Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 241

Chapter 241

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,220 words 0 views Progress saved
Download Book

taɓa iya ƙwatar kansa ba a hannun Ayan, bai da wannan ƙarfin ko kaɗan, hatta ruƙon da yaron yay masa ji yake kamar an jona masa electricity. zuwan police wajen suka ƙwace Ayan da ga kan Amir wanda yake ƙoƙarin kaiwa ƙasa. banda haki babu abin da Ayan ke yi, idonsa yay jawur kamar bana ƙaramin yaro ba, police suka kama hannun Amir suka saka masa ankwa, sai a yanzu idonsa ya kai kan Turaki, yaji gabansa yay mugun faɗuwa, ya wurga ido ya ƙara kallon Ayan, jini ba banza ba, don lokaci guda ya tuna da mugun dukan da ya sha lokacin da suka yi kidnapping Fillo. don haka tsananin tsoro ya kama shi, ya tabbatar yanzu idan Turaki ya gane waye shi to sai dai waninsa, dan haka gwara yabi ƴan sandan, duk runtsi zai fito ya sani. police su ka kama Amir suka saka shi a mota suka tafi. bayan su Turaki sun dawo daga dubiyar Fulani Azima, direct gidan ya wuce da yaransa, in da anan suke cin abincin dare duk friday. ana jin tsayuwar motarsu Boɗejo tace,"to ga kajin nan sun iso". Mum na zaune kan kujera, da jaririyar Nihal a hannunta ta gama yi mata wankan yamma, tayi murmushi da jin furucin Boɗejon. Turaki ya shigo tare da yaransa, waɗanda sai da suka fara zuwa ɓangaren Baffa suka gaida shi. jikokin gidan duk suka yi wajensa su na yi masa sannu da zuwa, ya ɗauki ƴar gidan Zaytuna me suna Aisha. Maama tayi jikin Boɗejo tana cewa,"nayi kewar tsohuwa". Boɗejo tace,"kinga ni kuwa yau ba wanda nayi kewa a cikinku, ko babu komai bakina da na Kakarku luff babu rabon faɗa". "ai kuwa tun da kika faɗi haka ba zan ba ki abin da na taho da shi ba". Boɗejo da a yanzu ta ƙara zama tsohuwa tukuff ta janyo Maama jikinta tana faɗin,"haba ƙawata ƴar mutunci yi haƙuri, ai yanda bana iya fita inci ni ɗaya ban rage miki ba haka kema na sa ni". Maama ta dubi Turaki da ya zauna akan kujera su na gaisawa da Mum, tace,"Abie ka ɗauko min leda ta?". ya kalli gefensa yay mata nuni da ledar, sannan ta miƙe taje ta ɗauko, tazo ta zauna ta buɗe ta ɗauko dublan ɗin ciki tana bawa Boɗejo, wacca ke tambayar aina suka siyo shi, ita kuma tana bata labarin yacca ta kwaso shi a ɗakin Inna Wuro. da daddare bayan sun gama cin abincin dare, suka fara haramar tafiya gida. Mum ta juye musu sauran teba da miyar gandar da akayi a flask tace su tafarwa da Ilham. ko da suka koma gida Turaki ajiye su yay ya ƙara fita, ya tafi siyo magungunan da likita ya rubutawa Ilham, wacca likitoci suka yi iyaka bincikensu akan rashin haihuwarta, suka tabbatar da cewa da wuya idan ta haihu sai in kuma wani iko na ubangiji. tana zaune a parlo tana kallo su Ayan suka shiga, tayi musu kallo ɗaya ta ɗauke kanta taci gaba da kallon film ɗin da ake yi a mbc action. ganin bata kula su ba Ayan yace,"Anty daga wurin Maminki mu ke". furucin nata yasa ta mayar da hankalinta gare shi tana jin cewarsa. "ya ku ka ƙara samun yanayin jikin nata?". Ayan yace,"ba sauƙi, sai tsanani da ya ƙara. yau da muka je jini yana ta zuba ta duburarta, sai botiki aka tara mata ma a wajen, ta ƙara motsewa babu kyan gani". Ilham ta saka kuka sosai tana kifa kanta akan ƙafafunta, tsawon minti biyar tana kuka kafin ta ɗago