuba yanka goma sha biyar". sai kuma ta kalli tsohuwar tace,"Yaya kun kai ɓangaren Madina kuwa?". "ehh Hajiya yanzu Yami ta tafi kaiwa". "to masha'Allah, sannunku da aiki". sannan ta ƙara cewa da ita,"Yaya don Allah ce da Madina ta bayar da maƙullin store, sai a samu waɗanda za su ɗebo lemuka aciki, a ɗebo katan arba'in, akai katan sha biyar gidan Babana, sai a bar sauran anan". cikin sauri tsohuwar ta miƙe ta fita, sai da ta fara zuwa ta duba wajen aikin suyar ta su sannan ta wuce ɓangaren Hajiya Madina. nan ɓangaren ma cike yake da mutane waɗanda mafi yawansu ƴan'uwa ne, duk sai ka kalla fuskokin su zaka shaida ashe Hajiya Madina ƴar dangi ce, saboda kusan duk kamannin su ɗaya. "Hajiya tana sama ne?". tsohuwar ta tambaya a sanda ta shiga parlon. "kamar dai ta shiga kitchen". wata acikin mutanen dake zaune akan kujera ta faɗa. "ta fito ta koma sama fa, yanzu suka wuce ita da Zaytuna". Tsohuwar ta miƙe cikin hanzari ta hau upstairs, ta tsaya a ƙofar ɗakin Hajiya Madina domin jiran iso bayan tayi sallama. a sanda babu wanda ma ya jita saboda akwai ƴar hayaniya acikin ɗakin. Hajiya Madina na tsaye a gaban madubi tana ɗaura sarƙa a wuyanta, a lokaci ɗaya kuma tana bayani ga Maga. "kinga ba wani nama da za'a kai gidan Hakimi, shi ya siyo mana, ko a gidansa ake taron, mu da aurar da ƴaƴa shi da karɓe nama. wani lokacin ma dai Baffa ya fiya neman suna, ya mayar da Hakimi kamar wani ubansa, to kice su yanka a haɗe gaba ɗaya da na gida, in Baffan ya dawo ace masa mantawa aka yi". Maga ta miƙe tana ƴar dariya ta fita, Yaya ta shigo ita ma, ta durƙusa tana cewa,"Hajiya wai ki bayar da maƙullin store za'a ɗebo lemuka". "Zaytuna duba drower ɗin nan ki miƙo mata maƙulli". sai kuma ta dubi Yayan ta ƙara cewa,"don Allah da an ɗebo a rufe saboda jiya sai da akayi mana ta'adi". Umman Nadiya ta shigo ɗakin a lokacin. "ke Madina da ma Turaki aure ya ƙara?". Hajiya Madina ta kalli fuskarta a cikin madubi tare da yin murmushin takaici sannan ta ce,"wa ya guntsa miki wannan maganar?, to ba sabon aure yayi ba tsohuwar matarsa ya mayar, ita ma kuma don fitinanniyar Kakarsa ta ƙara tayar da rigima ne, yauwa biyayya ya ƙara yi a karo na babu adadi, don Allah a bar ɗana ya huta a daina yawan zancensa ana faɗar masa da gaba, haba tun jiya da akace an ɗaura aure da shi ake ta ƙwala kiran sunansa acikin gidan nan kamar wanda yay sata, to idan ma auran ya ƙara zunubi ya aikata ko me?, ina ruwan wani?, ko ba mata huɗu aka halasta masa ba?, haba mutane da shegen gulma da tsugudidi". Umman Nadiya tace,"to jarababba Allah ya ba ki haƙuri, ni tambaya nayi ba wani abu ba". Hajiya Madina dai bata ƙara tanka mata ba, ta haɗe rai ta juya kan Zaytuna tana yi mata faɗan kukan da take tayi tun jiya da aka ɗaura aure. "ni dai ina ga sai na haɗa miki da duka tukunna, haba kuka yaƙi ci yaƙi cinyewa abu tun jiya, to ki shiga hankalinki da ni". Umman Nadiya tace,"to ai dole tayi kuka, ita kaɗai ce fa acikin su zata yi nesa". "yo nesa abu da ba ƙasar zata bari ba, Allah na tuba ina

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243