tare da ɗaukar wayarta ta shiga kiran lambar Turaki, sau kusan sau biyar kiran yaƙi shiga, ana ta faɗa mata not recherble. ta kalli agogo taga ƙarfe tara da rabi a lokacin, ta miƙe ta wuce ɗaki, ba jimawa sai gata ta sakko sanye da hijab. ta kalli yaran tace,"idan Babanku ya dawo kuce masa na tafi wurin Mami. ku faɗa masa ina ta kiran wayarsa taƙi shiga". su ka amsa mata,"to, a dawo lafiya". "Allah yasa". ta faɗa tana nufar ƙofar fita, maganar Maama ta dakatar da ita,"Anty ko za ki tafi da tebar?". ta kalleta tace,"Mum ce tayi?". "ehh". "Maama ba zan iya ci ba, ku cinye idan kuna so. akwai pancake a kitchen na ajiye muku, ba kwa buƙatar wani abu?". suka haɗa baki wajen faɗin,"ba ma buƙatar komai Anty". ta kalli Ayan tace,"saura ka sakata kuka". yay ƴar dariya yace,"Anty wai haka kawai nake sakata kukan?, sai fa tayi min ba daidai ba". tayi murmushin ƙarfin hali kawai ta fice ba tare da ta ƙara ce musu komai ba. sai wajen goma Turaki ya dawo gida, yana shigowa parlo ya tarar da Ayan akan Maama yana zazzaga mata masifa. "dilla Malama bani abu na, na rantse da Allah daga yau ma kika ƙara taɓa min kaya sai na faffasa miki baki, kin dai ji na faɗa miki". ya faɗa yana sakin ƙwafa me ƙarfi, sai kuma ya saka hannu ya dungure mata kai glass ɗin idonta ya faɗi, a rikice ta durƙusa tana neman glass ɗin. ta lalubo shi da ƙyar ta saka, ta turo ɗan ƙaramin bakinta gaba tana hura hanci tace,"kuma wallahi idan Abi ya dawo sai na faɗa masa". tana ƙoƙarin raɓawa ta gefensa ta wuce, ya fincikota yana faɗin,"ɗauko min kayana ki bani". ta fizge tana faɗin,"ba zan ɗauko ba ɗin". a zuciye Ayan ya ɗaga hannu zai mareta muryar Turaki ta dakatar da shi. "Ayan!". ya kira sunansa da ƙarfin sauti wanda hakan yasa Ayan ɗin nutsuwa. "me ta taɓa maka da ma?, kai da baka da haƙuri, na faɗa maka bana son wannan zafin zuciyar taka, idan ƙanwarka bata taɓa abinka ba na wa kake so ta taɓa?". Ayan na faman huci yace,"to Abie ita ce komai ta ɗaukar min sai ta lalata, kalla fa yanda ta fasa min sabon earpod ɗina, kuma shekaranjiya da Uncle Bello yazo ya ban shi". yay maganar yana nunawa Turaki. "kuma shi ne saboda rashin tunanin akan abun duniya zaka ɗaga hannu kace zaka mareta?, ranar da bana raye a haka zaka kula da ita?". Ayan yay shiru bai ce komai ba, ya kumbura yayi fam yana tunanin abin da zai yiwa Maama ya huce. "garin ya kika fasa masa abun sa?". "Abie ba na sane Allah, nazo sakkowa daga upstairs na zame shi ne ya faɗi daga kunnena". Turaki ya jefawa Ayan key ɗin motarsa yace,"ka je mota ka ɗauko nawa". yana rufe baki Maama ta ce,"Abie ni fa?, Farha ta karɓi nawa aro kuma ba zan iya cewa ta ba ni ba". "ki bari zan siyo miki wani Maama". washe gari da safe wajen ƙarfe takwas hayaniyar yaran nasa ta tashe shi daga bacci, ya tashi ya shiga toilet yay wanka, bayan ya fito yazo ya tsaya jikin window yana hango su. a field suke su na buga basket ball, Ayan na ta yawo da ball ɗin yana dariya, ita ma Maama na ta yawo wajen ganin ta kare ball ɗin daga shiga cikin raga, sai dariya take yi tana cije leɓenta, motsi kaɗan sai ta gyara zaman glass ta karyar da wuya alamun ta fara gajiya. duhun garin kuma ya fara hanata gani sosai duk da medical glass ɗin da ke sanye a idon

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243